UWARGIDANA
(...Ɓakin Ƙishi)°📖Page Sept📖.
Dumm! Ta ji saukan abu, Zuwa wani lokaci kuma ta ji shiru.
Cikin sauri ta bude idanunan ta da suke a rumtse jin shiru bata ji zafin bugun a jikin ta. Tun lokacin da ta ga Halima da makeken karfe a hannu ta sadaukar kawai, Na farko ba ta da wani ƙarfi a jikinta balle ta ce zata kama Halima da kokowa wajen kwace kanta tun a asibiti likita yace jikinta yana bukatar hutu ita ta nemi sallama lokacin sallamar ba yi ba, na biyu inda aka dinka mata yana mata wani azababben ciwo har lokacin wanda yasa take takawa a hankali dafe da inda yake ciwon da hannun dama tana yamusa fuska. Kawai karfin hali ne yasa take motsa jikin banda haka ita kaɗai tasan abin da yake wakana a cikin jikinta dalilin da yasa ta rumtse idanunta ta sadaukar take jiran saukan abin da ta gani a hannun Halima wanda tuni ta iso gabanta. Sai dai abin mamaki ta ji karar bugu tabbacin an kwalawa mutum amma kuma bata ji zafi ko wani abu daga jikinta ba, sai wani daɗɗadan kamshi da ya bugi hancinta wanda ya zarce ƙwaƙwalwarta, ga wani lallausan hannu da kakkarfan hamtse da ya kewaye ta, inda ta yi luff ta shige cikin faffadan kirjinsa kafin ta sake rufe idanunta tabbacin tana cikin ƙariya, sai sauraron yanda bugun zuciyarsa yaƙe take, wanda yaƙe daidai setin kunnen ta."Ka gommace na kashe ka a madadin ta ke nan Khalil?" ta tambaya fuska cike da mamaki, Sai ta jefar da ƙarfen dake rike cikin hannun ta wanda da niyyar ta ta kara kwalama Aïda shi, ta fara tafa duka hannayen ta biyun tana fadin
"Ya yi kyau Khalil! Ya yi kyau na ce! ranka fansa ke nan a gare ta" Ta yi wani murmushi mai daci inda ta ba wa hawaye daman sauka daga cikin idanunta ta fara ja baya da baya tana kallon su har ta je bakin kofar gidan ta dauki jakarta wanda ta yasar tun lokacin zuwan ta a inda yake, ta juya zata bar wajen sai kuma ta kasa tafiya ta tsaya kallon su cikin daci da kunan rai. Da sauri mai ɓalle kofa ya duka ya dauki ƙarfen ya bar wajen cikin sauri-sauri da gudu-gudu dan kar ma Khalil ya waiwaye sa.
Da sauri Aïda ta sake bude idanunanta jin kalmar da yake fitowa daga bakin Halima cikin hargowa da daga murya kamar wata zararriya, nan Aïda ta fahimci ashe *mon bonheur* in ta ne ya fansheta inda karfe ya sauka jikinsa.
Ta yi saurin daga kanta dan ta kalle shi sai ko ta yi sa'a shima ita din yake kallo cikin so da kauna, idanunsu na sarkafewa cikin juna ya sakar mata da wani kayataccen murmushi kafin ya kashe mata ido ɗaya sannan ya daga gira ɗaya sama alamar tambaya
Sai ta girgiza masa kai cikin maida masa da martanin murmushi zuciyarta cike da son sa da jin dadin samun sa matsayin miji a gare ta, ta sa duka hannayen ta biyu ta rungume shi basu san da wanzuwar wata halitta wai ita Halima ba a wajen, da yake unguwa ce ta masu kuɗi yasa ba ka ganin gilmawar mutane sosai sannan lokaci kowa yana wajen aiki, sai da suka gaji a haka kafin suka saki juna cikin sauri Aïda ta koma bayan shi ta fara taɓa shi, daidai wajen da ƙarfe ya sauka nan hannun Aïda ya sauka a bazata nan da nan ya ce "Wasshh kin ta bo wajen mon amour". Cikin sauri ta dauke hannun ta daga wajen tana fadin "Sannu" cikin tausaya masa Duk ta shiga damuwa kamar zata yi hawaye.Hannunsu sarkafe cikin juna suka fara takawa sannu a hankali har suka isa gaban kofar gidan inda Khalil ya fito da key cikin aljihu ya buɗe musu gida suka shiga, Halima ta take musu baya zuciyarta kamar ya fito daga cikin kirjinta haka take ji saɓar tsanar da take wa Aïda yana kara sananta, idanun ta kuma kamar su fado kasa saɓar harar.
Cirko cirko a tsaye suka iske 'yaran a farfajiyar gida, da sauri sukayi wajen mahaifiyarsu suka rungume ta, ba su kalli inda mahaifinsu yake ba balle yasa ran gaisuwa daga gare su, shima bai nuna ya gan su ba suka yi sashen Aïda tare inda yake taimaka mata.
Bayan buɗe ɗakin idanunta suna sauka kan kayayyakinta masu tsada da suke farfashe, zuciyar ta ya buga ta kau da kai da barin kallon dakin ta juya zata bar wajen sai ta tsaya can nesa da kofa take karewa falo kallo lungu da tsako tana takaicin wannan rashin tarbiyya da 'yaran suka nuna mata, ta yi nisa sosai cikin tunani ta ke jin maganarsa sama sama
YOU ARE READING
UWARGIDANA
AdventureLabari ne da ya ƙunshi abubuwa masu tarin yawa ƙaddara, soyayya, hakuri, zazzafan kishi....