ASALINA
Na
Ummu na'imFollow and vote for me on wattpad @ummunaim
*Page* 6
... Saitin bakinta ya hadesu wuri guda ya hura mata iska da karfin gaske aiko sai gashi ta fara motsi da eyes dinta alamun ta farfado ,itako nabeela wani irin bak'inciki ne ya turnuk'eta da taga yanda Yaya umar yai ma noor ,ji tai kaman ta zunduma ihu
Bude idanuwanta tayi a hankali ,idanuwan nan sun rine sunyi jawur ,kamar a mafarki haka takejin komai,don har yanxu brain dinta ya Gaza tattaro duk wasu bayanai da amsoshin da zuciyarta take bukatan sani ,cikin dauriya take amsa sannun dasuke ta jero mata lokacin da umma take kokarin mikar da ita ,a hankali ta k'arasa mik'ewa da kanta don nuna babu abunda ke damunta duk da cewa ji take zuciyarta na mugun zafi kaman garwashi, da taimakon umma suka isa d'akin Hajiya ,a saman gado ta kwantar da ita ,gaba daya suka fita suka bar wurin don ta huta .
Yana zaune shiru a dakinsa ,ya tasa laptop din sa da ya dakko don ya fara wasu tsare tsare na asibitinsa da aka kusa kammalawa amma yaji bazai iya hakan ba ,duk wani numfashi da yake fitarwa da tunaninta yake tafiya ,a hankali ya sauke ajiyar zuciya a karo na biyu ya dauki wayarsa don yai dialing number ta amma ya kasa,duba lokaci yayi yaga 11:30pm ,may be ta samu bacci yanxu bai kamata na tashe ta ba ,ya fadi cikin ransa ,kusan minti biyu ya kara dauka yana tunanin abunda ya kamata yayi don yana matukar son ganinta ,yana bukatar sanin halinda take ciki don yaga tashin hankali sosai a cikin idonta ,ganin ya kasa samun nutsuwa ne yasa ya tashi ya shiga band'aki ya watsa ruwa ,yana fitowa ya kimtsa kansa ya zira farar jallabiya ya fita,koda ya shiga falon babu kowa ciki , kai tsaye ya wuce dakin Hajiya don yasan a can zai sameta ,yana shiga dakin ya hangota kwance saman gado tana bacci a hankali ,fuskar ta tai fayau da ita tsayawa yayi yana kallon ta wani irin sonta na kara mamayeshi ,after each and every second yanajin linkuwar kaunar da yake mata ,kusan 5 minutes yana tsaye yana kallonta har yad'an jingina da bango ,tunani da dama suke yawo a zuciyarsa game da dalilin da yasa ta shiga halinda take ciki a yanxu, k'arar bude kofar bandaki yasa shi waigawa Hajiya ce ta fito da alama alwala tayi ,ganin Yaya umar a tsaye yasa tace: a a umaru ya akayi bakaje ka kwanta ba,sha biyu saura mintoci kadan fa yanxu" murmushi yayi ya k'arasa shigowa d'akin yana fadin:"ta ya zan iya bacci baki sanya mun albarka ba ,nazo ganinki ne naga lafiyarki kafin na kwanta,kuma bacci ya kaurace ma idona Sam shiyasa" sakin baki tayi tana kallonsa ,don yana maganar ne yana kallon fuskar noor dake bacci cikin kokarin kauda tunanin da yazo ranta tace :"to ai sai kazo mui hira tunda kai bakada mai tayaka ,kaga da ace kayi mun kishiya da sai in huta nima tunda ni na tsufa" k'arasowa cikin dakin yayi ya zauna a saman rug din dake tsakiyar dakin fuskarsa dauke da murmushi yace:"ai in sha Allah an kusa ,kin kusa sanin kishiyarki",dariya tayi tace:"to Allah ya nuna mana dan sai na fi kowa farinciki"amin ya amsa mata, man zafi ta dakko don ta Shafa ma k'afarta sannan ta zauna ,shi ya karbi man zafin ya dunga shafa mata yana mammatsa mata kafar,jefi jefi suke hira ,a karo na biyu ya k'ara d'aga idanunsa ya kalli noor sannan yana fuskantar Hajiya yace:" ta fada miki abunda ya sameta dazu" ta fahimci inda maganarsa ta dosa duk da bai ambaci suna ba,hakan tasa tace:"ta ce mun babu abunda ya sameta ,bigewa ce kawai tayi," "amma kin yarda da hakan " ya tambayeta , Hajiya tace: "to tayiwu bigewarce kasan tsautsayi ance ba ya wuce ranarsa" shiru yyi badan ya yard a bigewar tai ba ,ahaka ya k'ara kusan 20 minutes kafin ya tashi ya koma d'akinsa
************
ta bangaren noor kam tayi kokari sosai wurin ganin ta rage damuwar dake ranta ,don ko cikin dare lokacin da Yaya umar yashigo duk tana jinsa ,tayi kamar tana bacci ne don batason ya tambayeta game da komai,bayan ta jima tana salloli da ambaton Allah ta samu nutsuwa sosai a zuciyarta ,ta yanke shawarar bin komai a sannu har ta fahimci gaskiyar al'amarin ,dukda cewa idan ta tuna maaganar nabeela na iya kasancewa gaskiya ta kanji duk duniyar babu dadi ,addu'a tayi sosai don tasan tabbas akwai wata a k'asa don magana batayin kanta.
Har suka gama shirinsu na wucewa gidan biki ba ta bari wani tunani ya hanata sukuni ba duk da cewa yana cikin rantaa haka ta cigaba da kasancewa a gidan bikin ,duk inda ta shiga sai an yaba ta ,nan na fahimci cewa ba kyan halittar noor bace kadai yasa ake ganin kyawunta,don suma dangin Engr Muhammad fulanin usuli ne farare dasu kyawawa saidai zubin kyawunsu ba daya bane don ita noor kyawunta mai sanyi ne Wanda ba'a cika samun irinsu ba ,its a unique one gaskiya,nutsuwarta,hankalinta da kyan zuciyarta su suke k'ara haska ka ta ....sai misalin k'arfe 9 na dare sannan driver yazo daukansu ,haka suka tattara suka koma gida nabeela ko taso a barta ta kwana a gidan don har ta yi new friends ,kuma tana jin dadin hirar da takeyi,ba kamar wata zee zuru da idanunta suke a bud'e had exchanging numbers sukayi da nabeela don tasu tazo daya
*********************
Gaskiya bikin Khadija diyar engr ya k'ayatu sosai tun ranar laraba ake shagali har ranar lahadi inda duk suka tafi yola don can amaryar zata zauna , ko a can yola ma wani sabon shagali ne ya taso, nan suka nuna al'adun fulanin usul, duk gabadayansu suna gidan amaryar mutane sun cika mak'il,noor dai hayaniyar ta fara yi mata yawa don kanta har ya fara juyawa ,ba tare da ta tai notifying kowa ba ta fita daga gidan amaryar,so take ta koma can gidan engr amma batasan yanda zatai ba ,tana tsaye wajen gidan amaryar ta hango Khalid k'anin amaryar ba tare da tai masa mgn ba ma ya k'araso wurinta bayan sun gaisa ne ya tambayeta Inda ta nupata fada masa gidansu ta keson komawa,motarsa yaje ya dakko tunda dama tana fake ne a side din titin yace:shigo na ajiyeki,nima can zan koma' murmushi kawai tayi tana kokarin bude motar wayarta ta fara ringing ,ganin yanda take kokarin Ciro phone din daga cikin bag dinta cikin sauri yasa Khalid yai parking sosai yai mata alama da ta amsa wayar,hakan yasa ta jingina da motar ta fara magana cikin nutsuwarta ,suna nan tsaye wasu rantsattun motoci suka fara shigowa layin har guda 5,daidai saitin gidan amaryar sukai parking ,ganin mutane a wurin yasa ta fara kokarin bude motar ta shiga hakan yai daidai da kiran da Aisha tai mata da d'an karfi,Wanda naga ya kafe noor da ido tun shigowarsu layin naga ya juya kansa kadan ya maimaita sunan a hankali bakinsa dauke da murmushi ,a wurin noor kuwa duk y'anmatan sun fito suma don kiran da umma tai musu cewa su dawo su fara shirye shiryen komawa Kaduna ,wata wacce naga sun manne da Nabila naga ta k'ura ma motocin ido tana ma nabeela nuni a fakaice ,y'anmatan gaba1 sun rud'e da ganin irin wannan had'uwa ,basu k'ara rudewa ba sai lokacin da haddadden saurayin dake zaune bayan motar ya fito ,ganin yanda suke yi ne yasa noor tai musu magana din kada suyi abun kunya ya gane duk shi suke kallo ,jingina yayi shima jikin motar kamar yanda tai a lokacin da zakin muryarta ya dira tsakiyar kansa don motocin nasu sunyi kurkusa a karo na 2 ta k'ara musu magana "ga Khalid ze maida ni yanxu ko zaku jira driver ne still?"Afra tai saurin cewa
"Ki tafi kawai ya kaiki idan kin kosa mu zamu jira driver din"
Noor tace
" to shikenan ,sai kunzo"
Motar da bude ta shiga a hankali tana musu wavingWayarsa ya Ciro ya tura text kamar haka
" Abdul find out where that car that took off now is going to" ya tura ma daya daga cikin Wanda suke tare .nan da nan wata mota cikin motocin nan ta fara binsu har saida yaga inda suka tsaya*********
Haka suka shirya suka koma Kaduna ,y'anmatan babu labarin da sukeyi sai na wannan saurayin,har afra fadi take ita wallahi yayi mugun kwanta mata arai sonshi takeyiKo bayan sun dawo daga bikin basu koma Zaria ba sunaa gidansu dake Kaduna,nabeela ta karbi shawarin da wata k'awarta zee zuru ta bata akan Yaya umar kuma ta kuduri aniyar amfani dasu don ita gsky tana matuk'ar son auren Yaya umar ,tunda suka koma bata samu ganinsa ba sai bayan kwana uku,bata San cewa shima a lokacin ya tafi abuja ba dan kammala wasu takardu da zasu bashi dama na mallakan private hospital, duk kwanakin da yayi bai ganta ba yayi sune ci kin takura kuma ba yaso ya fito mata kai tsaye da maganar din ita bata mishi kallon da ya wuce na brother ba ......
!
YOU ARE READING
ASALINA
General Fictionduk iya yanda mutum yaso ya gano irin yanayin da take ciki bazai tab'a ganewa ba don despite all that happened to her last night she's still wearing an expressionless face as usual but still takasa mancewa kamar kullum don abun yai matuk'ar d'aga ma...