part 18

625 31 0
                                    

07/07/2018
🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*

🌐 *HAJOW*🌐
🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐


Page *18*



*Bismillahir Rahamanir Rahim*



Bayan wata daya.

Haka rayuwar su Amina da Ahmad ta dinga kasancewa cikin jin dadi da kwanciyyar hankali.

Sai dai abu daya ne Ahmad baya taba iyawa shine kusantar Amina dan da ya zo kofar dakin Amina da niyyar ya kwana zai ji kuma ya fasa baya son shiga.

Na'ima kuwa har yau tana gidan sai gulma da take kwashewa take fada wa Mami.

In kuwa Yaa Ahmad ya tafi aiki tai ta yin abubuwa a gida Amina kuwa in ta shige Daki bata fitowa in ba girki take ba ko wani abun.

Na'ima dai ta takura mata dan tai ta jifar ta da bakaken maganganu.

Bata taba fadawa Ahmad ba dan bata son hada shi da yar uwar sa.

Na'ima kuwa Tana jin haushin yadda take ganin Ahmad ke kula da matar sa duk da ita ma tana burin ana mata kamar haka.

Tana lura da rashin kwanan da baya yi a dakin ta a wannan ba karamin dadi take ji ba.

Dady kuwa har gida ya zo yaga dakin Amina. Ya saka musu albarka tare da bata kudi masu yawa.

Bayan har yanzu be dauke abinda akewa Mama ba.

Sosai yai musu nasiha ya kuma ce da Amina in da akwai matsala tana tarar sa kai tsaye ta fada masa.

Ta dauke shi tamkar mahaifinta sannan duk abinda Ahmad yai mata tana fada masa kar taji koma.

Daga baya yai musu addu'a da nasiha mai ratsa jiki.

*******
Yau kamar kullum tin asuba ta tashi sai dai yau bata jin karfin jikin ta.

Da kyar ta iya gyara gidan ta hada musu break.

Ta shiga tai wanka ta shirya cikin wani farin less wanda akai masa ado da jan abu.

Tayi kyau sosai tai dinkin doguwar riga. Sai dai da ka kalle ta za kasan bata jin dadi.

Bayan ta gama shiryawa ne tayi bangaren Ahmad. Shima lokacin ya fito cikin shirin shi na tafiya office.

Tana ganin sa ta karasa da sauri tana karasa ta saka masa maballi.

Tana gamawa ta durkusa ta ce,
"Ina kwana?"

"Lafiya lou. Ya kika tashi."
Ya yambaye ta yana kamo hannun ta.

Mikewa tayi ta amsa da
"Lafiya."

Kallon ta yayi ya ce,
"Meenal me yake damun ki?"

Kallon sa tayi ta ce,
"Me ka gani?"

"Haba Meenal kinsan dai ina gane ki ko ta murya bare kuma gani gaki."

Murmushi tayi ta ce,
"Weather ce kawai."

Ta kama hannun sa sukai daining. Sai da suka ci sannan ya mike zai tafi aiki.

Sai da ta rakashi har bakin mota sannan ta dawo.

Daki ta shiga ta kwanta sai bacci. Ba ita ta tashi ba sai karfe daya.

Alwala tayi tai sallah sannan ta fita dan samar musu abinda zasu ci.

Tuwo Ahmad ya ce yana so miyar allayahu wannan yasa aikin ya rike mata ga shi bata jin dadi.

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Where stories live. Discover now