UWARGIDANA
(...Ɓakin Ƙishi)Mallakar :
©️ AMYCHA°📖Page Seize📖.
AïDa
Humm mai yake so na faɗa masa ke nan?
Ko so yake na tashi hankalina na yi hauka kamar yadda matarsa HALIMA ta yi?
Indai wannan gidan ne wallahi ina maraba da duk wanda zata shigo duk da ina sananin son mijina amma hakan ba zai sa na tashi hankalina ba.
Maza ke nan idan sun yi niyyar kara aure, zuba musu ido kawai, sannan dole zaki kai zuciya nesa saboda wasu abubuwa da zasu fada maki ke kanki kasan sun fade shi ne kawai saboda basu da makama wajen faɗin dalilin da yasa suke son kara auren, sannan abin takaici basa taɓa cewa za su ƙara aure saboda ra'ayin kansu ko kuma saboda Allah ne ya halasta musu. Dole sai sun kirkiro wani dalili sun daura wa matar gida kamar dai gazawar ta yasa za a kara auren bayan kuma ba haka yaƙe ba.KHALIL ya kalli saɓar idona yake gayamin zai kara aure ne kawai saboda y'aransa sunce basa jin daɗin abincin da mai aikinsu take dafa musu, hum wannan har ya kai hujjar da zai sa ya kara aure ne? Me yasa ba zai ce min kawai zai kara aure ne dan yana ra'ayin hakan ba? Sai dai ya yaudareni da wani magana mara tushe. Yo mara tushe mana wannan har ya kai a kara aure saboda shi?.
Haka lokacin da yake neman aurena yace min zai kara aure ne saboda yana son macce mai ilmi a kusa da shi, saboda ta gida bata da ilimi (HALIMA ke nan) sannan shi babban mutum ne yana yawan zuwa manya-manyan taruka saboda haka yana da bukatar mace mai ilmi da gogewa a kusan shi, yanzu kuma ya fake da hujjar y'ara.
Cikin danna duk wani abu da yake son bayyana a kan fuskata na fara magana
"Amma me zai hana ka ɗaukar musu wata mai aiki, tunda matsalar ke nan ta rashin iya abinci ne? Kuma ga Falmata nan ta dafa musu wanda suke so din mana tunda ita ma macce, ita kuma laure(mai aiki) ta yi musu shara, wanke-wanke, wanki da dai sauran ayyukan duka"Na kura masa ido ina kallonsa da nazartarsa, sosai na kafe shi da idanuwa ina jiran jin amsar da zai bani, sai ya fake da wani irin malalacin murmushi kafin ya jawo ni jikinsa ya rungume ni a tare muka sauke wata irin ajiyar numfashi, ya fara min magana a kunne kamar mai rada yana
"Kin manta FALMATA na zuwa boko ne, yaushe zata dafa musu? Kin fi kowa san halin y'aran ai, yanzu sai na dauko wata mai aikin su buge da kawo wata matsalar, wannan ma kullum cikin zubar da abincin suke gashi ba cin naki suke ba ɓalle na ce ki ringa sa musu, shi ne...."Na yi sauri katse shi da fadin "ca nake wannan amintacciyar mai aikin mahaifiyar su ce, sannan ko lokacin da Halima take nan ita take dafa musu abincin suke ci ya aka yi yanzu ya zama bata iya ba?"
"Kin san me? Ba zaki gane bane y'aran ne wani lokaci sai a hankali. Idan na auro ta zata fi kula da su a kan na sake dauko wata mai aikin sannan za su fi darajata akan mai aiki" yana maganar ne cikin sarkafe harshe da kame-kame
Na yi wani murmushi mai sauti
"Hum wannan bai kai hujjar da zai sa kace dalilin kara aurenka ke nan ba.
Ca nake nima a matsayin matarka nake amma banga sun darajani ba, farkon zuwana har abinci nake hada muku amma karshe da me suka saka min? Na ji zaka auro ta ne dan ta dafa musu abinci, yanzu misali idan ka auro ta ta zo bata iya abinci yanda suke so ba, in suka sake maka korafi sakinta zaka yi ka kuma auro wata ke nan, tunda saboda su ka auri ta?"
Sai ya kara matseni a jikinsa gam yana murmushi mai sauti daidai wuyana, ya kasa fadin komai ya dago yana kallona, na daga masa gira daya alama ina jinka kai nake sauraro sai ya fake da faɗin"Kin san shi aure nufi ne na Allah kuma kinga ke kina zuwa makaranta ita waccan din jahila ce bata boko ba arabi kawai ina son ta kulla da yaran ne kawai. "
YOU ARE READING
UWARGIDANA
AdventureLabari ne da ya ƙunshi abubuwa masu tarin yawa ƙaddara, soyayya, hakuri, zazzafan kishi....