chapter Ten

1.2K 80 19
                                    

ASALINA

Na

Ummu na'im

Follow and vote for me on wattpad@ummunaim

*page* 10

Daga kai tayi a hankali ta kalleshi shi din ma ita yake kallo dake wa tayi ta taka a hankali cikin nutsuwa zuwa inda yake tsaye not letting her heart's weakness to control her anymore daga d'an nesa dashi ta tsaya tana kallonsa though not directly kamar yanda shi yake mata" Yaya barka da dare"ta gaidashi a hankali ,bai amsa mata ba instead ya cigaba da kallon fuskarta yana inspecting yanayinta sannan cikin muryar datake dauke da tsantsan kulawa yace : me ke damunki?" Ya tambayeta ,kallon fuskarsa tayi na 2 seconds ta d'auke kanta gefe tace:"babu abunda ke damu na Yaya" still yana kallon fuskarta yace:" yaushe kika fara k'arya bansani ba noor" kara dakewa tayi da murmushinta mai masifar kyau tace:" da gaske Yaya I'm not lying...I'm fine! Ta karashe maganar tana juya idanunta kad'an fuskarta dauke da faffadan murmushin da ya bayyana fararen hakoranta " ba k'aramin birgeshi tayi ba hakan yasa ya kafeta da ido yana cigaba da biye ma zuciyarsa shima tasa fuskar tana d'auke da ni'imtaccen murmushi dukda bai gama yarda da cewa babu abunda ke damunta ba amma yanda yake kallonta yasanya shi farinciki ,ji yake kamar su dawwama a haka steps biyu ya kara sai gashi a gabanta ,itako ganin hakan yasa gabanta d'an fad'i kad'an saurin sadda kanta tayi k'asa tana wasa da Zara zaran yatsunta ,cikin wani irin murya mai taushi yace:OK then since kince nothing is wrong ,let me find out my self " ya fad'i yana sanya thumb finger dinsa kan jaw dinta a hankali ya d'ago da fuskarta wani irin yarr! Taji a jikinta saboda batayi tunanin zai yi hakan ba dukda hakan bata bari ya nuna a fuskarta ba shi kam tunda ya d'ago da face dinta ya sanya idanunsa cikin nata yana ganin abubuwa da yawa cikinsu ,duk da yaga sign of depression cikinsu but still jinsa yake kamar ya dawwama a yanayin da yake ,itama tun tana d'aurewa har taji wani irin weakness na sauka a jikinta hakan yasa tai raurau da idanunta don tunanin datake kauce ma shine yasamu nasarar dawowa cikin zuciyarta,idanunta na cikin nasa zuciyarta cike da mamakinsa saida yai two minutes yana kallonta sannan ya janye idanunsa cikin yanayin da shima ya samu Kansa na kasala yace:"now tell me what's wrong don I 've seen everything inside your eyes "ya fad'i a hankali kaman baya son yin magana ,marairaicewa tayi cikin sassanyar muryarta tace:" Yaya da gaske fa babu komai ,kaina ne kawai ke mun ciwo kuma yayi sauki yanxu" fuskarta ya tsura ma ido na 5 seconds sannan yace:" so why do you keep saying babu abunda ke damunki bayan kanki na ciwo,uhum? " shiru tai masa daga k'arshe dai yace taje ta kwanta ta huta idan ta farka kan bai bar ciwo ba still sai ya duba ta,nodding kawai tai masa ta juya abunta ta tafi d'aki ,shima saida yaga shigewarta sannan ya juya ya shiga d'akin umma yana addu'ar mallakarta a matsayin mata a k'asar zuciyarsa

Saida ta kammala duk shirin bacci kamar yanda ta saba sannan ta kwanta still duk wani abunda ya faru bai bar brain dinta ba ,tana kwance yanxu for almost an hour amma babu alamun bacci a idonta ,wayarta dake vibrating saman bedside drawer ta kalla sannan ta kai hannunta a hankali ta dauki wayar ,siririn murmushi tayi da taga me kiranta sannan ta dauka wayar a hankali tace:" assalamu alaikum" saida ya lumshe idanunsa saboda jin sweet voice dinta sannan ya amsa da " wa alaikumussalam cool one " murmushi tayi tace: ka yini lafiya " yace :" to alhamdulillah but I'm partially not fine "ya karasa maganar a marairaice " humm" kawai tace ganin batada niyyar magana yasa yace:" bazaki tambaye ni abunda ke damuna ba " still dai a marairaice yai maganar ,dariya ya bata saboda yanda yai maganar d'an dariya tayi sannan tace:"to what's wrong? " yace :" kawai nagaji da zama a garin nan ne ,na k'osa na dawo na ganki noor,not even that I just want you to be mine cos koda yaushe inaso na rika feeling dinki around, gashi rashin sanin matsayina har yanxu shike k'ara mun fargaba har inji sam na rasa nutsuwa ta" guntun ajiyar zuciya tayi tace:" I think advisably you should stop letting anything stop you from your work ..." Be bari ta k'arasa maganar ba yai saurin cewa :" your love is not "anything "noor it is everything to me ,so kinga there is no way I can get rid of it,noor inasonki irin Wanda ban tab'a tunanin yana existing ba , its a very special one noor ina jinki har a cikin jikina" ya k'arasa maganar cikin gajiyayyiyar murya ,Jim tayi kamar batason magana har saida yace:" shikenan I understand your silence ,babu komai zan cigaba da jira so take your time and choose what's best for your life cos nima bazan yafe ma kaina ba idan nai sanadin da zai sanyaki zabar ma zuciyarki abunda bata gama amincewa dashi ba" :" shikenan na fahimceka amma kadaina sanya fargaba a cikin ranka duk abunda zai faru tsararrene daga Allah idan Allah yayi zamu kasance tare babu mai hanawa "
" you're right noor, amma dole a rayuwa mutum yai putting efforts dinshi kan abunda yakeso sai ya nemi taimakon Allah so kinga in this instance babu laifi don na fad'i haka tunda ban sani ba may be kiyi turning request dina down" ya fadi a hankali

Has llegado al final de las partes publicadas.

⏰ Última actualización: Nov 06, 2018 ⏰

¡Añade esta historia a tu biblioteca para recibir notificaciones sobre nuevas partes!

ASALINADonde viven las historias. Descúbrelo ahora