019

14 1 2
                                    

UWARGIDANA
(...Ɓakin Ƙishi)


  MALLAKINC.B. AMYCHA

TSARA LABARI TARE DA RUBUTAWA: 
©️  AMYCHA


"Mama, Baba fa yace mu fitar da kayanki daga cikin ɗakinki"

"Meee? Ku fitar da kayana cikin daki? Akan wane dalili?"

"Bai faɗamin dalilin ba Wallahi iya abinda ya faɗa min ke nan dazu da safe"

"Babu inda za'a fitar mini da kaya wallahi suna nan daram"

"To Ni yanzu idan ya sake mini maganar me zance masa?" Ta karasa fada cikin turo baki gaba tana kallon mahaifiyarta

"Ki ce masa baza'a fitar ba inji Ni" Cikin matsifa kamar KHALIL ne a gabanta

"Amma Mama me yasa yake son na fitar masa da kayanki daga dakin?"

"Wannan tambayar ba Ni zaki yi wa ba, idan kin koma ki tambayi shi mahaifin naki, duk sai mu ji dalilinsa na yin hakan" Tana maganar cikin ɓacin rai da masifa

"Allah ya huci zuciyarki Mama, in sha Allah zan fada masa..."

Suna cikin hirar suka ji sallamar su  tare da shigowa cikin dakin ko wannensu ya samu guri ya zauna tare da  gaishe da mahaifiyarsu. Ta amsa tare da kallon su daya bayan daya, ganin yanayin Papy ya bambanta sosai da ta 'yan uwansa yasa ta tsaida kallonta a kansa tare da tambayarsa abinda yake damunsa

"Papy baka da lafiya ne, na ganka haƙa?" Tare da nuna shi da hannu

"Ina fa lafiya Mama!"

"Kamar  ya ke nan, me ya faru? Ko dai AïDa ce ta sake takuramuku?"

"Ina fa ita, ita din banza! har ta isa?" Ya amsa cikin isa kamar AïDa tana ganin shi

"Yauwaa koda na ji! To faɗa min ina jinka"  Ta juya kan sauran tana faɗin "Ko cikinku akwai wanda yasan abinda yake damunsa?"

"Ina fa muka sani, sai dai ya fada" FALMATA da Muktar suka hada baƙi wajen amsa mata tare da zuba masa ido suna kallonsa

"Wai Mama da gaske baki ji abinda jiya daɗɗadare ya faru da mu ba? an kusa kashe mu fa a gidan gabadayanmu fa?"

"Kashe ku kuma?"

"Eh wallahi, baki ji ba ke nan? Ai jiya munsha da kyar"

"Gidan nake da zan san abinda yake faruwa a cikinta? Kai kayi miki gwari-gwari yanda zan fahimta ba ka tsaya kana guntsira min magana ba"
Ta sake gyara zamanta saman canapé (capet) tare da kwantar da Abbas akan cinyarta wanda ya fara barci. Ta tattara duk natsuwarta da hankalinta ta maida shi wajen Papy wanda yake zaune cikin 'yan uwansa

"Uhmmm ina jinku?" Ta fada cikin kosawa

"Wai Mama dama Falmata bata fadmiki wannan labarin ba?" Papy ya fada yana kallon Falmata cikin mamaki  wacce ta haɗa girman sama da kasa tana jifanta da harara. Shi dai a zatonsa tuni ta fadawa mahaifiyarsu tunda ta riga su  zuwa.

Bai san cewa ita ma zuwanta ke nan bata jima ba, sannan sun iske su suna maganar da yafi daga musu hankali wanda mahaifinsu ya aiko Falmata dan ta fadawa mahaifiyarsu, su kuma basu san da maganar ba saboda lokacin basa gida sun fita.  Kafin su gangara zuwa kan maganar ne su kuma suka shigo.
Sai dai kafin ita FALMATA ta amsa masa, suka ji maganar sa cikin kwanciyar hankali yana faɗin

"Haba Mama faut pas faire l'innocence là (ki daina nuna ba baki san komai ba mana)

"Kamar ya? Ta ya zan san abinda yake faruwa da ku a gidan mahaifinku?

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 22 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

UWARGIDANAWhere stories live. Discover now