part 22

605 36 1
                                    

11/07/2018

🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*

🌐 *HAJOW*🌐
🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐

Page *22*


*Bismillahir Rahamanir Rahim*


Ummah ta ce,
"Baka ji nane?"

Naufal kamar zai yi kuka ya ce,
"Kije gida na sauwake miki saki daya!"

Kuka Naima ta fashe dashi. Halima kuwa tai saurin mikewa ta yi wajen ta tana cewa,
"Tashi tashi ki tafi gidan ku."

Tana tura ta tana kuka haka ta fita. Naufal ma daki ya shige yana kukan dan Allah ma ya sani yana son matar sa tana faran ta masa.

Ummah kuwa murna take haka ma Halima. Na'ima ta tafi gida tana kuka kamar ranta zai fita.

Napep ta tara a kofar gida da bata jin zata iyab tuku ma. Mai napep ya kai ta har can gida tana bashi kudi ta sauka tana kuka ta shiga gida tana kala ihu kamar wacce akace yau mahaifiyar ta ta mutu.

Mami ta fito da saurin ta kama ta ta ce,
"Lafiya? Ke me ya faru? Me ya faru? Lafiya?"
Mami ta jero mata tambayoyin nan gaba daya.

Kuka Na'ima ta cigaba da rusawa, Dady ne yai magana ya ce,
"Wai lafiya?"

Dady ya fito da sauri dan ganin me yake faruwa.

Cikin sheshekar kuka ta ce,
"Saki na yayi."

Mami ta ce,
"Sakin ki yayi?"

Na'ima ta ce,
"Wallahi kanwar sa da Maman sa basa so na. Baki ga abinda suke min ba. Suka saka shi ya sake ni."

Mami ta ce,
"Ashe wannan yaran bai da mutunci. 'Yar tawa ta cikina zai wa wannan ya kuwa sanni kuwa."

'Yar dariya tayi ta ce,
"Lallai Naufal."

Kallon Na'ima tayi. Mami ta ce,
"Daina kukan mana daina kukan. Dan Allah ki daina kina daga min hankali."

Kukan Na'ima ta rage, amman duk da haka batai shiru ba.

Cikin kuka Na'ima ta ce,
"Ni wallahi Ummah shi nake so bazan iya rayuwa bashi ba."

Mami ta ce,
"Ya isa. Menene haka maza nawa ne gasu nan waje barkatai."

Kuka Na'ima ta kuma fashewa dashi ta ce,
"Ni wallahi Mami shi kadai nake so bazan taba aure ba in bashi ba."

Dady dake gefe yayi dariya ya ce,
"A binda taiwa wani shi ya biyo ta yanzu. Tayiwa matar wanta ba wani abu bane wannan illa sakamako, daman an ce *duk abinda ka gina shi zaka girba.* sannan ance *in zaka gina ramin mugunta ta kina shi dai dai kai"*

Mami ta ce,
"Haba Alhaji me ya kawo maganar Amina kuma a cikin nan."

Dady ya ce,
"Allah ba azalumi bane, duk abinda kayi sai ya bika. Kin san ance, *'Kai 'kayi koma kan mashekiya* kun so mata hakan ta faru da ita sai gashi ya faru akan ku. Ke kuma sai ki shiga ki ta zaman gidan aure wata uku amman kina gida Allah ya shirya. Abin da ciwo na rasa ina tunanin ku ya shiga kwakwalwar ku ta dashe akan aikata laifi. Kuma ki sani makarantar da kika saka ta ta haddace komai tayi degree yanzu ga result nan. Kuma ke na fada miki."

Ya fada yana nuna Na'ima ya ce,
"In da zaman gida ne gashi nan kiyi tayin sa."

Ya shige ciki ya barsu anan. Na'ima kuma ta kara sa kuka tana cewa
"Mami dan Allah ki bashi hakuri dan Allah Mami."

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Where stories live. Discover now