chapter five

678 27 0
                                    

ASALINA

Na
Ummu na'im

Follow me on wattpad @ummunaim

*page* 5

Few minutes ya kaishi harabar gidan zuciyarsa na cigaba da azalzalarsa Kai tsaye wurinsu ya tunkara wani sashe na zuciyarsa na kissifa masa yaje ya hanasu fita ,ta can wani bangaren kuma dayan ya dauka a wannan lokacin ,why should I even think of stopping them in the first place ? and why the sudden restlessness and uneasiness? Yai directing tambayarsa ga zuciyarsa ,shiru yai Jim kamar yana jiran amsarta.,knowing that bazai samu wani amsaba a lokacin kuma baida tangible reason na hanasu yasa ya yanke shawarar fasawa..turning yayi ya nupi wurin da yai parking car dinsa ya bude ciki ya wurga kansa not paying any attention to alamar fitan motarsu daga harabar gidan ,baisan me zaiyi ba ba tare da wani tunani ba ya kunna motarsa yabi bayansu cikin saurinsa,haka yai ta binsu a baya ,shi bai ma san yanayi ba ,zuciyarsa ce kawai take sanyasa yin hakan ,kuma sai ya ke yi ba tare da wani shakka ba cos he already knows his nature of being over protective akan duk abunda yaji ya naso ,kokarin shi kullum yaga ya ba wannan abun cikakken kulawa,unlike idan bai damu da abu ba Sam bai bi ta kan wannan abun

Cikin dak'ik'u 30 suka iso gidan san turaki wato family house din su hajjo kenan daga gefe ya samu wuri yai parking motarsa yana jirin fitowarsu har saida suka shiga cikin gidan sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tada motarsa ya bar wurin

A haka ya nupi masjid don sallatar juma'a prayer, ya dade sosai cikin masallacin bayan idar da sallah yana addu'o,'in sa sai
Around 2pm sannan ya kama hanyar zuwa gida ,kad'an kad'an tunaninta ke k'ara taso masa duk da kokarin danne zuciyarsa da ya keyi ,koda ya is a gida kai tsaye bangaren sa ya nupa ta baya ba tare da ya shiga ta falon ba ,yana shiga d'aki ya rage kayan jikinsa ya fad'a bayi yai wanka ,da yake garin yau ana fama da rana sosai kamar ba damina ba kamar dai yanda ya ke kasancewa a mafi yawancin ranakun juma'a ,hakan tasa yana fitowa daga bandaki ya shirya cikin wata pure white armless shirt da bakin wando 3 quarter ,k'ure air condition din dakin yayi ya haye gadonsa ya kwanta ,tunaninta ya shiga yi duk wasu hotunan face din ta, beautiful smile din ta da cute dimples din ta suna masa yawo a kwakwalwa ,murmushi kawai yake shi kadai lokaci guda yana jin dadi da nishadi game da sabon yanayin da ya samu kansa a ciki, baida kokwanto ko kad'an na cewa yana k'aunar noor,don zuciyarsa ta gama gasgata hakan even though shi ba ma'abicin soyayya bane but yasan all these special and strange feelings are nothing other than an exquisite love ,a haka wani irin bacci mai dad'i ya kwashe shi ,yayi bacci sosai mai cike da mafarki masu yawa mostly about noor, mafarkin da yayi na k'arshe ne ya sanyashi Saurin farkawa bakinsa dauke da addu'a ,kansa ya cira ya duba agogon da ke manne da wall din dakin cikin sauri ya mike ganin har karfe biyar da kusan rabi ,lokacin sallar asr ya kwace masa sosai guntun tsoki yaja ya shige bathroom ,alwala ya dauro yazo yai sallah ,yana zaune still a inda yai sallar ya jiyo tsuwwar phone dinsa ,cikin kasala ya mik'e ya nupi Inda ya ajiye wayar saman bed side drawer ya d'aga ganin sunan NOOR da yayi daradara na yawo a saman screen din wayar yasa heart dinsa skipping a little, cikin dakiya ya daga ya kara a left side ear dinsa ,duk maganar da takeyi bai tsaya maida hankali wurin hada ma'anoninsu ba melodious voice din ta kawai yake sauraro yana lumshe da idonsa sai da yaji tai shiru sannan ya fara tunaninta shin ko me ta fad'a masa ne ? Ta bangaren noor kuwa jin shirun yayi yawa yasa tace: "Yaya pleaseee....kaga hadari ya had'u sosai and I've called the driver yace mummy ce ta aikesa kasuwa kuma babu yanda zaiyi dole ya fasa zuwa daukanmu ya tafi sakonta" heavy sigh yayi a k'asan throat dinsa sai lokacin ya fahimta inda maganarta ta dosa yace:'alright gani nan zuwa yanxu"ya ajiye wayar yana maida numfashi ,get back to your senses man ,haba can't you control yourself 4 once?" Yaji mind dinsa na kwabansa, mikewa yayi cikin karfinsa ya shiga bathroom ya sakar ma kansa shower minti 10 kacal yayi ya fito daga band'akin ,shiryawa yayi cikin wani farin lallausan yadi mai taushin gaske ,ya sanya hularsa kalar ash takalminsa ma haka ,silver agogo ya Daura a hannunsa ya spraying hadaddun perfumes dinsa masu kamshin gaske ya zira car keys dinsa ya tafi maido dasu noor gida ,ta bangaren noor kam tana ta kokarin kara calling dinsa tai masa kwatancen gidan amma kirar taki tafiya,duk ta fara gajiya ,ga garin ya k'ara yin bak'ink'irin da hadari ,rugugi kawai ke tashidaga sama, ko wani lokaci ruwa na iya sauka

ASALINAWhere stories live. Discover now