chapter two

820 60 3
                                    

ASALINA

Na

Ummu na'im

Follow me on wattpad @ummunaim

*page 2*

A hankali suke tafiya tana rik'e da hannun Hajiya har suka fito part din hajiyar wata kofa naga sun nufa wacce ta fi kowace kofa kyau da girma a duk cikin kofofin gidan da suke cikin babban falon Wanda zai saadaaka da part din mommy,umma da kuma Hajiya ,a hankali ta bude kofar bakinsu dauke da sallama a lokaci guda suka shiga cikin falon ,gabadaya family suna ciki kamar yanda suka saba a duk lokacin weekends lkcn daddy yana gari kenan sincea abuja yake aiki a NNPC don shine mataimakin shugaban wurin gabadaya,prof Abbas Saleh mutum ne mai son yin adalci a duk inda ya samu kansa ,hakan tasa har cikin gidansa ma ya tabbatar da kowa yana samun irin kulawar da ya kamata ,bai bada wata kafa da za'a samu wata b'araka a cikin familynsa ba ,mutum ne tsayayye mai kokarin yin komai yadda ya kamata ,shiyasa ko cikin matansa Hajiya hadiza(mummy), da Hajiya Maryam( umma) ba za kaji wani mummunan Abu ba ,lafiya kalau suke zaune ,sauran yaran gidanma a haka suka taso ,tarbiyar da akai musu kenan girmama juna ,zamanlafiya a koyaushe ,har masu aikin gidanma gaba dayansu sunajin dadin zaman gidan,to hakance ta sanya prof Abbas ya ware lkc na musamman da yake zama da iyalinsa that's every Saturdays and Sundays bayan sallar isha' ,ta hakane yake gane matsalolinsu,buk'atunsu ya kuma ji ra'ayoyinsu akan wani al'amari idan ya taso Wanda kuma ya kamata su sanya ra'ayinsu a ciki,yana ganin shigowar mahaifiyarsa cikin falon yayi saurin sauka daga saman kujerar da yake zaune ya koma saman carpet ,a gaskiya yana matukar girmama mahaifiyarsa ,shiyasa kullum cikin yi masa addu'o'i take da sanya masa albarka hakan ne kuma yasa yake k'ara samun daukaka da nasarori masu yawa a rayuwarsa,har kujeran dake kusa dashi ta k'arasa ta zauna cike da girmamawa da ladabi ya gaidata ,sannan matansa da sauran yaransu suma sukai nasu gaisuwar,Noor itama ta gaida iyayenta sannan ,da ganan kuma sai hiransu suka cigaba dayi kamn yanda suka saba ,masu kai buk'tunsu na kudi suna yi ,musamman mummy ,don ita akwai son kashe kudi ,itama afra haka take don za'a iya cewa ma tafi mamanta son kashe kudi dama ance magaji mafiyi ,nan ta shirya nata karyar itama ta fada don tasan daddy is not the type that gives out money unnecessarily ,

Kusan minti 20 aka dauka babu Ya umar a wurin ,Hajiya ce ta fara lura da hakan ," yo waini ina ummaru ya shiga ne ? Duk ga y'an uwansa anan shi yana can d'aki ko baya gidan ne?" Ta k'arasa maganar tana duban Daddy, " ehy to d'azu dai da muka iddar da sallan magriba ya fada mun zai tafi cikin gari,wata kila har yanxu bai dawo ba "" ko kuma yana can daki yana karance karancen nasa na fama ba " cewar Hajiya " shi tunda ya fara karatun likita shikenan ya auri takardu ko gajiya ma ba yayi...je ki dubo...." Ba ta karasa maganarta ba nabeela tai saurin mik'ewa tana "Hajiya bara na dubo ko yana d'akinsa ne ,ta juya cikin dan sauri zata fita dama can zaman da sukeyi a wurin hankalinta na wurinsa tana ta sauraron shigowarsa,saurin da takeyi yasa ta manta da karamin stool din da ke ajiye a side din kujerar karshe nafalon aiko da karfi da buge a k'afarta da stool din ,a lokaci guda suka juya suna mata sannu ,ita kam bata damu ba da zafin da k'afarta keyi burinta kawai taje taga ya umar ,ci gaba tai da tafiya ,har takai bakin k'ofa tajiyo muryan daddy" dawo nabeela kiyi zamanki ki huta sannu ko,noor tashi ki dubo yayanku a dakinsa ," tom daddy" a natse ta mik'e ta fita wani irin tuk'uk'i ne ya taso ma Nabila don ita ba haka taso ba ,duk da noor tana matsayin knwar Yaya umar saida ta bata haushi don ita batak'i bama ya daina ma kowace mace magana ba ko ya alak'arsu take kuwa (Nabila yarinyar mummy ce da ita tazo gidan sbd tana gudun barinta wurin dangin mahaifinta bayan rasuwar mahaifin Nabila ,shikuma daddy ya yadda zai rike ta kamar y'arsa,shiyasa ma babu Wanda zai gane ba y'ar gidan bace,Ita kanta bacin daddy yai insisting akan a rinka kaita danginta tun tana karama to da bazata fahimci cewa ba nanne gidansu ba don tun tana y'ar shekara 2 daddy ya auro mahaifiyarta)

Ta wani dogon hanya naga tabi tacikin falon ta baya sai gata a wurin wani kofa still dai budewa tai ta fita sai gata a wani madaidaicin haraba da kuma wani building din just like an apartment ,da alama nanne BQ din gidan ,knocking ta karayi a karo na biyu bakinta dauke da sallama ,kwance yake idonsa lumshe kamar mai bacci though b bacci yake ba ,jin muryarta yasa ya mik'e zaune,yanason amsawa amma saboda yanda yakejin Kansas ya masa nauyi yasa ya mik'e ya nufi kofar ,yana tafe yana lumshe ido ,bai tunanin zata shigo ba tunda bai bata izini ba ,don a yanda ya Santa bats taba shiga dakin mutum ba tare da izini ba kamar yanda itama batai zaton ya taho ba donjin da tayi shirun yayi yawa ,yana bude kofar kokarin murd'a handle din,unknowingly ya bugeta a fuska ,Dan k'ara ta saki siriri kaman yanda voice dinta yake ,cikin hanzari ya karasa bude kofan "ya salam! I'm sorry na buge ki bansan kina kusa ba sosai ya fadi yana rik'o hannunta " Dan murmushi tai ,"its OK fa babu komai ,nasan bakasan nai kusa da door in ba" shima murmushin kawai yayi lokacin daya daina jin sautin muryarta don tuni d'an maganar da tayi ta fara narkar masa da zuciya,"golden voice "ya fadi cikin ransa with a little soundless sigh,uhm? " am dama daddy ne yace na duba ko kana d'aki cos baka zo falo ba" sai a sannan ya tuna ya kamata ace yana falo ne yanxu " oh!wallah na mantà ! Yai exclaiming ," OK muje" juyawa tai ta fara tafiya batare da tai magna ba,yanda take tafiya a hankali shima haka ya maida tafiyarsa can kasar zuciyarsa yana mamakin yanda nutsuwanta yake nunawa a kome ta keyi ire irenta gaskiya is extremely hard to come by these days ,yawancin mata suna kokarin maida Kansu kamar ba mata ba sbd hijabin nutsuwa,da kamun kai da suka yaye ma fuskarsu,ya tafi can wata duniyar sallamar da tai ne ya dawo dashikusan a tare suka shiga falon ,tunda ya shiga nabeela ta kafe shi da kananun idanunta ,shi baimasan tana yi ba ,after some minutes da shigansu suka tashi zuwa dining dake falon don yin dinner,noor da aysha sukai serving kowa, sanan suma suka zauna,fruits salad kawai tasha ,sai wurin 9:30 sannan kowa ya nufa nasa bangaren ,yana lura da yadda take Shafa gefen fuskarta from time to time ,alamun wurin da ya bigeta yana mata zaafi amma hakan bai nuna ba a fuskarta,don fuskarta be cika fallasa sirrin dake zuciyarta ba shi yasa ko da ranta ne ya baci ko wani abun baimata dadi ba baa ganewa don she really knows how to control herself in all situations, baiji dad'in hakan ba har cikin ransa ,

Kayan karatunta ta dakko ta fito daga dakinta don zuwa na Hajiya tai karatu ,just 10mins after taji sallamarsa amsa masa tayi sannan ya shiga,karasawa yayi har kusa da inda take zaune ya Ciro mn zafin da yake amfani dashi ya bata"gashi ki Shafa a fuskarki idan zaki kwanta ,in sha Allah it will stop paining OK?""alright Yaya nagode"ta fadi tana Karba not feeling comfortable because of the kind of nighty she was wearing dukda long sleeping dress ne but a wurin ta ganin rashin dacewan hakan ta ke sbd yanda ya lafe mata a jiki sannan mai guntun hannu ne,shima bai bata lkc ba ya fita ya koma NASA dakin

Monday 2:30 pm
Bacci take sosai me cike da natsuwa da kwanciyar hankali tunda suka fara exams bata samu natsuwa nayin enough sleep ba sai yau da ta gama ,ya fito daga dakin hajiya har zai wuce kaman ya tuna wani Abu ya koma yai sallama a bakin kofar dakinta baa amsa ba ,Dan tura kofan yai kadan ya leka ,kwance ya hangota a middle din bed tana bacci ,samun kansa yayi da tura kofar gabadaya ya shige ciki ,kallonta ya tsaya yi yana inspecting fuskarta ,her face was glowing, sann Zara zaran eyelashes dinta sun kwanta luf luf dasu sunyi kyau,scarf din kanta ya fita lallausan kanta da bbu kitso,ba karamin kyau baccin ya kara mata ba ,juya wa tayi tana Dan mika Kad'an ,ji yayi zuciyarsaa tadanyi tsalle as if zata Faso ribcage dinsa cikin Sauri ya juya yana kwabon kansa,
A falo ya tsaya ya fidda
ajiyar zuciya a fili "what has came over me ne wai?" Ya fadi a kasan throat dinsa"don't forget she's your sis dai "yai scolding Kansa yana nupan part dinsa at the same time.

Do comment please
Don't forget to vote and
Share share share
Bye bye

ASALINADonde viven las historias. Descúbrelo ahora