part 20

652 41 0
                                    

10/07/2018

🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*

🌐 *HAJOW*🌐
🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐

Page *20*

*Ina mai kara baku hakuri. Yanzu dai ai a hankali ba lokaci abubuwa sun rike. Dan haka ba kullun zakuna ganin posting ba sai an ssamu lokaci.*

Nagode.

*Bismillahir Rahamanir Rahim*



Ibrahim, Dady ya kalla ya ce, ya kira Na'ima ta kawo musu lemo da ruwa.

Na'ima dake daki tana waya da saurayin ta Ibrahim ya kai mata sakon Dady.

Bata san su waye ba dan haka da saurin ta taje ta debo musu.

Tana zuwa Falo taga Amina sai ta hade rai. Direwa tayi ta gaishe da Ahmad ta juya zata tafi Dady ya kira ta.

"Baki ga Antyn ki bane?"
Dady ya tambaye ta.

Fuska ta kara batawa ta ce,
"Ina yini?"

Tayi ciki ba tare da ta tsaya amsawa ba. Mami ma mikewa tayi tai cikin gidan.

Dady ne ya girgiza kai yana mata addu'ar Allah ya shirya ta.

Ahmad ne ya matso da kayan da Amina ta kawo Bude fulas yayi yana nuna masa.

Dady sai dadi yake ji yana murna. Yana sa mata albarka.

Yana ganin miya ya ce,
"Amina daukon waccan shinkafa, inci da miyar ki."

Daukowa tayi hade da plate. Abincin ta zuba masa, ta zuba masa miyar da nama da yawa.

Mikawa masa yayi yana sa mata albarka.

Ci yake yana santi sun sha hira. Har ya gama yaci snacks din.

Santi yake ya ce,
"Uhmm Ahmad ashe wayo kai min. Kullum wannan dadin kake ci, ka barni da abincin su Mamin ka."

Murmushi Ahmad da Amina sukai. Dady ya ce,
"Amina Allah miki albarka Allah kara hade kan ku. Allah ya baki zuri'a ta gari."

Ahmad da yaji maganar Dady sai jikin sa yai sanyi.

Dady ya kalle shi yace,
"Ahmad ya dai?"

"Ba komai!"
Ya fada yana yin kasa da kansa.

Amina ma kasa tayi da kansa. Dady yayi murmushi. suka dinga hira har tara da rabi.

Amina ce, ta ce,
"Ina Mami zatai mata sallama."

Dady ya kalle su ya ce,
"Ahmad ka raka ta kuje ko?"

Suka mike sukai ciki. Mami na zaune akan gadon ta suka shiga da sallama.

Amsawa tayi tana ganin Amina ta dauke kan ta.

Dan durkusawa tayi ta ce,
"Mami mun fito zamu tafi sai da safe."

Tsaki Mami tayi ta ce,
"To Mayya sai da safe wallahi kurwa ta da ta dana tafi karfin ki."

Shiru Amina tayi ta mike, Mami ta bita da wani mugun kallo ta ce,
"Shegiya matsiya ciya. Mayya kin zama mana karfen kafa kin makalewa 'dana kamar cingum."

Amina dai bata juyo ba ta fice idon ta jajir.

Ahmad kuma da ransa yai mummunan baci yai shiru dan ba yadda zaiyi da mahaifiyar ta shi.

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Where stories live. Discover now