UWARGIDANA
(...Ɓakin Ƙishi)
°📖Page Dix📖."Bébé ya ƙarfin jiki?" bata san shigowarsa ba balle ta ce ga lokacin da ya shigo da ledodin. Sai jin hannunsa yana yawo saman wuyanta da maganarsa ta yi, shi ya katse mata tunanin da ta lula. Ta yi hanzarin bude idanunanta ta ganshi zaune bakin gadon dai-dai inda ta jingine kai, sanye da rigar shan iska irin dogayen nan ta maza mai kama da jallabiya
"E, alhamdulillah da sauki, amma sosai wajen nan yake min ciwo da zugi" ta nuna wajen da hannu tana yamusa fuska saboda ciwon da take ji a wajen ya wuce misali
"Ayyah sannu chérie! Ki kokarta ki tashi ki ci wani abu, sai ki sha magani ki samu ki ɗan huta. Akwai rashin hutu ma a tattare da ke ga shi ke kika matsa a sallameki kan zaki kula da kanki amma kin kasa, shi ya sa na so zaman ki a asibiti ai"
"Ummm" ta muskuta ta gyara zamanta
"Bari na dauko assiste/plat na zuba mana wannan abun"
"Sai ka ci zaka tafi masallaci?""Dawowa ta ke nan daga masallacin ai"
"Har an yi isha'i ke nan"
"Tuni, baki yi ba ne?" Bai tsaya jin amsar ta ba ya fita zuwa kitchen. Da kyar Aïda ta mike ta shiga banɗaki ta ɗan wasa ruwa a jikinta ta sake arwallah ta zo ta tada sallah, shi kuma ya shigo da plat da ruwan gora da zobo mai sanyi da bol biyu. Ya samu waje ya zauna ya zuba musu a plat. Bayan ta gama sallah ya ciyar da ita ya bata magani tasha kafin ya kwantar da ita saman gado kamar wata jinjira ya ja mata kofa ya fita a hankali.
*** 🤔 **** 🤔 ***
"Kawa kina ina? Ki zo ina cikin tashi hankali, yanzu zuwa na daga station an kulle min 'yara a cell saboda matsiyacir nan, Aïda ta zame min masifa da bala'i wallahi aurenta da Khalil banda jefa ni cikin alkaba'i ba abinda na ribace shi" cikin daga murya hade da ɓaci rai
"Hum Ni na rasa ta inda zan fara kawa, kuma Khalil yana kallo bai ce komai ba?"
"Ina ko zai ce wani abu bayan ta asirce shi, haka yana kallo aka sa y'aran nan cikin wannan kazanta da wari, a ciki za su kwana fa" ta karasa cikin sheshekar kuka da tashin hankali yayin da ta kara kankame wayar daga faduwa da ya kusa yi tana kallon y'aranta kanana da suke cin abinci cikin tautsaya musu, tuna cewar yayyunsu na can cikin wahala da kazanta
"Kai wannan mata ta zame mana masifa, duk inda muka buga ba Nasara, saɓar ta nuna miki ta isa yasa ta kayi y'aran police station har aka kulle su"
"Kina ina? Na yanke shawarar kai ta wajen malamin nan wanda kwanaki kike bani labarinsa dan a haukatar mini da ita"
"Ina gida yanzu na gama sallah isha'i kin san mutumin bai dawo ya yi abinci ba da na zo wallahi, amma kar ki mance abin da yaƙe sakanin ku da Aida kan harkar malamai"
"Kaiii raba ni da wannan maganar! Ta ya zan zauna ina kallo ana wahalar min da y'ara"
" Ki kara hakuri dai kar ki yi abin da zamu yi da-na-sani, ki jira in na zo zamu yi magana cikin kwanciyar hankali, yanzu halin da kike ciki na tashin hankali duk matakin da zaki ɗauka ba zai haifa mana ɗa mai ido ba, kar mu sake jefa rayuwar y'aran nan cikin wata matsala bayan wanda suke ciki"
"Shikenan sai kin zo din, dan Allah ki zo fa" cikin muryar damuwa
"Zan zo In sha Allah in dare bayi ba saboda har yanzu bai zo ya ci abinci ba kuma kin san bazan fita ba Indai bai zo ya ci ba, kawai ki kwantar da hankalin ki"
"Ina hankali zai kwanta ya'ya suna can wajen da bai dace ba"
"Shi yasa tun farko ban so wannan lamarin ba, da yake lokacin hankalin ki ya gushe kika ƙi saurarona, amma me ya sa basu ce ke kika sa su ba?"
YOU ARE READING
UWARGIDANA
AdventureLabari ne da ya ƙunshi abubuwa masu tarin yawa ƙaddara, soyayya, hakuri, zazzafan kishi....