UWARGIDANA
(...Ɓakin Ƙishi)°📖Page Neuf📖.
"Yanzu tafiya zaka yi ka bar su a nan, cell za'a sa su fa y'arana za su zauna cikin kazanta da wari har na tsawon sati ɗaya amma ba zaka yi komai a kai ba?" Cikin sheshshekar kuka, y'aran kuma maimakon su zo su roki mahaifinsu tare sai su kayi kememe ko motsi daga inda suke zaune.
"Halima me kike son na yi? Ni na sa su?"
"Ka sa a fitar da su a wajen nan, ko ba kai ka sa su ba ai y'aranka ne"
" Ina ce kin ji abin da Inspecteur ya faɗa, ta ya zan fitar da su?"
"To ka sa dole Aïda ta janye ƙarar mana"
"Ke ma kisa dole y'aranki su maida mata jikinta ya dawo yanda yake a baya ba raunika ba komai sai na sa ta janye ƙarar, mara hankali kawai, dama baki shirya wa irin wannan rana ba, a cikin abinda kike koya musu?"
Daga haka ya sa kai ya bar ta tsaye a wajen har ya bacewa ganin ta, sosai maganganunsa suka kone mata rai kullum ita ce take bata tarbiyyar y'ara bayan shi mai tarbiyyan bai taba tsaya wa ya maida hankali ya ba su ba amma yake kushe tarbiyyarta, maganar Inspecteur ya dawo da ita daga tunanin wucen gadi da ta shiga
"Officer ku wuce da su cell, yarinyar a kai ta wajen mata, ba sai kun wahalar da su ba saboda tuni sun amsa laifin su, takarda zamu haɗa musu na zuwa kotu nan da sati ɗaya In sha Allah"
Bata san lokacin da ta kwasa a guje ta fita waje dan ta roki Aïda ba, sai dai kash fitar ta ya yi daidai da fitan motarsu Khalil da Lawan daga haraban office din.
Nan ta tsaya tana kallo har suka ɓace wa ganin ta, haka ta ja kafadunta ta fita bakin titin ta tari napep ta hau saboda ko ta goma office tuni an wuce da y'aran cell banda damuwa ba abinda zuciyarta take ciki, tana zaune ita ɗaya a baya duk abin duniya ya taru ya yi mata yawa, ita ba ta taɓa kawo wa a kai za'a iya zuwa har nan ba.
Ta tsani Aïda kiyayyar da take mata ya kara ribanya fiye da baya tun da aka auro Aïda yanzu wata shida kacal amma kamar wanda suka yi shekaru ba ta taɓa samun sukunin zuciya ba har kawo yanzu ita da ya'yanta.Ba ta taɓa sammanin Aïda zata zame mata ciwon ido ba...ko da yake Wanda ta iya aure Khalil har ta iya shigo gidan tun a Ranar da Khalil yace an aura aurensa da 'Yar wance ta san Aïda a tsaye suke. Saboda Aïda ita ce ta bakwai, kafin ita Khalil ya yi yunkurin kara aure, 'yammata daya ɗaya har shida duk sai ta yi yanda ta yi ta bata maganar auren da taimakon malamin tsubbunta wanda ya shaida mata ba wanda ya isa ya aure mata miji. Khalil zai yi ta Neman aure amma ba zai taɓa aurensu ba har ya gaji ya hakura. Lokacin da ya zo mata da maganar aurensa da Aïda ta sake koma wajen malamin wanda ya kara shaida mata kar ta tada hankalin ta auren ba zai yiwuwa ba, wannan ma kamar sauran za'a shashantar da maganar har su rabu amma sai ta ga sabanin haka inda magana ta sha banban da sauran lokuta. Ba ta hakura ba kullum cikin bibiyar bokaye da Malaman tsubbu take amma abu kamar ba'a yi kullum Aïda ce da nasara a kanta.
"Hajiya wani layi zamu shiga"
"Na'am?" ta tambaya bayan ta yi firgigit ta dawo da ga tunanin da ta lula lokacin da
Ta ji mai napep yana tambayar ta, cikin gyara zaman mayafinta ta nuna masa layin da hannu, ya kaita har bakin kofar gidan ta sauka ta shiga ciki bayan ta biya kuɗin sa...Abin duniya duk ya isheta ta rasa inda zata fara kamawa, Da farko ta fara da yanda zata yi a saki y'aranta kafin ta sa a Turawa Aïda wata cuta wanda zai zama ajalinta ko kuma na biyu Ta fara sa a tura mata cutar sannan a kashe mata zuciya ta yanda zata amince ta janye karar a saki y'aranta cikin sauki..
"Mama yunwa" A guje ya fada saman ta, shigowarsu kenan cikin gidan tare da kannansa bayan sun ji dawowar Mamansu tun da dama suna makwabta ne
"Ba na aje muku abinci ba, me ya hana ku ci kai da kannanka?"
"Lokacin ba mu jin yinwa ne" sauran kannansa ma duka suka bi bayansa suka fada saman mahaifiyarsu suna maida numfashin wahala da gajiya da yawo a unguwa
"Ai sai ku dauko ku ci yanzu da kuka fara jinta" tana sauke su daga saman jikinta kafin ta mike,
Ta ɗauki buta ta shiga bayi bayan ta fito ta daura arwallah dan tun lokacin da ta shigo gida ta ji an shiga masallatai sun fara sallah amma a lokacin ba ta san abinda ya hana ta yin arwallah da sallah a kan lokaci ba sai yanzu da lokaci ya fita.
YOU ARE READING
UWARGIDANA
AdventureLabari ne da ya ƙunshi abubuwa masu tarin yawa ƙaddara, soyayya, hakuri, zazzafan kishi....