UWARGIDANA
(...Ɓakin Ƙishi)°📖Page Douze📖.
Cikin kasala da wani irin murya mai zakin sauraro ta fara wa Khalil magana wanda shi tuni kamshin jikinta da yanda take narke masa a jiki ya saukar masa da wata kasala mai wuyar fassara, ya shiga cikin wani irin yanayi idanusa a lumshe suke kamar mai bacci, bayan shi kadai yasan halin da yake ciki da abinda yake gudana a wannan gangarar jikin nasa, can sama sama yake jin maganarta abinda ta furta na ƙarshe shi ya zaburar da shi. Bai san lokacin da ya bude idanunsa da suka sauya kala saɓar yana cikin yanayi ya kafeta da su, so da kaunar ta na kara fuda duk wani sassa na jikinsa suna kara nutsewa cikin jini da soka.. tabbas yasan Aïda ta daban ce a duniyarsa, samun ta babba nasara ce. Zuciyarta cike take da alheri shi yasa lokacin da ta yi ƙarar su Papy bai ce mata kalla ba saboda yasan ba yin kanta bane, yaya Aïcha ce tushen hakan sannan wala Allah hakan zai sa yaran su daina takura mata ko su fara shakkar ta
"Mijina farin cikin ruhina ina neman alfarma ɗan Allah ka yafeni, gani gaban ka ina mai neman yafiya a gare ka, nasan na bata maka, Ni mai laifi ce, ban ji Kunya na yi ƙarar ya'yana station, ka fahimci ni ban yi haka don bata maka ko tozarta ka ba, sai dan ya zame min dole ita ce hanyar da nake ganin zai kawo mana mas'alha da fahimtar abinda suka aikata babban laifi ne saboda gaba. Nasan zuwa yanzu sun fahimci abin duniya take ciki, hakan yasa na yanke shawarar janye karar ba sai ta kaimu ga zama kotu ba sannan ayi min iyaka da su a rubuce kayi hakuri da furucina amma kamar hakan zai sa su daina neman hallakani ko makamantansu. Nasan zaka ce inda Ni na haife su bazan yi ƙarar su ba duk abinda zasu yi min, amma suma basu ɗauke matsayin mahaifiya ba wace ta haife su da ba zama suyi kokarin aikata abinda suka aikata ba..... amma duk da haka uwa nake wajensu dole na kara hakuri da su sannan kai mahaifinsu ne dole ko su ci darajarka. Na yanke In sha Allah zuwa litinin tun safe zamu station mu taho da su. Dan Allah ka yafeni masoyina sanyin idaniya da zuciya...."Bai bari ta kai karshe ba ya katseta ta hanyar hade bakinsu, dole ta hadiye sauran maganarta sai da ya tabbatar da ta shanye maganar ta hanyar hadiye yawunsa sannan ya sake ta yana jifanta da wani irin murmushi mai haɗe da dariya, ta zumburo baki tana faɗin "Dan kada ka yafe mini yasa kai haka ko?"
"Subhanallahi ai ke kullum cikin nema miki yafiya da yafe miki nake, ko kin yi laifi ko bak'iya ba na yafe miki ya ke annurin zuciyar Khalil" ya fada yana kai hannunsa gefen fuskar ta yana shafa wa. Ta yi likimo tana amsa sakon da yake aika mata "Nayi haka ne kawai dan ki samu ki numfasa, tun da kika fara magana ƙinki ki yi shiru ki saurara bayan mu ya kamata mu nami tafiyarki da y'ara. Amma har kike irin wannan dogon jawabi bayan ke aka wa laifi... Tabbas ba zan miki karya ba, na ji ba dadi lokacin da aka rufe su duk da nasan laifinsu ne sannan mahaifiyarsu ita ce sila saboda ko Ni ita take nuna musu bani da daraja. Amma na ji dadi sosai da na ji wannan zantukan daga baƙin da kullum yake neman tsanyaya min zuciya, kullum sonki karuwa take cikin kalbi da ruhi"
"Tabbas kin goge duk wata damuwa da nake ciki saboda kullum da zaman kotu nake kwana nake tashi, ya rayuwarsu zai kasance a can in an yanke musu hukunci aka kai su kurkuku kamar yanda Inspecteur ya fada zasu iya kai har shekaru huɗu a ciki, kinga ke nan rayuwar su ta tawaye sosai. Kullum ina cikin neman yanda zan yi kar ayi wannan zaman na kotun, Ga shi kuma ina jin kunyar tunkarar ki da maganar dan kar ki fassarani da wata manufa, amma yanzu kam alhamdulillahi tunda da kanki kika janye, muna godiya Allah ya yi miki albarka ya kara ma ki lafiya, ina matukar sonki ma préférée, Allah ya bamu ya'ya na gari" ya shiga sumbatar ta ta ko ina. Sosai ya ji daɗin janyewar da ta yi hakan yasa sai da ya nuna mata tsantsan farin cikinsa a aika ce. Bayan komai ya lafa sunyi wanka suna zaune saman table à manger dabda juna sun sa abinci mai rai da lafiya a gaba Aïda cikin shagwaba da zolaya ta kalle shi ta ce "Ni bazan ci abincin da huce ba shi yasa tun dazu na so mu ci amma daga maka tarba duk ka bi ka takura min har abincin ya fita a raina" saida ya yi dariya mai sauti yana kai lomar abincin bakinsa yace "Yanzu wannan abincin ne ya huce bébé? bayan da zafinsu yanzu kika zuba fa daga cikin cooler. Duk da nasan rigima kike ji ai ke kika hana muci tun dazun" ya kashe mata ido shima yana sokanarta
"Ni dai Allah bazan ci wannan abincin ba in ka gama a siya min wancan abun na rannan" ta fada tana langwabe kai irin ya tuna din nan
"An gama zuciyar Khalil, idan kike ce sai na dawo zan karasa cin abinci ma yanzu zan bari na tafi nemo miki bukarki, saboda duk wata bukatar ki ya shan gaban komai sarauniyar zuciyar Khalil" ya yi mike yana kokarin barin gaban table din cikin sauri ta kamo hannunsa
"A'a Ni ban ce haka ba mon amour ka gama ci sai kaje ka siyo min, nima bukatarka ce a gaban komai daga wajena dan haka koma ka zauna sai ka gama" ta dauki jus zobo dake saman table cikin carafe ta siyaya wa Khalil a cikin verre bayan ya zauna ta kai bakinsa ya kurba ya hau santi har da lumshe ido kafin ita ma ta kurba dai-dai inda yasa bakinsa haƙa dai wannan dare suka kwana cikin so, kauna, kwanciyar hankali da ta zuciya.
*** **** ***
Yayinda wasu suke can cikin kunci damuwa da tashin hankali wanda ya haifar musu da rashin samun wadataccen bacci kamar Halima da take tufka da warwara.
Aïda ta zame mata babban masifu ita ce ta katangeta da masoyinta kuma uban ya'yanta Khalil wanda take jin zata iya komai dan raba Khalil da Aïda ko dan su ji yanda ita ma ta ji idan tace komai to tana nufin komai din.
Sai Safa da marwa take cikin ɗakin da yake dauke da ciki daya da palo sai dan karamin rumfa a bakin dakin da banɗaki daya a waje da kuma kitchen.
Idanunta ya sauka kan y'aranta da suke kwance saman babban Kalifa suna bacci cikin kwanciyar hankali. Tausayi da sonsu ya kara ribanya a cikin zuciyarta, yanzu banda Aïda, da suna can rungume da mahaifinsu, ga su da ƙananun shekaru basu san abin da yake faruwa a rayuwarsu ba amma tabbas rayuwarsa akwai nakasu.
Saboda rashin rayuwa waje guda tare da duka iyaye biyu babban nakasu ne ga ya'ya ma'ana duk yaron da ya taso iyayensa basa tare waje ɗaya. To tabbas ayuwarsa a tauye take, hankalinsa ma daban take da wanda ya taso tare da iyayensa biyu waje guda, komin gata da arziki da zaka samu idan har iyayen ka basa tare to tabbas kai nakasasshe ne.Abinda take gudu wa y'aranta ke nan kuma ga dukan alamu suna nuna kamar sun tabbata. Y'aranta zasu rayu ba tare Ubansu a kusa ba, idan kuma tace zata maida su can wajen uban nan ma zasu rayu ba uwa to amma duk inda za su gidan ubansu shi ne ya fi musu kowane gida a duniyar nan dan haka dole zata maida y'aranta can gidan ubansu saboda shine dole su. Ta daura hannun ta ta shafe dan cikin ta da ya tasa kaɗan alamar tana dauke da ciki na wata hudu zuwa biyar da yake bata da irin girman ciki yasa sai kayi tunanin cikin wata biyu ko uku haka. Har lokacin Tana shafa cikin take faɗin "Kai/ke na fi ji wa tausayi, ace ka/ki zo duniya mahaifinka baya kusa balle yasan damuwar ka, lafiya da rashin sa. Idan nace daga na haife ka zan mika ka ga mahaifinku dan na kuntata masa da amarya sa dole nima zan kuntata. Meye abin yi? dole na maida wannan yaran gidan uban su Aïda ta yi dawainiya da su tunda ita dai ba zata taɓa haifuwa har duniya ta nade in dai gidan Khalil take. Daga ya'yana sai ya'yana ba wata mace da ta isa ta haifa masa bayan ni" ta yi wani irin murmushi wanda ya fi kuka ciwo da daci a zuciya. Ta kara sa ta zauna bakin katifar inda y'aran suke ƙwance ta zauna ta sake daura wani uban tagumi da hannu biyu, can kasan zuciyarta kuwa Allah ne kaɗai matsanin abin da yake wakana saɓar ciwo da zafin da take ji a cikinsa...
Tauye wa Aïda haifuwa shi kadai ne zai sa ita ma ta ji zafin abinda ta yi mata, ita da haifuwa sai dai ta ji labarin sa amma ba dai cikinta ya dauka ba "Sai dai ta raini ya'yan da na haifa ta zama nannynsu" ta furta tun karfi cikin ɓacin rai sai da daya daga cikin yaran ya ɗan motsa alamar zai farka ta yi saurin rike bakin ta tana zare ido. Sai kuma ya juya ya kwanta...Bangaren Khalil kuwa sosai ya ji daɗin daren jiya, washe gari haka ya yi ta ma Aïda hidima bayan sun yi break fast khalil ya kira Lawan yake shaida masa abinda Aïda ta yanke na sakin y'aran bai san cewa harda gudummawar Lawan a cikin haƙan ba.
Aïda har mamakinsa take yanda yake cikin walwala da tarin annashuwa. Sannan ta tausaya masa saboda y'aran basu ɗauke shi bakin komai ba saboda tuni mahaifiyar su ta dasa kiyayyar sa da rashin kimarsa a cikin zukatansu, dalilin da yasa basu ɗauke shi bakin komai ba face dolen sa ya yi musu hidima kamar yadda Halima tasa musu cikin kunne da zuciyar su....©️ AMYCHA✍️✔️
YOU ARE READING
UWARGIDANA
AdventureLabari ne da ya ƙunshi abubuwa masu tarin yawa ƙaddara, soyayya, hakuri, zazzafan kishi....