chapter seven

591 40 1
                                    

ASALINA

Na ummu na'im

Follow and vote for me on wattpad@ummunaim

*page*7

Duk wani abu da ya kamata yayi da ya shafi hospital dinsa ya kammala duk ya k'osa ya koma ya ganta yai missing dinta sosai,she's always in his mind and every slightest opportunity da zai samu tunaninta yake yi,yanxu ma da ya koma masaukinsa abunda ya zauna yi kenan bai ko damu da rashin cin abinci da baiyi ba tunda yayi wanka ya rage kayan jikinsa ya koma saman Kujera yai zamansa had'e da lumshe idanuwansa yana hangota cikin idanunsa ,a haka ya dauki lokaci mai tsayi yana aikin abu guda ,idan ya tuna wani abun game da ita yai murmushi wani ya sashi dariya ,saida ya duba agogo ya fahimci ya kwashi lokaci mai tsayi a haka ,cike da kasala ya mik'e zuwa band'aki saida yai wanka sannan ya dauro alwala yafito ,kayansa gaba1 ya dauka zuwa mota don ya tsara yana idar da sallar zuhr zai dauki hanya in sha Allah

Misalin k'arfe 4:30 na yamma ya isa gida cike da kasala da gajiya ,ko kayansa bai tsaya dauka ba ya nufi cikin gidan,kaitsaye ya nupi d'akin Hajiya ,nabeela dake sakkowa daga sama taga lokacin da ya shigo nan take taji zuciyarta na rawa wani irin Abu na taso mata ,dakatawa tayi har saida ya wuce sannan ta sauko da d'an saurinta ta nupi d'akinsu din bata so ya ganta cikin shigar da tayi ,wata doguwar rigace jikinta na wani silk material datasha squeezing saboda baccin da tayi a saman mummynta

Yana shiga dakin sautin dariyarta ya doki kunnensa tsaya yayi cak yana kallon side view din fuskarta da yake tana kwance ne ,ba k'aramin kyau tai masa ba , sannan yanda take dariya fuskanta na glowing snn both side dimples dinta na shigewa yasa shi shiga wani yanayi mai wiyar fassara nan take ,jin kamshin turarensa ya sa ta d'an juyo still dariyar take wow! Even her laugh is different and unique " ya fada a zuciyarsa yana sauke ajiyar zuciya a sanyaye tabbatarwa da tayi shine ya shigo dakin ya sanyata dagowa daga jikin Hajiya datake kwance still dai dariyar ya kasa escaping bakinta ,dariya take sosai amma cikin natsuwa sannan mai matukar birgewa ,ai Yaya umar a wurin ya kusa zama soko din he totally couldn't control himself ,kallonta yake directly ba tare da wani tunani ba ,all he was feeling at that moment was coolness and easiness in his mind, this is how he wants her to be ,he really wants to see her happy,dariyar noor ne ya fara tsagaitawa saboda irin kallon da taga Yaya umar yana mata fuskarsa dauke da k'ayataccen murmushi ,sadda kanta tayi k'asa a hankali ta furta" Yaya barka da dawowa" k'irjinta na d'an bugawa saboda sudden tunanin da take kokarin manta wa ya dawo mata sabo,cikin dakiya da basarwa ya amsa mata din bayaso ta fahimci komai daya shafi kaunar da yake mata cos he don't know how she'll react,yafiso yabi komai a sannu yanda ya kamata ,ita kam Hajiya yi tai kamar ma bata ga komai ba ,shima cikin son basarwa ya k'arasa shigo d'akin " naga alama yau hajiyar tamu ta koma fagen barkwanci ,nima bara na zauna naji me nene abun dariyar ? Ya fadi yana kallon noor, murmushi kawai tayi hajiya tace:"um kyaleta kaaji ,ni banga mene abun dariya cikin magana ta ba ,Yaya hanyar,an dawo lfy ?" Ta kauda maganar yace: "lfy qalau alhamdulillah ,komai yayi kyau" tace: "to masha Allah, Allah ya tabbatar da alkhyri" "amin" yace yana shaida mata komai ya kammala ,nan ta sanya albarka ciki, minti goma ya kara a wurin kafin ya mik'e da nupin ya wuce dakinsa Hajiya tace:" ka zauna noor ta kawo maka abinci mana",yana mik'ewa yace :"no Hajiya na gaji sosai ina buk'atar hutawa ,idan na fito anjima naci abincin",koda ya fito wucewa yayi abinsa baiko lura da nabeela da aka caba ado ba har yaso yai yawa ,tunda mistakenly ya kalli inda take sau d'aya ya d'auke kansa shima don tana zaune ne a inda dole duk Wanda ya fito daga d'akin Hajiya ya lura da ita ,har ya kusa fita falon tai kokarin tattaro k'arfinta ta gaida shi don ba k'aramin kwarjini yai mata ba ,ba yabo ba fallasa ya amsa mata ,dama shi din bai iya wulakanta d'an Adam,duk da yana da izza amma Sam bashi da wulak'anci ...wani nannauyar ajiyan zuciya ta sauke tace :"na shiga uku!!" Anya kam zan iya? Ta tambayi kanta, Jim tayi a wurin kafin ta mike ta nupi dakinsu ,number zee zuru tai dialling don ta fada mata halin da take ciki ,saida ya kusa yankewa sannan ta d'aga cikin hargitsattsiyar murya tace " zan kiraki anjima nabeela ,I'm busy right now" kit ! tai disconnecting kiran ,nabeela bin wayan tayi da kallo ranta na k'ara baci,kusan 15 minutes ta dauka a haka har bataji lokacin da afra ta shigo d'akin ba ,
"Mummy tace na kiraki ,kije ki sameta a d'akinta" ta fada mata tana zama saman gadonta ,chat take da wayarta hakan yasa bata kula da rashin amsa ta da nabeela tayi ba,lura da yanayinta da tayi yasa ta kirata ,juyowa tayi tana fuskantar ta,observing yanayin fuskarta tayi sannan tace" anty nabeela me ke damunki ne haka ,you look disturbed " ajiyar zuciya tayi ta koma kusa da Afra ta zauna tana fuskantarta tace: "afra kinsan wani Abu?"ta tambayeta not expecting an answer itama girgiza kanta tayi alamar a'a
Nabeela ta cigaba da cewa :afra ina cikin damuwa,ina cikin matsala,I'm completely
confused bansan ya zanyi ba ,inason Yaya umar sosai ,inason aurensa amma bansan ya zanyi yasoni ba ,na rasa yadda zanyi ko kallon arziki bai mun balantana na sa ran zai soni ,na rasa yanda zanyi afra"ta k'arasa maganar cikin raunanniyar murya

ASALINADonde viven las historias. Descúbrelo ahora