part 12

645 36 0
                                        

29/06/2018

🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Labarin wata mata*

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*



Page *12*


*Bismillahir Rahamanir Rahim*

*Masoya ina ganin sakon ku. Ina godiya Allah ubangiji ya bar zumunci. Nagode sosai*


Ai kuwa da dare  ya kira ta kamar yadda ya sabar mata.

Kafin ta tafi ckul xai kira acam ma yana kira yaji lafiyar ta. Haka in ta dawo sannan da dare kafin su kwanta ma zai kira.

Yanzu ma da ya kira  labarin abinda Yasmeen ta fada ta bashi. murmushi yayi ita kuwa dariya take, tana cewa,
"Wai Yaya sai suna mana kallon masoya wai ya ake soyayyar nan ne ma. Har da ake cewa haka."

Shima dariyar yayi, ya ce,
"Nima ana yawan fadan hakan amma ni na cewa ke kanwata ce, soyayya kuma ni da ba budurwa ba da wa zanyi soyayya."

Dariya tayi ta ce,
"Yauwah Yaya Allah ya kamata ka fito da mata da ka dawo musha biki dan Allah na matso naga Matar ka tinda baka fada min batun ta ba."

Dariya yayi, ya ce,
"Kema kinsan da ina da budurwa kece farkon sani ko?"

Kai ta gyada, sannnan ta ce,
"Eh ina Sadyn ka kuwa?"

Ta kece da dariya saboda tini dramar da ya fada mata sunyi akan wai tana son sa dan Allah ya aure ta.

Kwafa yayi ya ce,
"Ni kike wa dariya ko? Zan rama ne, bari kema nasan yadda zanyi dake."

Ya danyi shiru, Amina ta cigaba da dariya.

"Yauwah ina Garbatin ki?"
Ya fada yana dariya shima.

Fuska ta bata kamar yana gaban ta tai shiru. Duk maganar duniya yayi amman tai shiru wannan yasa ya hau bata hakuri dan sam baya jurar fushin Amina. Sai da yai ta lallashin ta sannan ta sauko suka cigaba da hirar su.

Sai da zata kwanta ne sannan sukai sallama.

Ahmad har aiki yake koya mata ta waya ko online.

Sosai suke mu'amala duk wanda yaga yadda suke mu'amala ko yaji labari zai ce soyayya suke.

Dan daga baya kowa kishin kowa yake bama sa son daya acikin sun ya ce, yayi budurwa ko saurayi daga ya fada za su fara fushi da juna har sai ya bada hakuri.

Haka rayuwar su ta kasance,  Ahmad kuwa wani amininsa da suka tafi daga Nigeria tare shi ne ya fahintar dashi da son juna suke.

Lokacin da shima ya tinkare shi da maganar son Amina yake musu yai masa.

Sai da ya tambayeshi yadda yakeji game da ita sannan ya ce masa.

"A gaskiya nasan shakuwa ce ke tsakani na da Amina wacce ta kai har ake mana kallon soyayya muke."

"Yadda kuma nake jin ta araina nasan tana da matsayi me girman gaske. Kasan abinda baka sani ba shine wallahi ko rashin lafiya take nima sai nayi haka nan jikina na fada min a halin da take ciki na dadi ko akasin haka. Ina jin ta kamar Na'ima."

Dariya Muslim yayi ya ce,
"Karya kake yanzu in Na'ima na rashin lafiya kaima kana yi? Ina Na'ima na wani halin kai ma kana ji a jikin ka. Duk abinda kake ji game da Amina kana jin shi game da Na'ima kullum ka kwashe lokaci baka kira ta ba ko bakuyi chat ba."

Ido Ahmad ya lumshe tabbas yasan duk ba haka bane ga Amina kawai yake jin kuma yake iya haka.

Ya jima kafin ya ce,
"Ni fa duk da haka ban yadda ba."

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Where stories live. Discover now