UWARGIDANA
(...Ɓakin Ƙishi)
©️ AMYSHERH✔️
°📖Page Une📖.
Écr: 07032024Da wani irin mugun gudu ya sha burki a gaban babban katafaren kofar gidansa yayin da kura ta turnike wajen hatta shi kansa sai da kuran nan ta rufe shi ruff amma bai damu ba saboda abin da yake faruwa cikin gidan tafi daga masa hankali fiye da wannan ƙurar da ta bade shi. Ko daidaita parking bai yi da kyau ba ya afka da gudu cikin gidan yana kwala kiran sunanta yana karawa gudunsa karfi sakamakon jin bata amsa masa ba, hakan ya kara wa massarrafar numfashinsa gudu kar dai har mai aukuwa ta auku sun kashe ta? balle da ya tuna yanda tai masa magana cikin tashin hankali da abin da ta fada masa ta cikin wayar ya kara jefa shi cikin sabon tashin hankali wanda yafi na lokacin shigowar sa cikin gidan tsanani "Mon bonheur idan ba kai saurin zuwa gidan ka ba, zaka tarar da gawarwaki ne" abinda ya kara amsa kuwuwa a ƙwaƙwalwarsa kenan.
Yayin da su kuma y'aran suke rige-rigen barin ɗakinta cikin gudu zuwa na su tare da kargameshi da kuba sakamakon jin muryar ubansu wanda yake kiran sunan masoyiyarsa ba gaggautawa tare da nufar sashenta cikin tashin hankali. Saidai isar sa bakin kofar ɗakinta abin da idanunsa da ƙwaƙwalwarsa suka nuna da haska masa ya fi daga masa hankali, sunanta da yake ta ambata tun shigowar sa ya makale a makoshinsa sakamakon abinda yake gani a gaban sa,
saɓar rikicewa ƙafafunsa kasa daukar sa sukayi suka fara rawa, sunyi masa wani irin nauyi wanda hakan ya haddasa masa faduwa saman guiwowinsa a nan bakin kofar dakin ya fadi ya fara rarrafawa zuwa inda take kwance cikin mawuyacin hali da jini. Yayinda hannun ta ɗaya dafe da cikinta amma har lokacin bata motsa ba kuma bata ce da shi komai ba illa idanunta da suke a buɗe, duk da kamar ma ba rai tattare da ita, yayinda jini ke aikin gudu daga cikin jikinta hakan ya haddasa bacewar inda take kwance wanda shi bai san takamaiman inda duk wadannan gudan jinin suke fitowa daga jikinta ba, saboda saɓar yawan jinin da ya gani a wajen. Haka zalika komi na dakinta an farfasa su sun fita hayyacin su kamar yadda mai dakin ta fita a nata hayyacin. Da kyar ya samu karfi a jikin sa ya mike tsaye, ya karewa dakin kallo, sai jijjiga kai yake sosai ya girmamawa wannan lamarin, tuna halin da take ciki yasa da sauri ya shiga uwar daki ya dauko hijabinta ya sanya mata shi da kyar
Yayin da illahirin jikinsa yake ɓari sannan zufa sai karyo masa take ta ko wane kusurwa ta jikinsa saɓar yana cikin tashin hankali inda ya jike sharkaf kamar wanda aka wasa wa ruwa. Zuciyarsa cike take taff da mamaki da tunani, bai taba kawowa ko tunanin y'aran nan sun girmi tunanin sa haka ba sai yau, neman kashe rai fa sukayi! lalle y'ay'a sai uwayensu mata dan ko tantanma baya yi wannan aikin uwarsu ce ta sa su 'ya subhanallah! Sai yaushe matar nan zata yi hankali ne' ya furta a can kasan zuciyar sa.Nan da nan ya ciccibe ta yayi wajen motarsa da ita cikin sauri sauri da gudu gudu sakamakon rashin numfashi da ya lura a tattare da ita, ko takalma babu a ƙafarsa, yasa ta bayan mota ya zaga shima ya shiga mazaunin driver ya tada motar ya kara mata wuta sai babban asibitin cikin gari.
*** *** ***
Bangaren y'aran suna jin tashin motar mahaifinsu, ko wannensu ya fito daga maboyarsa suna zazzare idanuwa, yayin da suka fara kallan-kallo sakanin su, sai kuma suka tuntsire da dariya kamar wasu 'yan fashi da makami duk da basu da maraba da 'yan ta'adda, abinda suka aikata yau har sunfi 'yan ta'adda ma hatsari. Nan da nan samarin su uku suka fice daga cikin gidan suna jijinawa kan su akan abin da suka aikata yayin da ita kuma budurwar ta tattare kan kananun kannenta ta fice itama daga gidan, ko rufe gate basu yi ba kowa ya kama gabansa. Yayin da yanayinsu ya bani mamaki matuƙa duba da yadda suke cikin kwanciyar hankali da walwala bayan abin da suke aikata.
Sannan babu wata nadama ko tsoron abin da zai je ya dawo daga baya a tattare da su... Sai ma fatan "Allah yasa ta mutu" da suke mata maimaitawa.*** *** ***
Babban asibitin gari ya yi da ita cikin gaggawa da tashin hankali
Yayin da yake tuki cikin kasada dan gani yake kamar asibitin ma tayi masa nisa, hankalinsa sosai yake a tashe yana tuki yana waiwayar ta. Balle ma idan ya tuna y'ay'ansa ne fa da wannan aika-aikar tare da hudubar mahaifiyarsu
Sai waiwayen ta yake, ganin wahalar da take ciki yasa ya kara wa motarsa huta, kamar mai tashi sama
Isowarsa asibitin ko kama daidaita tsayuwar motarsa bai yi ba ya bude morfin motar ya fito ya fara kwalawa ma'aikatan asibitin kira nan da nan suka hallara gabanshi cikin tashin hankali yayin da shi kuma yake ƙoƙarin ciccibo ta daga bayan motar, nan da nan su ma suka fara rige-rigen taimaka masa suka fiddo ta daga motar suka daura ta saman kujerar nan ta mara lafiya da ake daura marasa lafiya sukayi cikin asibitin da ita yayinda sukayi masauki a urgence. Shi kuma yana biye da su da kyar aka dakatar da shi a bakin dakin urgence din suka fara ƙoƙarin ceto rayuwar ta inda suke ta ƙoƙarin tsayar da jini wanda yake ta ambaliya daga jikinta. Da kyar suka gano inda wannan uban jinin ke fitowar wanda sosai suka girgiza da wannan lamari saboda guri ne mai hatsari sosai ga 'ya mace sannan duba da irin jinin da ta zubar yasa hankalin su kara tashi dan ba lalle ne ta rayu ba sann tunda suka shiga da ita har wannan lokacin bata motsa ba sannan ba numfashi a tare da ita. Haƙan yasa nan da nan suka fara ƙoƙarin jona mata oxygène(na'urar janyo numfashi) ganin haka yasa mijinta ya tuntubi docteur cikin damuwa akan inan ta ne ya samu ciwo. Nan docteur ya kwatanta masa halin da take ciki sannan yace "Ta na cikin mawuyacin hali duba da inda ta ji ciwon, sannan ta zubar da jini sosai, dan haka muna bukatar ƙarin jini. Amma mun samu numfashin ta ya daidaita. Ka kwantar da hankalin ka In sha Allah zata ji sauki ne.
Maganar gaskiya inda ta ji ciwon nan guri ne mai hatsari sosai, ya akayi haka ya faru da ita, hatsari ta yi?"
Bai da bakin amsa wannan tambayoyin dan zuciyar sa banda tafarfasa ba abin da yake tun lokacin da likita ya fara masa bayani, yayin da shi kadai yasan hukuncin da zai zartas kan wannan y'aran. Nan ya shiga kiran numbern yayanta bayan ya daga ne ya sanar da shi abin da yake samun yar uwarsa. Ya fada masa asibitin da suke kafin ya kashe wayar ya shiga dakin futu da aka kwantar da ita bayan an gama mata komai, sai jiran farfaɗowar ta suke...©️ AMYSHERH
YOU ARE READING
UWARGIDANA
AdventureLabari ne da ya ƙunshi abubuwa masu tarin yawa ƙaddara, soyayya, hakuri, zazzafan kishi....