chapter three

646 35 0
                                    

ASALINA

Na ummu na'im

Follow me on wattpad@ummunaim

*page* 3

An tashi da wani irin yanayi mai dad'i sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a daren jiya,garin yayi luf luf ,daddan iska mai sanyi Wanda ke had'e da kamshin kasa mai dadi kawai yake kad'awa ,a karo na biyu ta kara juyi a saman gadon rungume da pillows dinta,kiran sallah subh data fara jiyo wa ne yasa ta mike da addu'a a bakinta don daama ba bacci takeyi ba,kai tsaye bathroom ta nupa ,toothpaste ta shafa a brush dintata wanke bakinta sannan tai wanka ta dauro alwala ,ko da ta fito bata tsaya yin kwalliya ba ,wani long gown na wani silky material purple naga ta sanya sannan ta fara sallah sai bayan ta idar da sallah ne ta gyara jikinta da kyau tai kwalliya mai kyau wace ta hau da yanayin shigarta ,har kusan karfe shida da rabi tana zaune a wuri guda, addu'o'in neman tsari da kaariya datake yi a kullum ta k'arasa sannan ta mik'e,tana fitowa daga dakinta ta shiga dakin Hajiya ,a saman carpet take zaune hannunta dauke da al'qur'ani tana karantawa , a gaskiya Hajiya mace ce mai kula da addini sosai,a gefenta ta zauna tana sauraron karatunta ,har saidata k'arasa Surar data ke karantawa  sannan ta juyo suka gaisa da noor,dan gyara gyaren da baza'a rasa ba ta tashi tayi don wurin babu wani datti komai yana a muhallinsa yanda ya kamata

Main kitchen ta nupa bayan kara kimtsa bangaren Hajiya da tayi tana jiyo maganar masu aiki sama sama ,gidan tsit yake don duk y'an gidan suna dakunansu,cikin fara'arta tashiga kitchen din, Baaba Jamila ta juyo cikin sakin fuska tana fadin:"a a noor har an fito kenan " ta amsa da :"ehy Baaba Jami nima na dawo bakin aiki ne tunda yanxu na samu hutun makaranta" ta fadi cikin raha,"to barka da dawowa diyar kirki " tace cikin dariya don dama indai tana gida tare suke aikace aikacen kitchen da ita,da murmushi kan fuskarta tace "yawwa baba Jami ,kun tashi lafiya?"" Lafiya qalau noor,gashi amma kin makara dan mun gama kayan Karin gabadaya kunun Hajiya ne kawai ya rage yanxu zan dama mata" " to baaba Jami kibar mun kunun na k'arasa hadawa" ta fadi tana karban siever da take tace tsamiya dashi,sakar mata tayi tana fadin " ki dan kara kadan akan yanda aka saba yi don nasan likita ma zai bukata" tom kawai tace ta maida hankali kan hada kunun tsamiyar,bayan sun gama a tare suka fidda kayan break din zuwa dinning,tana shirin nufar dakin mummy sai taga ta fito cikin shigar alfarma na wani haddaden lace mai kyau ,dama mummy irin matan nan ne masu son ado da kece raini ,tsayawa tai ta gaishe ta ,fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa mata kaman hadin baki sai ga umma itama ta fito ,itama tayi das da ita cikin doguwar rigar atamfa red colour ,ya kuwa amshe ta saboda skin dinta nada d'an haske,itama dai gaisawa sukayi har zata wuce umma ta dakatar da ita tace "wai yanaji shiru ne haka badai sauran suna daki ba har yanxu ?":" ehy umma kila basu k'arasa shiryawa bane "cewar noor" ko kuma suna can suna bacci ba maza jeki taaso su ,taya zaa ce har yanxu basu tashi ba ,ina ganin na kusa rabamuku aiki a gidannan don son jikin yaran nan ya fara yawa,common sense dinsu bazai fad'a musu ga abunda ya kamata suyi ba' umma ta fadi tana karasawa dining Kujera taja ta zauna directly opposite to mummy ,nan suka fara yin breakfast dinsu ba tare da sunjira yaran sun fito ba, yanda umma tai tunani haka abun yake don abarbaje ta saamesu cikin daki suna bacci, humaira ce kawai bata a wurin  da alama tana wanka ne sbd karan shower da take ji ,a hankali ta fara tashin Aisha ,kusan 3 minutes ta dauka Kafin ta tashi,Aisha ce ta tada sauran duk suka mike suna hamma don baccin ba wani ya ishe su bane,ita dai ficewa tayi da taga sun tashi ta koma daki ,bata dade ba ta fito dama wayarta ta tafi dakkowa,a falo ta samu Hajiya har ta fito tana zaune a saman carpet ,kai tsaya kitchen ta shiga ta kwaso kayan abincn Hajiya don ita a falo take zama ,duk gabadaya y'anmatan a lokaci dayasuka fito lokacin kam su umma sun gama nasu break din suna sakkowa daga dinning  su kuma suna wucewa zuwa dinning din ,kallon da umma tai musu ne yasa suka fara bada hakuri suna sun tuba don sun San sunyi laifi alamr zaku gamu dani kawai taimusu da ido suka  wuce zuwa dinning su mummy kam zama sukai  a falo  wurin Hajiya suna dan taba hira suna kallon tashar HUDA TV at the same time , noor   take zuba mata kunu,har bayan ta gama zama tayi tana jujjuya kunun da spoon ba ma tada niyyar tashi tai breakfast,sarai hajiyar ta d'ago ta don tasan yanda take wasa da abinci hakan yasa ta karbe kunun daga hannunta tana fadin:" kinga bani kunun nan kiga tashi kije ki karya abinki " bata ce komai ba ta mik'a mata ta mike zuwa dinning,koda ta isa dinning din tsayawa tayi tana tunanin wani irin abinci zataci wlh ita ba dan anmatsa mata ba batajincin komai,chocolate tea ta yanke shawarar sha hakan yasa ta juya zuwa kitchen,sauran kam basu bi ta kanta ba sunata faman cin abincinsu

Har sun gama cin abincin zasu bar dining din nabeela ta hango shi ya shigo falon ya had'e sosai cikin wata rantsatstsiyar farar shadda filtex ba k'aramin kyau yai mata ba ,don shigar da yayi ya haska light chocolate colour skin dinshi ,ai komawa tayi ta zauna tana kara duba warmers din abincin don bata son mik'ewa a tunaninta dinning din zai nupa don yin break,zama tai sosai tana kare masa kallo a fakaice daga sama har k'asa ,a fili ta nuna maitarta Wanda da ace sauran Wanda suke falon zasu lura to da sun d'ago ta alokacin ,agogonsa rolex dake manne a hannunsa   ya duba don bayaso ya makara sannan ya zauna a k'asa kusa da Hajiya daya bayan daya ya gaidasu sannan suma k'anninsa suka gaidashi, jawo flask yayi ya  zuba kunu cikin cup ya fara sha,nan yake shaida ma Hajiya taron kungiya ta likitoci da zai halarta a Kaduna a yau "to madallah Allah ya taimaka " tai masa addu'a "amin " kusan duk suka amsa a lokaci d'aya ,"Bara na dakko ruwa "ya mik'e yana fad'a ,cewa tayi:" Aa zauna mana baga k'anninka nan ba sai dayansu ta dakko maka " har afra ta mik'e dan ta dakko mishi  ya dakatar da it a"no barshi kawai yi zamanki Bara na dakko ay na riga na mik'e",wucewa yayi zuwa kitchen ,shigarsa kitchen din tai daidai da fitowar noor rike da mug na hot chocolate tea dinta ,garam taji ta jikin wani Abu kakkarfa saurin dagowa tayi saboda zafin dataji lokaci guda ta saki y'ar k'ara,hannuntayai saurin rikewa yace :I'm sorry kin kone ko? Tuni idonta ya Tara kwalla cikin marairaicewa tace: yaya I'm sorry please,I wasn't aware of your entrance" k'aramin bakinta ya kalla lkcn da take motsa shi kai kace ba magana takeyi ba lokaci guda yana jin sweetness na voice dinta har tskiyan kanshi,a hankali yace:"no you shouldn't be sorry kinji ,ba laifinki bane ,nine na shigo da sauri,so I'm sorry kinji kanwata" ya karasa maganarsa with a smile ,hannunshi dake rike da nata ya kalla yace:"now come, let me wash this mess OK?"yana maganrne yana janta zuwa wurin sink din kitchen din,da dan murmushi ta CE:"to ai Yaya gabadaya Gaban rigar tawa ta baci"saida yaji Yar a jikinsa lokacin dayakai dubansa zuwa gaban rigar nata,dakewa ya danyi yace :"to ay sai in wanke maki niba brother inki bane "ya fadicikinsigar ba'a kanta ta d'an duk'ar kasa a sanyaye tace :to ay Yaya dole sai na sake wasu kayan and you also need to change, kaga na bata ma jiki idan ba'a wanke yanxu ba stain din bai fita" ajiyar zuciya kawai yayi ya dauki ruwa yana fita kitchen din ta baya ,wayarsa ceta fara neman agaji ,Ciro ta yyi daga aljihunsa yaduba yaga Dr.al'amin,dagawa yayi ya kara a kunnensa," hello Dr .how far?"daga can bangaren Dr. Al'amin ya amsa masa:"normal fa,alhamdulillah,har ka isa wurin taron ne"yace :"no ban ma fita gida ba yanxun nan dai make son fita in sha Allah ."Dr.al'amin yace:" OK to ni yanxu na shigo Zaria ko zaka tsaya ne na k'araso sai mu tafi tare?"Dr.umar yace :"to shikenan babu matsala sai ka k'araso din " alright thanks,bye" da haka suka ajiye wayar,

Cikin shiga na wani lallausan voile material kalan sararin samaniya ya fito ,yanxu ma yana looking so devilishly handsome,a gurguje yai sallama da Matan dadaynsa,ya nupi dakin Hajiya daga karshe sallar walaha ya saamu tanayi hakan yasa ya zauna jiranta dan bazai iya tafiya bata sanya masa albarka ba ,don dukda tana kakarshi jinta yake a ransa tamkar mahaifiyarsa ,tunda itace ta zamo masa Uwa don Allah bai nupa zaiyi rayuwa da biological mum dinsa ba,she died since when he was just 9 years,tana idarwa tajuyo gareshi tai masa addu'o'i ta sanya masa albarka as usual ,kaman hadin baki sai ga noor ta fito cikin shigar lace itama kalar sararin samaniya,ba k'aramin kyau dunkin tai mata ba ,a gefen Hajiya tai ma kanta wurin zama sannan ta gaidashi don dama dazu basu gaisa ba ,saurin kauda tunanin da ya fara a ransa yayi ya amsa mata batareda muryarsa ya fallasa komai da yake gudana a mind dinsa ba kusan 2 minutes ya kara kafin ya mik'e ya fita din kiran da Dr.alamin yai masa cewa ya karaso,har ya kai bakin kofa yaji noor tace  :"Yaya Allah ya kiyaye hanya yasa Ku dawo lafiya" dan juyowa yayi Kazan yace:amin amin kanwata,nagode" murmushi kawai tai masa, kallon 10 seconds kawai ya k'ara mata brain dinsa ya hasko masa abubuwa masu yawa a kanta ,da dan Saudi ya bar falon,
A motarsasuka tafi suka bar ta Dr .al'amin a gidan....

ASALINAWhere stories live. Discover now