UWARGIDANA
(...Ɓakin Ƙishi)
°📖Page Quatorze📖.
HaLiMa
Maimakon na zarce gidana sai nayi masauki a gidan kawata kuma aminiyata Maimuna wacce muke kashewa kuma mu binne ba tare da wani ya ji ko ya gani ba. Abotarmu da amintarmu ya dade da kafuwa ta dalilin abotar mazajenmu... An ce sai hali ya zo ɗaya ake abota, to ina da tabbacin namu dai halin ya zo ɗaya
"Subhanallahi! Me zan gani haƙa? Halima ya na gan ki cikin irin wannan hali? Abu ne ya faru da y'aran?"
Ta jera min tambayoyi cikin tashin hankali bayan ta rungume ni, kafin muka zauna saman kujera mai cin mutum uku tana kallona, har lokacin na kasa furta mata ko kalma ɗaya. Abinda ya faru a gidan Khalil shi yake ci min zuciya, tun cikin adaidaita sahu nake saka ina warware wa, dalilin da yasa tun farko ban son kishiya ke nan, gashi abinda nake gudu ya faru, humm.
Sai sauke numfashi nake ina fesar da iska mai zafi ta baƙi ganin haƙa yasa da sauri Maimuna ta mike ta je ta bude firij ta dauko mini ruwa mai sanyin gaske ta mika min tana fadin"Karba wannan ki dan sanyaya zuciyarki! Dan Allah me ya faru ne? Ko dai har yanzu maganar y'aran nan ne ke damunki? Ki bar damun kanki akan y'aran nan fa In sha Allah baza a kai su gidan kaso ba"
Ni dai bance mata ci kanki ba, saboda in na tuna abinda ya faru sai naji zuciyata ta yi min nauyi ga wani abu mai daci da ya tokare min makoshi shi bai fada ba, shi bai fita ba, cikin ƙarfin hali na girgiza wa kawata kai alama ba wannan ne yake damuna ba
"Tun fa da kika shigo nake tambayar ki amma har yanzu kin kasa magana. Ke da wa? me ya faru? Dan Allah ki bude baƙi kiyi min bayani kin bar Ni cikin tashin hankali"
Ta karasa fada yayin da ta kamo duka hannayena biyu ta rike su cikin nata tana kallona, duk da haƙaMaimakon na amsa tambayoyinta sai na fashe da kuka wanda tun dazu nake son yin sa amma ban samu ba sai yanzu, kuka nake tun ƙarfina kamar wanda aka daka, kuka da yake fitowa daga can kasan zuciya, kuka ne kadai zasu wanke min tsasan da ya daskare cikin zuciya, yau na zubar da hawaye saboda baƙin cikin da Aïda ta kusa min, yarinyar da na so hanata zaman lafiya da kwanciyar hankali yau ita ce take neman samin hawan jini take son taga numfashina ya tsaya, Inna lillahi wa Inna ilaihiraji'un abin da nake ta maimaita wa ke nan a can kasan zuciyata.
Inda na san haka zata faru da tun farko lokacin da take bina sau da kafa don mu zauna lafiya na yarda na zauna da ita lafiya, da yanzu ina can gidan mijina cikin ya'yana.'Baƙin kishina ya hanani zama a cikin gidan da muka ginashi Ni da mijina gashi yau Ni ake nuna wa gadara. Wai ma laifina ne ko na Khalil? Inda bai kara aure ba ai bazai taɓa wulakantani ba'
Da kyar na iya buɗe baƙina na labarta abin da ya faru tun daga station har zuwa kofar gidan.
Ruwan sanyi nan kam sosai ya taimaka min saboda tas na shanye shi sai a lokacin nasan lalle na kwaso ƙishirwa.
Maimuna kam bayan ta gama jin bayani kasa magana ta yi saɓar mamaki, har lokacin hannayenmu rike da juna, kafin na raba na fara share hawaye da suke tserere saman kumatuna, cikin murmushi mai ciwo nace mata"Ba abinda yake kona min rai a halin yanzu kamar kalmar da Khalil ya fada mini"
"Wanne ke nan daga cikin kalmomin nasa?"
"Hum inda yace min: Ke a wa! Za'a bude miki wannan kofar, in kina so ki bi inda matar gida ta bude, in kuma bai miki ba kina iya komawa inda kika fito"
"Tabbas da ciwo amma dole zaki hakura sannan yana da kyau kina kau da kai ga wasu abubuwan in ba haka ba ki kamu da ciwo kinga su dai ba asarar su a ciki"
"Haƙa ne, gaskiya kuka ma rahma ne tunda na zubar da wannan hawayen kaso saba'in ciki dari na damuwa da nake ciki sun tafi"
"Shi yasa na kyale ki lokacin da kike kuka ban hanaki ba"
YOU ARE READING
UWARGIDANA
AdventureLabari ne da ya ƙunshi abubuwa masu tarin yawa ƙaddara, soyayya, hakuri, zazzafan kishi....