part 15

657 40 1
                                    

02/07/2018
🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*

🌐 *HAJOW*🌐
🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐

Page *15*


*Bismillahir Rahamanir Rahim*


Washe gari tin asuba da ta tashi tai sallah ta koma bacci dan bata wani samun bacci tinda aka fara hadahadar bikin nan.

Ahmad kuwa bayan ya dawo daga massalaci ya shiga dakin ta.

Gani ta yayi can tsakiyar gado ta cure gu daya sai kace me jin sanyi.

Wani murmushi ya saki yana jin tausayin ta a ransa.

Yasan ko wace amarya tare take kwanaa da mijin ta a daki daya ko da ace ba abinda zai shiga tsakanin su.

To amman wai shi me ya hana shi zuwa wajen sahibar sa abar kaunar sa.

Kansa ya buga yana yin tsaki. Kan gadon ya hau ya janyo ta jikin sa.

Ya jima yana kallon ta kafin daga karshe shima baccin ya dauke shi.

Karfe goman safe ta farka. Jin ta jikin mutum yasa ta tai saurin rufe idanun ta.

Kwanciyya ta cigaba dayi har shima ya farka. A hankali ya zare jikin sa gudun kada ta tashi.

Bangaren sa ya nufa inda yana fita ita kuma ta mike ta fada ban daki.

Wanka tayi ta fito ta saka wata doguwar riga mara nauyi.

Hijab ta saka har kasa ta fara aikin gayaran gidan.

Sai da ta dauki awa biyu sannan ta gama. daki ta koma  ta shiga ban daki ta kara yin wanka.

Fitowa tayi tana shafa mai. Tayi kwalliya me kyau sannan ta bude akwatin ta.

Wani less ne orange kala me adon purple ta dauko.

An masa dinkin riga da zani. Kayan sun mata kyau sosai. silvern dan kunne da sarka ta saka sanna ta dauko turare ta bade jikin ta dashi.

Wayar ta ce tai kara ko da ta duba sai taga Anty ce

Dauka tayi da sauki ta ce.
"Ina kwana Anty?"

"Lafiya lou Amarya ya kuka tashi ya mai gidan naki."

Kasa Amina tai da kai ta amsa da
"Duk lafiya lou."

"Ok daman aiken abinci zan muku na ce bari na fada miki."

Murmushi Amina tayi ta ce,
"To Anty angode Allah kara girma."

Anty ta ce,
"Ba komai Amina na dauke ki kamar yadda na dauki Ahmad ne da Basma yar ta."

"To Anty Nagode. Allah saka da alheri."
"Ameen sai anjima,"

Sukai sallama. Zama tayi a gefen gado a ranta ta na tuno Mama ko ya take.

Sai kuma ga hawaye nan. Gaskiya ta yi kewar Mama wacce kullum suke tare Amina bata taba yin tafiya ko barin Mama ba.

Tana cikin kuka Ahmad ya shigo dakin. Ganin halin da take ciki yasa yai saurin karasawa gun ta.

Kamota yayi inda a take ta ji wani shock ya shiga jikin ta kamar yadda shima Ahmad din yaji.

Da sauri ya janye hannun sa. Kara kamo hannun nata yayi ya ce,
"Haba Meenal mene na kukan da wannan safen. Me nayi miki. Dan Allah kiyi hakuri in nai miki laifi."

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Where stories live. Discover now