013

1 0 0
                                    

UWARGIDANA
(...Ɓakin Ƙishi)




°📖Page Treize📖.




"Abar kauna ina godiya sosai, Allah ya miki albarka yaji kan iyayenki" ya fada bayan ya sake ta daga rungumar da ya yi mata.

"Ameen" ta amsa daga shi ban sake ce masa komai ba face kallonsa da nake yi, sosai na ga farin ciki mara misaltuwa shimfide saman fuskarsa, lalle sakanin wannan Uba da ya'yansa sai Allah. Saboda bayan cike-ciken takardu wajen saka hannu a takardar sakin  y'aran da yarjejeniyar masu yawa da sa hannunsu da na mahaifiyarsu, Ko inda Khalil yake basu waiwaya ba ɓalle nasa ran zasu mana godiya haka shima mahaifinsu.
Mahaifiyarsu kaɗai suka runguma bayan komai ya daidaita sukai ta kuka wanda yake bayyana baƙin cikinsu da kuma farin cikinsu.
Ita kuma fadi take tana kara wa cikin kumar baki  "Ku kwantar da hankalinku dole ma za'a sake ku, dan ba uban da ya isa ya kai min ya'ya prison" tana hararar inda nake zaune. Banda murmushin kalaman Halima ba abinda nake, Inspecteur da Khalil duk suma mamakin furicinta da ƙarfin hali irin nata suke. Haka ta yi ta habaice-habaice ba wanda ya kula ta balle ace an ji, ta gaji dan kanta ta kyale.

Ganin yana ta magana shi daya na ƙi tanka masa yasa ya tada motarsa muka fice daga ofishin bai hakura da  jana da hira ba wanda yawanci shi yake hiransa saboda ni dai a wannan lokaci ba abin da yake damuna da amsa amo a cikin kwakwalwa da kunnuwata sannan ya tsaya mini a rai irin kalaman da Halima ta yi mini, wacce sai da ta zo dab da ni ido cikin ido ta fada min shi cikin rada saboda sosai ta yi kasa da muryarta duk da ina da tabbacin Khalil yana iya jinmu saboda kusancin da nake da shi ta hanyar zama saman kujera daya.

Cikin tsantsan tsana da baƙin ciki ta fara faɗin
"Na tsaneki Aïda! Na tsaneki! Na tsaneki! Ina da dama da wallahi sai na kashe ki har kushewa. Ki rubuta ki aje ba ke ba haifuwa a duniya. Kin san ba abin da ya fi ciwo ga 'ya mace ta zo duniya bata samu haifuwa ba ko? To ki sani ki kara sani ba zaki taba haifuwa ba sai dai ki ji ana yi a makota"
Ta kara sa fada fuskarta ba digon annuri ko kadan sai ma tsanata da nake hangowa kara cikin idanunta.
'Wai dama mace mai zafin kishi haka take?' na tambayi kaina saboda ban taba zaton kishin Halima ya zarta tunanina ba sai a wannan lokacin, duk lokacin da Khalil yake faɗa min yanda take kishin sa ban dauka ya kai har haka ba, duk da ta yi iya kokarinta wajen ganin ta hana aurena da khalil amma hakan bata samu ba saboda Allah ya riga da kurta ba wanda ya isa ya hana. Ban san na fada duniyar tunani lokacin da take faɗa min maganar ba sai da na ji tana wani makirin murmushi mai sauti, abinda ya anƙarar da Ni kenan na yi sauri kawar da damuwar da yake son shimfiduwa saman fuskata na maida mata da murmushi ina lumshe ido alamar ta ci gaba da maganar irin ban ji zafinsu ba

Daga nan ko kalamanta sosai suka yi tasiri a zuciya da ƙwaƙwalwata sannan ya nakasa min abubuwa da yawa a jikina, tabbas rashin haihuwa ga ya mace wani babban nakasu ne ko da kuwa ace Allah haka ya halicce ka, balle ka ji wata tana i kirarin da sa hannunta dole wani abu ya darsu cikin zuciyarka komai imanin ka. Amma kuma dole na nuna wa Halima hakan ba wani abin tashin hankali ko damuwa ba ne, saboda Allah yake bada haihuwa ba mutum ba.

Na aro jarumta na kara yafa a kan fuskata cikin murmushi mai sanyi amma ga duk wanda yasan da shi ake yasan cewa wannan murmushin ya kunshi abubuwa da yawa, cikin sanyin muryara da ya zame min jiki na amsa mata "Allah me iko! To sai ki amshi raina mana Halima tun da ke kika busa min shi "  Na tsagaita da maganar ina kallonta itama har lokacin Ni take kallo kamar yadda nake kallon ta, amma saɓanin ita da  naga ta zaro ido waje ta kara wa idanunta girma irin kamar ta ji mamakin jin martanin ko wani abu haka daga gareni.

Na ci gaba da faɗin  "Eh! Tabbas Kamar yadda numfashina ba'a hannun yake ba, baki isa ki kashe ne ba, kuma haka ke baki isa hanani haifuwa ba muddin Allah ya kurta min haihuwa. Jahila! Me yasa ke kullum zahilcinki kara hauhawa yake? Indai irin haihuwar ki ne ai gwamma babu? Me za'ayi da haifuwa irin naki mara amfani? Ai ga irin haihuwar naki abin da ya tsinanamiki, y'aran da basu san matsayin mahaifinsu ba balle ai maganar girmama da daraja na gaba da su.... Humm bari na barki haka dan naga ƙwaƙwalwar ki  ba iya daukar abubuwa masu mahimmanci yake ba in banda maganar boka.
Ki dai ji da abin da yake gabanki, Saninki ne na fi ƙarfin duk wani bokanki jahilar banza, kamar yanda bokanki bai isa ya hanani shigowa gidan Khalil ba to ki koma ki fada masa bai isa hanani haihuwa ba muddin Allah yasa a jikina. In kin gan ban haihu ba Allah ne bai bani ba amma ba kazamai mutane irinku ba. Sannan ba kiyi mamakin furta min haƙan daga baƙin ki? Humm Halima kenan"

UWARGIDANAWhere stories live. Discover now