015

1 0 0
                                    

UWARGIDANA
(...Ɓakin Ƙishi)





°📖Page Quinze📖.




kwatsam bayan wata uku da fara tafiya Salah makaranta wata safiyar talata aka koro shi daga makaranta... Ya zo yana kuka yana majina yake faɗa wa Aïda ai an kore shi daga makaranta bada hakkinsa ba, shi bai yi komai ba. Aïda cikin tashi hankali tasa shi gaba suka tafi makarantar tare dan jin abinda yasa aka koro shi bayan yanzu kamar ya maida hankalinsa ga karatun.

Bayan ta samu shugaban makarantar abin da kunnenta suka jiyo mata ya fi komai tada mata hankali, yana faɗa mata ne sam baya son Salah a cikin makarantar sa saboda makarantar an hana shan taɓa da duk wani kayan shaye-shaye a cikin ta amma shi Salah haka yake zuga guda na dalibai su sha taɓa an hana shi yaƙi hanuwa har wasu dalibai ma sun fara kwaikwayon sa ganin haka yasa suka koreshi dan kar ya gurbata tarbiyyar wasu yaran ma.

Aïda sosai ta kadu da jin wannan labari daga baƙin shugaban makarantar saboda ita bata san Salah yana shan taɓa ba sai a ranar.
Hankalinta sosai ya tashi nan ta bawa shugaban hakuri akan ba zai kara ba in sha Allah zata mishi magana, sam ya ƙi yarda saboda cewa ya yi har kuɗin da suka biya zai maida musu saɓar bai son ganin Salah a makarantar sa su kaishi wata makarantar. Saboda Iyayen dubban dalibai sun shigar da korafi kan lalacewar tarbiyyar ya'yansu hakan yasa aka kore shi kuma basa buƙatarsa.

Bayan ta ji duk bayanan da shugaban makarantar ya yi dole ta hakura ta kyale maganar komawarsa makarantar suka komo da shi gida. A hanya sai ƙaryata shugaban makarantar yake akan sharri yake masa shi bai shan taɓa, Aïda dai bata sake ce masa komai ba saboda kunya ma take ji yanzu sai ai zaton ɗanta ne kuma bata bashi tarbiyya ba, bayan haka ta iske su.

Da daɗɗadar bayan Khalil ya dawo sunci abinci  sun kare suna hira take labarta masa abinda ya faru da Salah dan kar yaga ya daina zuwa makaranta, da kuma abin da yasa aka kore shi wanda shugaban makarantar ya fada mata, shima sosai ya ji mamaki hankali shi ba karamin tashi ya yi ba, amma ba yanda zai yi tunda y'ara dai Halima ta gama bata musu tarbiyya, banda rashin tarbiyya taya y'aran da haifa ace suna gaba da mahaifinsu kuma a cikin gidan sa duk da sunce ko yana so ko baya so dolensa ya zauna da su dan ba inda zasu nan ne gidan su. Haka ya zuba musu ido yaƙe kallonsu ko ya hadu da su a farfajiya gida haka zasu wuce shi ba tarbiyya ko kaɗan kamar zasu bangare shi wani lokaci dole shi zai tsaya musu su wuce... Shi inda yasa  alamurran y'aran nan a ranshi da warhaka ya dade da mutuwa. Ya can zancen zuci ya ji Aïda na sake kawo shawarar mai zai hana ya bude wa Salah shago tunda bai son bokon, da zamansa haƙa a gida?
Khalil  sai da ya kalle da kyau yace sam bai san da wann maganar ba tunda shaye shaye yasa a gaba ko an bude masa shago haƙa zai tattara abokai cikin shagon su kashe shagon ba uwar riba bare riba.

Rayuwar gidan Khalil sai a hankali kullum cikin fargaba da tashin hankali nake kwana nake tashi, saboda Ni dai ban taba ganin gidan da y'ara suke son kashe mahaifinsu dan kawai mahaifiyar su ta dawo cikin gidan ba. Ya'yan mijina ko wane wayewar gari sai sun fito da sabon salo na tashi hankali. Har auren ya fara fita daga kaina saɓar rikici da tashin hankali, gashi dai Halima bata gidan amma da ita da wanda yake cikin gidan duk daya ne, kai Ni gwamma lokacin da take nan nasan ina kishi da kishiya akan yanzu da na rasa da wa nake kishin?

Ban san cewa auren mai mata kuma da ya'ya manya sa'annina tashin hankali bane sai na shigo gidan Khalil, kafin muyi aure duk abinda ake faɗa min kan mai mata gani nake kamar kawai ba'a son na auri Khalil ne.
Duk bin boka ake fadin matar shi tana yi ban yarda ba a wancan lokacin saboda so ya rufe min ido.

Balle Yaya Aïcha da kullum take nusar da Ni akan na rabu da mijin wata na yi na kaina, saboda tafi son na auri mara mata Ni kuma a lokacin soyayyar Khalil ne kaɗai a gabana dalilin da yasa nake ganin kamar Yaya Aïcha tana ƙin Khalil ne. Ashe ita akwai abinda take hango min wanda Ni a wancan lokacin ban hango shi ba sai da na shigo cikin gidan.

UWARGIDANAWhere stories live. Discover now