57

2.4K 152 0
                                    

🔺5⃣7⃣🔺
Drivern bai zarce koina ba sai ma saukin kamal,su uku suka fito daga cikin motar suka shiga gidan,sun samu  kamal yana waya yayinda ake sanar dashi cewa basu sami imtihal a gida ba,yana gama wayar kenàñ driver ya shiga sanar dashi abinda ya faru,wanda hakan yasa kamal ya shiga masifa sosai,yana mai cewa kai da aka ce blocking din sa kawai zakayi! me ya kai ka har ka bugi motar sa! driver yace"kayi haquri ban san da zuwan shi bane kwata kwata,
sbd ya jima da parka motar sa yana waya, yayinda ni kuma na dakata muna jiran isowarshi, ban ankara ba sai jin nayi ya bugi motar,kasancewar gudun da yake sosai, da ace baya gudu da komai zai zo a yanda kake so.......kaga ni bana son jin wata maganar banza!,ace ku dukan ba wanda ya lura da lokacinda zai tada mota...kai tukuna ma wane irin wawaci ne  ya same ku, wanda ake so a tsayar an samu ya tsaya da kanshi har kwa wani tsaya jiran sa,wanda hakan yaja  kun 6ata min lissafi na gabadaya,ni bana ga Imtihal kuma shi kaje  ka kashe..... Ai kuwa yanzu kake da damar samun Imtihal a sauqaqe sbd mijinta ya mutu,idan ta haife abinda ke cikin cikinta sai kaje musu a matsayin kaje neman aurenta,kamal ya kai dubansa ga wanda ke maganar wato doctor usman da yanxu ne shigowar sa, cike da takaici kamal y buga tsaki yace wannan zancen banza ne naji kana yi!ta yaya kake tunanin zan iya jira har ta haife abinda ke cikin cikinta wanda koda ace plan dina yayi zan sa a zubar da cikin ne sai muyi aure,amma bawai don na jirata ba.

Yanzu dai ka sallame su tukun sai muyi magana,kamal ya jefa musu bunch din kudi en dubu dubu.

Bayan sun fita ne, doctor usman ke cewa,wai kai meyasa baza ka haqura da ita bane ka huta, kaje ka nemo santaleliyar buduwar ,ba ka tsaya ga wacce tayi aure har ta samu ciki ba..... Mtsw amma kai wawane wlh baka san meye so ba! ba ciki ke dauke a jikin Imtihal ba ko 'ya'ya goma ta haifa ina sonta a hakan!...ai Kaine wawan wanda ko samun Imtihal din kayi iyayenka baza su yarda ka aure ta ba! amma kawani nace wa abinda baya da asali... Kul! wlh kar ka sake kiranta marar asali!ko bata da asali naji na gani zan zame mata komai,don haka kar sake kiranta da hakan, and get out of my house!ba musu Doctor usman ya fice sai dai ransa a 6ace.

Haka ma kamal ransa ba qaramin 6aci yayi ba,fridge ya bude ya dauko ruwa yasha ko zai sami sassaucin zafin da zuciyar sa ke masa, amma sai yaji ruwan tamkar ruwan zafi,hade da wani  irin gumi da yaji yana keto masa ta koina,toilet yaje ya watso ruwa,.

Bayan ya fito ne ya kasa zama ya kasa tsayi yana tunanin wata mafita,wanda yafi son yaje shi da kanshi ya aiwatar da abinda yake ganin zai samo imtihal da kanshi ba tare da ya sake dauko hayar en fashi ba sbd yau sun bashi haushi ba kadn ba.
   Haka ya qaraci tunanin sa da neman mafita,har guraren 12 dare,bai sami mafitar ba, sae yaji gabadaya duniya tayi masa zafi, musamman ma yanda yasa a ranshi cewa yau Imtihal ta zama tashi har abada sae gashi aka sami akasin haka.

      Fita yayi daga 6angaren sa ya nufi 6angaren da ya bawa mutannen sa masauki ya samu sun bar gidan amma duk kayan mayen su na ajiye sun sha sun rage saura, haka kawai ya kama abubuwan yana sha ba sassauci,sai da ya fara jin kansa na juya masa ne ya daina sha, ya shiga jijjiga kanshi ya fadi ruf da ciki kan tsakiyar falon,can yayi yunqurin tashi amma ya kasa sbd yanda abubuwan suka buge shi har baya iya gane sama yake ko qasa kasancewar yau ne na farko da ya fara shan kayan maye.
    Daga haka bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi,wanda har safe yana a gurin ko motsawa bai yi ba.

A 6angaren Imtihal kuwa kwance take tana bacci taji umma na mata knocking hade da kiran sunan ta, da qyar ta iya amsa kiran sbd yanda take jin jikinta ba dadi ga kuma yawan faduwar gaba da yake damunta tun jiya.

Ta jima sosai kafin take
   tashi  a hankali taje ta bude qofa sannan ta nufi hanyar toilet sai taji  faduwar gaba sosai,tunawa tayi da lokacin da Afnan yace idan taji hakan ta riqa addu'a hakan yasa ta shiga yin addu'a har ta rage jin abun....
umma ce tayi sallama ta shigo dakiñ tare da fadin wai ke sai yanzu zakiyi sallah,bayan tun dazu na tashe ki!yi haquri umma wlh tun jiya da dare nake jin jikina ba dadi, ko yanzu ma da qyar na samu na tashi, to Allah ya sauwaqe kuma idan  kika gama sallah kizo Abbanku ya dawo yana kuma son magana damu,taçe to" ba tare da tayi mamakiñ jin dawowar sà ba sbd tun jiya da safe akace yana hañya, nan ta fice toilet tayi arwala tayi sallah.

IMTIHAL (COMPLETED) .Where stories live. Discover now