ASALINA
Na
Ummu na'im
Follow and vote for me on wattpad@ummunaim
*page* 8
Ba tare da wani tunani ba ya cafko hannunta ya hadesu da nasa hannun yana cigaba da kallonta ,wani irin kaunarta yakeji na linkuwa a cikin zuciyarsa ,yayi kusan minti 3 yana k'are ma fuskarta kallo abubuwa da yawa suna yawo a zuciyarsa ,wani bangare na zuciyarsa kam tamkar garwashi haka yake jinshi ,wani irin makahon kishi ne ya taso masa zuciyarsa gabadaya ta kuntata ,tunda yaji sak'on da isa yazo ya fada na Neman noor da ake a waje yaji komai ya tsaya masa cak,ya rasa me ya kamata yayi din ya hanata fita ,yanxu ma kallon fuskarta da yakeyi ya k'ara jin wani sabon kishin na kara taso masa don sai yaga ta k'ara masa wani irin sihirtaccen kyau duk da babu makeup din da tayi, saida ya k'ara 2 minutes sannan noor ta samu courage din k'ara kallonsa don ita ma zuciyar tata ta Shiga rudani ,tambayoyi da dama take mata Wanda ita kuma ta gaza tattaro amsoshinsu, sunanta ya kira a hankali cikin kasalalliyar murya ,a hankali ta Kara dubansa " where are you going to? " ya tambaye ta kamar ba yason magana don kusan noor din kadai ta fahimci abinda ya fad'a shima don tana kallonsa ne yasa taji ,sadda kanta tayi k'asa a hankali tace:" waje" hannunta da ke cikin nasa yak'ara matsewa da k'arfi kusan daidai da yanda yake jin zuciyarsa a lokacin ,tsananin zafin da taji ne yasa ta d'an saki k'ara cikin siririn muryarta hakan yasa yai saurin sassauta rikon da yayi mata yana karanta addu'o'i da dama cikin zuciyarsa din idan ba haka yayi ba he might end up doing something he doesn't want to do , daurewa yayi yace: "OK ,ki kula da kanki" still yana mata wani irin kallo mai wuyar fassara itama cikin dakiya ta gyada masa kanta din she totally confused and his action made her speechless... a hankali ya k'arasa sakin hannunta ,itama a hankali ta juya ta nufi kofar fita a sanyaye duk jikinta babu kwari,at the same time tana k'ara ganin idon Yaya umar cikin idanunta kamar yanxu take kallon idonsa still tana cigaba da kokawa da zuciyarta saboda yanda takejin bugunsa na k'ara sauri
Nabeela da Aisha dake zaune suna ganin abinda ke faruwa were also confused ,nabeela wani irin bakinciki ya kamata idanunta sun cika taf da kwalla duk ta rasa me ke mata dad'i,Aisha kam cikin halin ko in kula tace :"_wai anty nabeela me ke faruwa ne " wani irin kallo ta watsa mata tace:" kije ki tambayesu mana" tana mik'ewa fuu ta wuce d'aki ta fad'a saman gado ta fara aikin kuka,Aisha kam binta da idanu tayi kawai ta girgiza kai taci gaba. da abunda takeyi
Noor kam ganin babu kowa a harabar gidan nasu yasa ta tambayi isa inda bak'on yake ,fad'a mata yayi yana falon bak'i batareda tace komai ba ta wuce can ,a bakin k'ofar ta tsaya tana tunanin yadda za'ayi ta shiga ,kusan minti 2 tayi kafin tai k'arfin halin yin sallama in her usual tone tana bude kofar falon jin an amsa mata sallamarta ,kanta a k'asa tai ma kanta mazauni cikin d'aya daga cikin kujerun dake falon ,a hankali ta gaishe shi ,be amsa mata ba saima tsayawa da yayi yana k'are ma fuskanta kallo ,itama rashin amsa mata da yayi yasa tai shiru kanta still na k'asa tana wasa da yatsunta ,shi kam abdallah kaman ya samu TV haka ya maisheta saida taji shirun yayi yawa ne ta d'ago da fuskarta ta kalleshi ,tsananin mamaki ne ya kamata a lokacin da taga Wanda yake zaune har saida abdallah ya fahimci haka cikin murmushinsa ya fara magana" barka da fitowa " ta amsa da :" yawwa barka ...ka yini lafiya" yace : lafiya kalau alhamdulillah " shiru ne ya d'an biyo baya kafin yai gyaran murya ya fara magana " am ...suna na Abdallah Abubakar, I'm from gombe but ina zama a kano,...,its obvious that you never seen me before right? gyada masa kanta tayi tana duban wani direction din daban,gyara murya yayi ya cigaba "well actually I first saw you at yola and...am...from that same instance I felt something stuck down here... I mean ... Deep down inside my heart...and that thing is just for you noor, why and how ? I can't say but I know quite well it all started from the very first instance I glanced at you ...kallon da nai miki was just once but that single glance had an unspeakable effect on me ...and I just felt that I need to find you ,cos both my heart and eyes are aching just for you noor" ya karasa maganar a kasalance yana dubanta ,shiru tayi na d'an wani lokaci tana jujjuya maganarsa har saida yakira sunanta cikin wani irin yanayi yace:"why are you silent noor ...please say something...I'm very eager to know whats in your heart,". A natse tace:" I don't get you Abdallah,I'm utterly confused ban fahimceka ba " ta fad'a a hankali and her voice says it all tabbas tana cikin rudani shima ya fahimci hakan since when she entered the room " smile din gefen baki yayi yace:" yeah you are of course confused that I can visibly see ,so kada ki damu ,I know my words all are clear for every mature lady wani irin yanayi ....a hankali ta amsa ya cigaba" I can see u are totally upset so ki aje wacan maganar da nai a gefe now just consider yourself sitting and talking With your bro OK ?...I mean just feel free " smile kawai tayi tana kallonsa ta fahimci yana da saukin kai hakan tasa taji ya birgeta har ta d'an saki jikinta
YOU ARE READING
ASALINA
General Fictionduk iya yanda mutum yaso ya gano irin yanayin da take ciki bazai tab'a ganewa ba don despite all that happened to her last night she's still wearing an expressionless face as usual but still takasa mancewa kamar kullum don abun yai matuk'ar d'aga ma...