part 23

605 35 1
                                    

11/07/2018

🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*

🌐 *HAJOW*🌐
🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐

Page *23*


*Bismillahir Rahamanir Rahim*





Ahmad ganin ta samu sauki ya sa ya mike ya fadawa Ibrahim yanzu zai dawo.

Wajen Dady ya nufa. Dady na gida zaune a falo shi da Mami sai Na'ima.

yana zuwa ya sawa Dady kuka.
Dady ya hau tambayar sa lafiya.
Ya ce,
"Dady Meenal ce ba lafiya."

Nan ya kwashe komai ya fada masa. Yana fada wa Dady.

Mami kuwa budar bakin ta sai cewa tayi,
"Ba wani ciwo sun je sun kama wata ne, an yi magani abu ya dawo kan ta."

Na'ima da ke zaune gefen ta, ta ce,
"Kai Mami dan Allah ki bar maganar nan gwara a tsaya ayi bincike aga gaskiyar me yake damun ta in ya so sai ki magana."

Mami ta ce,
"Ke dallah rufe baki. Wane irin bincike za'ayi bayan kowa yasan su waye su. Da farkon dai tin da akai auren nan ba ko barin wata bare ciki abu fiye da wata bakwai da aure fa. Gashi nan taje ta jawo wa kan ta jaraba ai, in kuwa ta warke shi zata kama."

Dady dake kallon ta rai a bace ya ce,
"Abinda nake so dake Hajiya shine ki daina zargi akan abinda baki sani ba. Sannan kuma har yanzu kin 'ki son yarinyar nan bayan kinsan Ahmad ba karamin yaro bane yaro ne mai hankali ya girma kuma yasan abinda yake dai dai. Na tabbata Amina babban rabo ce gare mu kuma sai kinyi alfahari da ita na tabbata."

Mikewa Mami tayi ta ce,
"Nifa bazan iya cigaba da zama da yarinyar nan ba wata rana a kawon gawar 'dana ba."

Na'ima ma mikewa tayi ta ce,
"Haba Mami nifa abin nan yanzu na saduda ya kamata, mu daina sa musu ido mu barsu su shakata dan Allah mu daina takura musu, haba Mami daman ance *duk abinda kayi kaima sai an maka.* domin ni shaida ce,"

"Dallah can yi min shiru shashasha sakarya. Mayun kuke so to kuje sa cinye ku gaba daya."
Tayi cikin daki.

Zama Na'ima ta yi ta ce,
"Dady to yanzu mene abin yi."

Dady yace,
"Bari na kira Malam Tanimu."

Dady ya kira shi sai cewa yai baya gari amman anjima zai dawo zai shigo insha Allahu.

Haka akayi kuwa da magariba sai ga malamin har gida wajen Dady.

Dady da kansa ya dauki mota suka nufi gidan Ahmad a daren.

Amina kuwa tana can ta tashi kamar ba ita tayi ba dan har ta gyara gidan ta musu girki.

Tai wanka tai kwalliya kamar yadda ta saba. Tana zaune a dakin ta Yaa Ahmad ya shiga.

Kallon ta yayi cikin so da kauna ya ce,
"Meenal kizo Dady na kira."

Da sauri ta mike tana cewa.
"Lah Dady ne ya zo."

Hijab ta saka, suka fito a tare. Tana ganin wannan malamin taji juwa na dibar ta.

Da kyar ta iya karasawa gefen Dady kafin ta gaishe shi ta zube agun.

Murmushi Malamin yayi,  Ahmad ya kalla ya ce dauko ruwa. Tofi yayi a cikin ruwan ya watsa mata.

Wata kara ta saki. A ruwan ya karayin wani tofin ya kara watsa mata a fuskar ta.

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Where stories live. Discover now