page 8

161 11 1
                                    

*KOWA YA IYA ALLONSA*....

   *Na SadNaf*

        Page 8

4WEEKS REVERSE PCOS SYMPTOMS PROMO CHALLENGE wanda za’a fara on 1st January 2024.
Program ne da mukema mata masu CUTAN PCOS. Muna taimaka musu wurin magance wannan CUTAN ta hanyar
1. Basu magungunan cutan
2. PCOS CYSTERHOOD discussion group
3.PCOS and Hormonal imbalance reversal da
4.Fertility Treatment
CUTAN PCOS yanada alamomi kaman:
-Yin kiba ba bisa dalili ba
-Yawan Kasala
-Rashin Bacci
-Gashi a gemu,saman ciki,da saje.
-Kuraje a fuska, baya da kirji
-Rikicewar jinin al’ada:Daina zuwa,ko zuwa sau biyu a wata.
-Zubewan gashi
-Yawan kwadayi
-Yawan Kamuwa da infection akai akai
-Daukewar sha’awa
-Rashin sha’awa
-Motsi a ciki
Dama dai sauran alamonin shi.
Zaki iya tuntuban mu ta WhatsApp a wannan number 08109388227 domin yin register,Ko kuma a shafukan mu na yanan gizo a TIKTOK,YOUTUBE da INSTAGRAM me suna “LafiyarMataTv”

*Page 8*

          Nana kasa ta zub'e dan har jikinta ya d'auki rawar ganin sa tun da ya Kadeta yakan fado mata haka kawai bata manta shi ba,bata Kuma san mai yasa yake yawan fado mata ba.

Ita kanta mamakin ganinsa a gidan da take aiki take.

Amma take ta dau haske da taga Jaseem ya nufi wajensa da gudu yana Daddy Oyoyo sai taji gabanta ya fadi da ta gane mahaifin Jaseem ne da Allah ya dora mata San shi.

A iya yau Allah ya hada jininta da Jaseem dan sosai taji tana kaunar Jaseem da taji hajiya Rabia nata labarin da mamakin yadda ya makale mata dan jaseem bashi da sabo ko su Yusrah bai wani Saba dasu ba Yana musu kiwuya,da iya ita kadai yake yarda.

Amma yana dawowa daga makaranta ya makale mata bai yarda wani ya masa abu sai ita.

Tana san Yara kyawawa sosai dan Jaseem kyakyawa ne fari tas dashi.

Ko a yanzu ma ba yadda Hajiya Rabia ba tayi dashi akan yazo ya wuce su hau sama su kwanta ba.

Amma Jaseem ya makale a wajenta wai dakinta zai kwana.

Hajiya Rabia kuwa ba yarda ne ba tayi da Nana da ta matukar yabawa da hankalinta ba,iya ibadar da take dashi yayi matukar siye zuciyarta.

Gata da kazar kazar din aiki komai nata a tsaftace banda Ladabi da biyayya da take dashi.

Idan a yadda take ganin Nana ne ba zasu samu matsala da ita ba.

Dagewar da Jaseem yayi yasa ta hakura ta hau sama tana ta mamakin yadda jaseem da bashi da sabo ya Saba da Nana daga ganin ta.

Jameel kuwa Sam sai ya kasa hade tunaninsa waje daya dan bai San mai Nana firdausi ke yi a gidansu kuma cikin daki ba.

Yadda yaga jikinta na rawa yasa ya gyarawa Jaseem zama a kafadarsa dan ganinsa da yayi yasa shagwabarsa motsawa yace "Nana firdausi fito Palo na ganki"

Yayi waje dan Yana so yasan mai ya kawota gidan har Kuma ya akayi ma aka Santa da alakarta da Yan gidan nasu da bai tab'a sani ba.

Nana bayansa tabi cikin Jin tsoro har lokacin gabanta bai bar faduwa ba.

A kujera mai zaman mutum daya Jameel ya zauna jaseem kuma ya sauka daga cinyarsa ya Kara komawa wajen Nana dake Shirin zama a kasa.

Jameel kuwa yayi saurin cewa "hau kujera mana ki zauna mana Nana firdausi"

"Aaa Yallabai nan yayi"

Duk yadda yaso ta hau Kujerar k'i tayi kanta a kasa Jaseem yayi dare dare a cinyarta sai ta dan b'oye fuskarta a jikin Jaseem.

"Nana firdausi ya jikin naki dafatan kin warke bansan gidanku ba naso Kara zuwa na duba ki na baki hakuri"

"Ba komai Yallabai na warke sosai ma"

KOWA YA IYA ALLONSA Where stories live. Discover now