UWARGIDANA
(...Ɓakin Ƙishi)°📖Page Deux📖.
25032024Sosai ya tausaya mata na halin da ta shiga ta dalilin sa 'E, ta dalilin sa mana, saboda dan ta aure shi ne duk wadannan matsifun suke afkuwa da bibiyarta' ya furta cikin zuciyar sa. Ga shi bata da kowa a garin sai Allah sai shi, saboda shi ya rabata da garinsu da dangin ta ta dalilin aure ya kawo ta wannan jaha, ga ta marainiyar Allah yanzu me zai ce da 'yan uwanta idan sun ji, kuma idan suka tuhume shi yanda abin ya faru, da wane yare zai fahimtar da su su san ba laifinsa ba ne, bare ma babbar yayarta wacce dama ita bata bari ta kwana kuma dama ita yake ji ma, idan ta ji labarin a yau yau din nan zata shigo mota ta zo garin kuma sai an yi gagarumar tashin hankali. Hakan ya kara jefa shi cikin tashin hankali duk da shima jira yake ta tashi ko zai samu sukuni cikin zuciyarsa kafin ya je ya hukunta y'aran nan, amma tabbas yasan danginta sai sun dau mataki kuma wallahi duk matakin da zasu dauka ba zai taɓa cewa komai sai dai ma ya goyi bayan su, shi yanzu sa'ar sa ɗaya ma da Allah yasa akwai ɗan uwan ta a garin wanda shima bai jima da zuwa garin ba ta dalilin aikin gwamnati da suka maido shi zuwa nan banda haka yau da ya zai yi da wannan tashin hankalin da y'aran nan suka jefa sa?
"Hum Yaya Aïcha kam ba yarda za ta yi ba da duk wani fujjarsa, duk yadda zai kwatanta da nuna mata bada saninsa abun ya afku ba dole ne sai ta ga laifi, sakaci da gangancin sa a cikin wannan lamarin, ga shi har lokacin matarsa bata farfaɗo ba" yana gama maganar zuci ya fesar da wani isa ma zafi daga bakinsa.
Shi yanzu ko ɗan uwan nata in ya zo da wane ido zai lalle shi, dama-dama ma da yake shi din namiji ne wata kila zai fahimce shi. Sai tufka yake yana warware wa.*** *** ***
Kyakkyawa da ita ga ta da kananun shekaru saboda sa'ar y'arshi ta fari ce, hancinta zuwait kamar biro yayinda baƙin yake daidai da farar fuskarta, idanun ta a lumshe suke amma duk da hakan bai hana aga girman su ba.
Fuskar ta fayau sai 'yan raunuka da aka yi bandejinsu tana kwance saman gadon asibitin yayin da sérum biyu yake shiga cikin jinin jikinta a lokaci daya, yayinda ɗayan na karin ruwa ne wanda tuni ya ƙare sai ɗayar na karin jini ne inda ƙarar na'ura kadai ke tashi a cikin wannan dakin. Yayinda shi kuma yake zaune gaban ta saman kujera kan sa saman gadon da take kwance yana rike da hannunta daya yana man-matsa yatsun hannun wanda suke cike da laushi da santsi farare sol da su yana shafawa da mirza su a hankali. Allah-Allah yake ya ji ta motsa ko hankali sa zai kwanta, yana cikin wannan halin ya ji sallamar sa, nan da nan zuciyar sa ta halba da sauri-sauri. Haka dai ya maze ya juyo suka hada ido nan da nan ya kawar da nashi saɓar kunyarsa da yake shi, ga shi dai shine babba amma tun da abun ya faru yake jin kunyarsa bayan shi kuma ɗan uwanta bai nuna masa wani abu ko alama na ɓacin rai daga fuskarsa ba, amma tabbas yasan yana cikin tashin hankali shima tunda har kawo wannan lokacin babu wani ci gaba da suka ga tattare da ita illa sai ƙarin ruwa da likitoci suke mata akai-akai."Ka bar damun kan ka, haka Allah ya ƙaddara mata fatan mu dai Allah ya tashi kafadun ta"
Ya sinci tashin amon muryarsa cikin ƙwaƙwalwarsa, nan da nan ya dago ya kalle shi kafin ya amsa masa da
"Amine Lawan!! Ba zaka gane ba ne amma wallahi ina cikin tashin hankali sannan wallahi lokacin da ma ta kirani ban yi jinkirin isowa ba, kawai dai ƙaddara ta riga fata ne, dan Allah kuyi hakuri""Haba Khalil! ka daina damuwa da daurawa kanka abin da Allah ne kadai ke da iko mana, kwantar da hankalin ka na fahimce ka, har dai muga tashin ta?"
"Ai dole hankalina ya tashi! Ina fa naga kwanciyar hankali in bata tashi ba! Na gode da ka fahimce Ni, amma akwai sakacina ciki. Yauwa dan Allah nace, ko, ka fadawa can 'yan gida ne? Ni wallahi kunya yasa na kasa kiransu" cikin raunaniyyar zuciya ya gama fada, yayin da yake ƙoƙarin raba hannun sa dake cikin na matarsa wanda yake wasa da yatsun tun dazu da tashi.
"E, na fada musu, sannan sun tambayeni ya jikinta nace da sauki. Shi ne suka nemi yin magana da ita sai nace dasu tana barci, yaya Aïcha tace sai ta zo duba ta, ina ma kyautata zato yanzu haka tana hanya, duk da nace ta zauna ba wani ciwo ta samu sosai ba dan dai kawai na kwantar mata da hankali, amma tace sam" yana maganar ya karaso gaban gadon da yar uwarsa take kwance kai, ya kare mata kallo sai ya ji zuciyar ta yi rauni sosai sannan ya tausaya mata.
Gaskiyar magana idan ya ce bai ji haushin abinda y'aransa suka aikata wa yar uwarsa ba ya yi karya sannan ya ji ciwo sosai da ganin halin da take ciki, amma da yake shi namiji ne shi yasa ya danne fushinsa da zuciyar sa ganin yadda shima mijin yake cikin tashin hankali.
Sannan lokacin da ya kira gida ya labarta musu abin da ya faru da 'yar uwarsu kamar yadda mijinta ya fada masa sosai hankalin su ya tashi nan ko wannensu ta fadi albarkacin bakin ta inda suka yi alwashin zuwa su daukarwa 'yar uwarsu fansa.
Yayinda shima da kyar ya samu ya lalashe su akan shima jira ne ke ta tashi ya ji ta baƙin ta kafin ya dau mataki, ba zai taba barin jininta da suka zubar ya tafi a banza ba
Nan yaya Aïcha tace sam ba zancen su zauna su duka a gida dole sai sun zo ita da yaya Fatimah (wacce take bi mata) sannan duk abinda ake ciki gaban su za'ayi shi a kare.*** *** ***
Bangaren Khalil kuwa shi kadai yasan halin da zuciyar sa take ciki, shi babbar tashin hankalinsa har yanzu bata motsa ko da ɗan karamin yatsanta ba.
Sai safa da marwa yake goye da duka hannayensa biyu a saman gadon bayan sa yana safa da marwa daga bangon dakin zuwa gaban gadon cikin sananin tashin hankali. Yana cikin wannan halin fiye da awanni yayinda tunani ma kasawa ya yi, can kamar ance masa duba can yana juyawa yayi arba da kyakkyawar idanun ta farare tas suna kallon sa, yayin da ya hango ɓ'acin rai mai sannani cikin su, bata ce da shi komai ba illa ƙoƙarin tashi da take son yi amma sai ta gagara, ganin haka yasa bai yi wata-wata ba ya kara sa wajen ta cikin zafin nama yana murmushi hade da hamdallah ya rungume ta yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya dan tunda da ya kawo ta asibitin nan bai je ko nan da can ba, in banda sallah da yake zuwa masallacin asibitin yanayi yana dawowa, abin mamaki ko yunwa bai ji ba tun dazu sai yanzu da yaga ta farfaɗo tukun ma ya tuna rabon shi da abinci tun jiya da safe kafin ya fita office da ta haɗa masa petit déj da ya ci tun shi bai sake cin komai ba sai yanzu wajen karfe ukun dare(3h) da ya ji cikinsa na kugun yunwa.
Bayan ya gama sauke lodi-lodin ajiyar zuciya kuma har lokacin bai sake ta daga rungumar da ya yi mata ya fara jera mata da tambayoyi cikin rawar jiki murya cike da zallar farin ciki"Mon amour sannu, ya jikin? ina yake miki ciwo yanzu?" Yayin da yake tattaba jikin ta amma bai taba inda ciwon yake ba, ita kuma har lokacin idanu kadai ta zuba masa tana kallon shi yayin da ƙwaƙwalwarta ya shiga tuno mata abinda ya wakana a jiya da misalin karfe sha daya na rana (11h) sakaninta da y'aransa. Ganin yana ta magana shi kadai bata amsa masa ya ci gaba da fadin
"Bari naje na kira docteur ya zo ya duba min ke, shirun ki yana kara jefa zuciya ta cikin tashin hankali, dan Allah ki ce min wani abu mana..."Wani hara da ta wurga masa shi ya katse masa maganar sa, yayinda ta fara ƙoƙarin raba jikinta daga rungumar da ya yi mata. Inda shi kuma ya fita zuwa kiran likita yayinda yake ayyana a ransa dole ta harare sa ya cancanci fiye ma haka. Amma shi yanzu damuwarshi ta samu lafiya.
Bayan isar sa ofishin likita ya sanar musu da ta tashi amma bata magana nan suka jera shi da wani likita suka zo.
Likitan ya duddubata ya yi mata 'yan gwaje-gwajen sa ya tabbatar da ba wata matsala bayan ciwon kasan mararta da suka gyara da yan raunukan fuskarta bayan wannan babu wani matsala jikinta. Nan ya fara cire mata ruwan dake jikinta yayin da yake tambayar ta inda yake mata ciwo, ta amsa masa da "Nan" yayin da take nuna kasa mararta wanda take jin wani azababben ciwo tana yatsina fuska saboda da ciwo. Khalil ya bude baƙi cikin mamaki yana kallon ta, shine tun dazu yana mata magana ta ƙi amsa masa sai yanzu ta amsa wa wani gardi daban. Hmm ya yi mata uzuri ba damuwa shi mai laifi ne wajen ta, ya sinci muryar likita ya na fada mata"Kar ki damu shima zaki ji sauki ne in sha Allah, yanzu jikin ne ba kwari, sannan ki daure ki sha wani abu mai dan zafi-zafi hakan zai taimaka wa cikin naki sosai"
Cikin fuskar ciwo ta amsa masa "Bana jin cin komai a yanzu, sallah kadai nake son yi"
"Ki daure haka nan ki sha wani abun zai kara wa jikin ki kuzari da karfi har ki samu kiyi sallah"
"To zan gwada sha" bata gama rufe baƙin ta ba har Khalil ya haɗa mata tea mai kauri yana meka mata yayin da tuni likita ya bar musu dakin.
Ta ko karba ta sha sosai ta rage sauran kaɗan shima dan ta koshi ne, sannan taji dadin sa sosai saboda saukar ruwan zafin sosai ya dumama cikin.Khalil kam sai murmushi yake ta zabgawa
Haƙoran nan kamar gonar auduga ana washe ta yayinda uwar gaiya ta yi burus da shi kamar baya wajen. Inda da kyar ta kokarta ta shiga toilette dan yin arwallah, lokacin da Khalil ya je taimaka mata ta saka masa kuka tana wasu maganganu wanda dole yasa ya sake ta jikinsa duk ya yi sanyi...©️ AMYSHERH
YOU ARE READING
UWARGIDANA
AdventureLabari ne da ya ƙunshi abubuwa masu tarin yawa ƙaddara, soyayya, hakuri, zazzafan kishi....