ZA'BIN RAI NAH Page 1

19 1 1
                                    

💝 ZA'BIN RAI NA 💝

Written and Story by ✍️

💕Maijidda Bashir Sharu

❤ ( MRS JEEDDERTY ) 💋

09138426858
WhatsApp number or call

*📚🖊️NAZARI WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*

_Kyawawan Nazari kafin rubutu na ɗamfare da bin ƙa'idojin rubutu._

_Cikakken Nazari kafin rubutu kan ƙayata duniyar Adabin hausa._


*** GARGADI !!! ***

Ban yarda wani koh wata su sauyamun labari na dan wannan littafin mallar marubuciya ce, please dan haka a kiyaye ✔✔✔

🌺Tsokaci :🌸 Wannan littafin kagyaggen labarine baayishi domin cin zarafin wani ko wataba in anci koro da abunda yayi dai dai da rayuwarka/ki alkalamine ✍️ yazo da salonsa ✍️✍️✍️, idan kuma kunci karo da wani kuskure a ciki kumun afuwa kasancewar wannan shine littafina na farko baza'a rasa samun gibi a ciki domun dan adan ajizi ne.

Labarin zaiyi nutso ne cikin wata rayuwa mai ban Al'jabi, Tausayi, Zalunci cin Amana, Bijirewa iyaye, dük na kunshe cikin tafiyar
Mrs Jeedderty acikin wannan labarin ✍️mai taken * ZABIN RAINA * ✍️.

Ya Allah ka lamuncemin na rubuta ✍️abunda zai amfani dubban al'ummar musulmi Amen 🙏 ya Hayyu ya Qayyum 🤲🤲🤲

* Sadaukarwa *

*Littafin baki dayansa sadaukarwace ga aminaina masu dubun karamci a gareni sune :

Halima Sa'id (walidan aunty),

* Oum Maryam √

* Aisha Jilani √

* Šâádátü bello √

* Hussaina Auwal √

* Aisha Hussain √

* Sadiya Muhd √

* Aisha Musa √

Allahu ya ja wannan zumuntar har zuwa gidan Al'janar Firddausi muzama makwaftan juna dan alfarmar Shugaban Halitta Manzon Allah S.A.W. Amen 🙏 ya hayyu ya qayyum 🤲🏿🤲🏿

🌹🌹🌹Da sunan Allah mai rahma mai jin kai, allah ka karo salatika Mara adadi gurun shugabammu Muhammadur Rasulullahi S.A.W. Amen 🙏 🌺🌺🌺🌺

Page 1

Hadarine ya karad'e garin baki daya sosae dan wanda koh yaushe ruwa zai iya zugewa. Wata yarinya nagani da bazata huce shekara goma 14 ba sanye take da wani hijab navy blue amma saboda tsufan da yayi bazaka taba gane kalar saba zaka dauka blue black ne .Fuskarta dauke take da liqab kafarta dauke da wani takalmi dan madina shima dae duk yasha jiki amma ko ina nata tsaf tsaff yake sauri sauri take takarasa gida kafin ruwan ya sauka a jikin ta . Gudu gudu takeyi duk dan kada ruwannan ya sameta tayi tafiya mai nisa sosai daga bisani ta karaso wani dan karamin gida maidaici sae dai marabarsa da kango kadanne shiga gidan tayi bakinta dauke da sallama batakae da karasawa muryar wata mata najiyo tana fad'in '' sannu asararriya kindawo kenan ? ''.

Yarinyarnan naji ta fara magana '' aa hajjo bahakabane can gidan ne to yau tayi baki shine naketa tayata aikace aikace ''.

'' To to fasiliya uwar yan tsara zance kamar tsinanniyar uwarki matacciya '' .

'' Kiyi hakuri '' Hajjo murna yarinyar takarafada da rawar murya hawaye na mata zuba idan da sabo da ta saba da cin mutunci da akemata da zagin uwarta da aketatayi

Muryar watace yarinyace ta dawo da ita hayyacinta daga tunanin datafada '' hajjo nadawo ''.

'' Oyoyo oyoyo ! farra (nau'in haske) sannunki da zuwa Farrahn hajjo ya makarantar sannu muje ciki kinga har amfara yayyafi ko zoki ci abinci kiyi wanka ki huta ''.

'' Ke Sahab ( gajimare mai bada ruwa) dauki bokitinnan kije can tuka_tukan Malam Ahmadu ki diba mana ruwa ki cikamana ko'ina ''.

'' To amma hajjo naga magarib tayi kuma ga ruwa ko mubari mutari na sama ko ? ".

'' Eh lallai '' hajjo ta fad'a '' wato me iskancinnaki yakai nan kenan to karkije ki bari uban da yahaifeki yazo shi sai ya debo maki kinjii yar iska kawae '' .

'' Kiyi hakuri bara na je na debo ''' ta fad'a a kasalance

'' kedae kikasani '' cewar hajjo tashiga wani kitchen da akayishi da langa_langa ta dauko wani bokiti na roba irin na panting dinnan tazo zata huce ta gabansu.

'' Sahab '' muryar Farra ce ta sata tsayawa ta juyo '' naam farra ya akai ? ".

'' Dama dama idan kindawo ga kayana ki wankemin '', cewar Farrah ido tazubawa Farra zatayi magana Hajjo tayi carabe tace '' yo auta har sae kinfadamata ki cillamata kice tawankemiki kayanki kawae yo menene amfaninta ah gidan ? ".

Tsawa akayi mai karfi had'e da ruwa kamar da bakin kwarya amma duk da haka Hajjo ta sata ta futa dibo ruwannan jikinta yajike duka sae karkarwa takeyi tana kammalawa bata shiga dakiba saeda tayiwa Farra wanki uniform dinta sannan tayi alwalar sallah tanufin wani dan daki tashiga tacire wannan hijab din atamface ajikinta doguwar riga itama tajike ta cireta ta dauko bakkon ta dauki riga da zani na atamfa tasaka ta dauki wani hijab din tasaka ta tada Sallah Maghrib tana idarwa ta zauna tanata lazumi har akae kira Isha'l ta kabbara Sallah itama tana idarwa ta tashi ta shiga kitchen ta dauki wata bakar leda da tunda tashigo nakagu naga menene acikinta tadauka tanufi dakin hajjo tashiga da sallama.

Farra tagani kusa da Hajjo suna zaune abincine agaban Farra din wanda ita ta zata tambaya bazaa taba bata shiba saboda duk gidan babu mai kaunarta harda kuwa haifinta Hajjo ce ta katsemata tunani da cewa '' yau ni Hajjo nashiga uku da wannan mayyar ''.

'' kiyi hakuri Hajjo gashi acan akabani yooo ai haka zaki kice yar albarka. 😳 To ke kinci ince ai ko ? ''.

''A'a hajjo kenafara kawowa kigani ''.

'' To kije kitchen akwae dumaman tuwon jiya kidiba mu sae muci wannan ungo Farra dibi kici. Kika tsayamin kemadage ko baki hucewane ? ''.

'' A'a Hajjo sae da safe '', mtsewww abunda Farra ta ja taski. Yayinda ita kuma tajuya tanufi kitchen din tadibi tuwon da ko dumi babu tadawo dakinta ta zauna tacı dan rabonta da abinci tun safe haka taci ta kammala tasha ruwa ta nemi makwanci ta kwanta ..........

Shin wacece Sahab ?, Menene alakarta da Hajjo ?, Wacece farra suwaye, iyayenta ?, Wanene ubanda Hajjo take magana akae shin uwar tata matacciyace meyasa basa sonta meyasa suka tsaneta meyasa bata farin ciki ?.
Kada kumanta da Mrs Jeedeerty acikin wannan littafin ✍️mai taken * ZABIN RAE NAH *✍️📕🖊️

PLEASE LIKE AND COMMENT fisabilillah !!!! 🙏🙏🙏 KUYI FOLLOWING 'DINA

Habibiyar NAZARI WRITERS ✍️📕🖊️

ZA'BIN RAI NAH  Part 1Where stories live. Discover now