ASALINA
Na
Ummu na'im
Follow and vote for me on wattpad@ ummunaim
*page* 9
Tunani kala kala suka dinga turo Kansu cikin zuciyarta ,tallabo kanta tayi da dukkanin hannayenta saboda nauyin da taji yana mata ,tunani take sosai amma duk yawancin akan Yaya umar takeyi ,still zuciyarta na k'aryata abunda idanuwanta suka gani kwance cikin idanun Yaya umar,a duk lokacin da yake kallonta itama takan shiga rudani don irin abunda take gani is nothing other than flows of love, may be wani abun ke damunsa da yake sanya yanyinsa canzawa haka,but Yaya umar bazai taba sonki ba,you are only his sister, ta Yaya zai so ki" zuciyarta ta fada mata don kokarin fire duk wani tunani a ranta "to idan abunda anty nabeela ta fad'a ma zuhra ya zama gaskiya fa?
O ya rabb!hakan na nufin nima na shiga sahun yaran da suka zo duniya ta haramtacciyar hanya kenan? Wani irin rad'adi taji a ranta da wannan tunanin ya shigo zuciyarta,tuni launin idanunta suka fara canjawa "Ya Allah!! Allah yasa hakan ba gaskiya ba ne,bansan yanda zan kasance ba if that turned out to be true, na san wannan dalilin shi zai zamo min Katanga da farinciki na,yes how can I be happy again bayan nasan daddy isn't my real father? Wannan tunanin na k'arshe ya sanya zuciyarta kuntata da raunana ,wasu irin hawaye masu d'umi suka fara bin kuncinta ba tareda ta shirya ba ,cikin sauri ta sanya hannunta tana share hawayen amma wasu sai k'ara zubowa sukeyi ,jin an turo kofa yasata saurin kwanciya kan gadon still bata bar zubda hawaye ba ,Hajiya ce ta shigo hakan yasa ta cigaba da kwanciya harsai da ta shiga bathroom sannan ta gyara kwanciyarta tai addu'o'inta ta kwanta tana ta kokarin kauda wannan tunanin daga zuciyarta ,ringing din wayarta ya dawo da ita reality ,abdallah ne ya kirata a sanyaye ta dauka ta fara magana,briefly sukai magana sannan kowannensu ya aje wayar ,nan Kuma ta fara tunanin Abdallah ,fuskarsa take kallo cikin idanunta ,murmushi tayi da ya tsaya saman lips dinta tabbas tasan Abdallah nada kyau ,don daka ganshi kasan akwai jinin fulani a jikinsa ba laifi he's handsome but ita ba kyau kad'ai take bukata ba , she needs a man that will always stand for her Wanda yake da hankali da mutunci Wanda yake sanya addininsa a farko kafin komai don wannan shi kadai zai iya kare mata mutuncinta a matsayinsa na mijinta,a haka har bacci ya sace ta ba tare data sani baYaya umar ma ta bangarensa bai samu wani sukuni ba koda yaje d'aki,tunani kala kala suka dunga turere niya a cikin zuciyarsa,tun lokacinda ya gama gaskata irin kaunar da yake ma noor ya dage da addu'a sosai akan al'amarin yana neman zabin ubangiji,yasan bazai samu Matsala ba ta bangaren daddy da Hajiya don a tunaninsa zasu fi kowa farincikin hakan yanzu tunaninsa bai wuce idan noor ta nuna tanada Wanda takeso ba don yasan daddy bazai taba aura masa itaba,amma duk da haka ya yanke shawarar tunkaran daddy da maganar don shi kansa yasan bazai iya jure wa ba kodayaushe soyayyarta ruruwa yake a ransa and he cant just withstands seeing her with another man,a haka yai shirin baccinsa ya kwanta cike da tunaninta
Sosai Abdallah yaji dadin samun gidansu noor da yayi da yanda ya sameta mai nutsuwa da sanyi bisa ga dukkan alama ba zai samu matsala da ita ba,a wannan karon kam ya gama amincewa da ya samu irin matar da yake burin aure kuma ya dau aniyar sanar da iyayensa ko shima ya huta da irin ciwon bakin da ake masa ,yasan tabbas Abbansa ba karamin farinciki zaiyi ba idan yaji labarin don ita Ummi tuni ya sanar mata tun lokacin da yaje yi mata sallama wurin bikin diyar engr Muhammad don a lokacin ya fada mata ya fasa tafiyar kuma ya fada mata dalilinsa ,side hugging dinshi tayi a lokacin cikin harshen fulfulde take fada masa irin farincikin da tayi don har ta fara tambayarsa ya nuna mata surukar ta ta though jinin Fulani ke yawo jikinta amma ita bata bar wata kunya tai mata Katanga da yaronta ba sosai take bashi kulawa kasancewarsa d'a d'aya tilo da Allah ya azurta su dashi ,dariya yayi a lokacin ya shaida mata yasa a dubo gidansu don sun wuce already a mota ,aikam cikin farin ciki tanuna goyon bayan daga tafiyarsa da yayi don ita tafi bukatar taga ya aje familynsa a kan kome duk da irin zugar da Hajiya saude take mata a kaikaice tanaso ta nuna rashin dacewar hakan wai almubazzaranci ne ,bata ko bi ta kanta ba ta sanya masa albarka da fatan alkairi,
ESTÁS LEYENDO
ASALINA
Ficción Generalduk iya yanda mutum yaso ya gano irin yanayin da take ciki bazai tab'a ganewa ba don despite all that happened to her last night she's still wearing an expressionless face as usual but still takasa mancewa kamar kullum don abun yai matuk'ar d'aga ma...