*KOWA YA IYA ALLONSA*....
*Na SadNaf*
Page 4
4WEEKS REVERSE PCOS SYMPTOMS PROMO CHALLENGE wanda za’a fara on 1st January 2024.
Program ne da mukema mata masu CUTAN PCOS. Muna taimaka musu wurin magance wannan CUTAN ta hanyar
1. Basu magungunan cutan
2. PCOS CYSTERHOOD discussion group
3.PCOS and Hormonal imbalance reversal da
4.Fertility Treatment
CUTAN PCOS yanada alamomi kaman:
-Yin kiba ba bisa dalili ba
-Yawan Kasala
-Rashin Bacci
-Gashi a gemu,saman ciki,da saje.
-Kuraje a fuska, baya da kirji
-Rikicewar jinin al’ada:Daina zuwa,ko zuwa sau biyu a wata.
-Zubewan gashi
-Yawan kwadayi
-Yawan Kamuwa da infection akai akai
-Daukewar sha’awa
-Rashin sha’awa
-Motsi a ciki
Dama dai sauran alamonin shi.
Zaki iya tuntuban mu ta WhatsApp a wannan number 08109388227 domin yin register,Ko kuma a shafukan mu na yanan gizo a TIKTOK,YOUTUBE da INSTAGRAM me suna “LafiyarMataTv”*Page 4*
Jameel
Sai da aka yi wa matashiyar dressing din goshinta da kafarta a gaban idonsa Yana tsaye kafin hankalinsa ya dan kwanta.
Bakin cikin da Nimrah ta da sa mi shi da tunanin da ya tafi yana yi ya kai shi ga Kade matashiyar da Allah ya rufa masa asiri bata ji gagarumin ciwo ba.
Ban da zagin daya Sha a wajen wayanda suka iso kan matashiyar akan ganganci ya kai shi ga kadeta ban da Allah ya tsare amma taso kauce masa ya Kade ta.
A wajen rubuta sunanta da ma'aikatan asibitin suka yi yasan sunanta Nana firdausi.
Ba za ta fi shekara ashirin ba.
Kudin maganganun ya biya suka fito tana dingisa kafarta da ta dage rigar ta sama saboda wajen gwiwarta aka dinke mata.
Hakuri yayi ta bata tace Mi shi ba komai ko da ya nemi Kai ta wajen da zata je girgiza masa kai tayi tana ya bar shi.
Dama dan kyautatawa yake san kai ta
A k'ok'arin tare mata Napep ya ga ta ciro wani Karamin waya daga cikin Jakarta da shi Kansa yaji ringing din.
Cikin kasa da murya yaji tana "Hajiya kiyi hakuri wallahi hatsari nayi a hanya yanzu haka ma daga asibiti nake shi yasa kika ga ban iso ba"
Iya abinda ya iya Ji kenan da hakan ya sa ya saci kallonta sai yaga hawaye take tana "Dan Allah kiyi hakuri Hajiya wallahi ba wasa nake da aikina ba yanzu ma zan zo ki gani ga ma Wanda ya Kade ni nan bari na bashi kiji".
Mai da hankalinsa yayi kanta a daidai lokacin da ta matso kusa dashi ta mik'a masa wayar tana "Dan Allah ka yi mata bayani tak'i yarda dani "
Duk da bata fada masa Mai zaice ba ya gane inda ta dosa wacce suke magana ce da ita ta waya bata yarda da hatsarin tayi ba
Sai dai ko da ya kai wayar kunnensa sai yaji an katse
Damuwar da ya gani a tare da ita bai ma ga haka a tare da ita ba lokacin da ya kadeta.
tausayinta yaji har a ransa duk da bai san ya take da wacce tayi wayar ba
Dan har Lokacin bata bar zubar hawaye ba ido kuma ta zuba masa dan taji yadda zasu kare da wacce take so yayi wa bayani
Kara duba wayar yayi Ya kalleta Yana "Ta kashe wayar idan ba damuwa muje na kai ki mana sai na bata hakuri tunda kamar yadda ne ba tayi ba"
Girgiza masa kai tayi tana "tunda har ta kashe wayar ko munje ba zata saurare mu ba Allah yasa hakan shi yafi alheri"
Tace tare da d'auke hawayen da ya zubo mata da bayan hannunta.
Sai yaji wani irin tausayinta ya Kara rufe shi.
![](https://img.wattpad.com/cover/358253171-288-k630976.jpg)