67

2.4K 392 21
                                    

🔺6⃣7⃣🔺
Ta rungume shi sosai tana kuka,police suka mata magana kan ta tashi za'a fice dashi theater room sbd ciwon da yake dauke dashi likitawa sunce sai anyi masa aiki cikin gaggawa ko za'a iya ceto ranshi.

Tashi tayi a hankali tana share hawaye,dago idonta da zatayi taga tsohon mijinta,tare da likita kusa dashi yayinda doctor ya miqa masa takarda ya sa hannu.

Sannan aka fice da kamal zuwa theater room.

Tsohon mijinta ya kalle ta sau daya ya kauda kai kamar yadda ita ma ta kauda kai taje ta sami guri ta zauna.

Shima zuwa yayi ya zauna nesa da ita.

A 6angaren su imtee kuwa, ganin Alhj Basheer a qasa,yasa farin cikin da take qoqarin nunawà ya koma zuwa  tashin hankali,ai kuwa ta safko kan gadon ta tafi  gun Alhj Basheer tana jijjiga shi sai dai kwata kwata baya motsi,Afnan ne ya bude qofa ya tafi cikin sauri ya kirawo doctor.

Doctor na shigowa aka kama Alhj Basheer cikin sauri aka dora shi kan gadon da Imtihal ta safka.

Doctor ya ba kowa damar fita daga cikin dakin sbd ya samu natsuwar duba Alhj Basheer, sai Nusaiba kadai da aka bari wacce duk abinda yake faruwa bacci take, har zuwa yanzu.

Da suka fita kowa ya kasa zama ya kasa tsayi,sae ka rasa wanda yafi shiga damuwa a cikin su,musamman ma hajiya da kuma hajiya saratu wato wacce muke kira da mahaifiyar Alhj basheer (sai dai yanzu mun gano cewa ba ita ce mahaifiyar sa ba hajiya ce mahaifiyar sa).
kallo daya zakayi musu kasan suna cikin tashin hankali,sai ka rasa wacce ta fi son sa a cikin su.

Maman Nusaiba kuwa wato hajiya zainab matar Alhj Basheer ita ma ba'a iya misalta tashin hankalin da ta shiga,ko kuma nace hankalinta ne ya rabu kashi biyu ga murnar samun erta Imtihal ga kuma ciwon zuciya da ya sami mijinta Alhj Basheer.

Gurin yayi tsit
kowa yayi zugum  musamman ma Abba da umma,yayinda suke kallon Imtihal da ta kasa tsayuwa  guri daya.

Afnan ne yakai dubansa gareta yaga sai faman zarya take ga tulun cikin da take dauke dashi, yaje ya  jawo hannunta ya zaunar da ita,ya samu guri a kusa da ita ya zauna yace"my imtee kar kisa damuwa a ranki sosai kinji,inshaAllah zai ji sauqi,
da qyar ta iya gyada kanta tana mai kallon qofar dakin.

Sun dau lokaci suna jiran fitowar doctor.

Doctor ya fito ya sanar da su cewa Alhmdlh,an ciyo nasara ya farfado,  amma baza Ku sami damar shiga ba sai idan ya farka daga bacci sbd ba'a so a tashe shi.

Nan ne fa hankalin kowa ya dan kwanta.

Hajiya  zainab tazo gurin Imtihal ta zauña tana mata kallo cikin tsananin so irin wanda mahaifiya ke yiwa er ta,Imtihal ta kai hannu ta riqo hannayen ta  gam yayinda ta saki murmushi a fuskar ta  tana  kallonta sae  jin  take wani  irin farin ciki yana ziyar tar zuciyar ta marar misaltuwa,hajiya zainab tace Imtihal mai kyan hali kenan ko, haqiqa ni ina mai matuqar farin ciki da kasancewar ki 'yata,kuma ina fatar kema zakiyi farin ciki da kasancewa ta mahaifiya a gare ki,sai dai nasan a lokacin da kika tsinci kanki da jin labarin ke  er tsintuwa ce kinyi matuqar baqin ciki da kuma Allah wadai da mahaifiyar ki kamar yadda naji labari a gun suraj,Imtihal tayi shiru tana tuna lokacin da suraj  yace ta daina fadin muna nan kalamai akan mahaifiyar ta dmn bata san wace irin qaddara ce tasa aka tsinto ta a bola ba........ai kuwa sai  ta fashe da kuka ta fada jikinta ta rungume ta sosai tana fadin"ki yafe min mama dmn gaskiya ne na kasance mai ganin laifin ki da fadar maganganun da basu da ce dake ba, sbd duk a tunani na kece ki ka jefar dani da kanki.
    Sai gashi a yau na fahimci ba haka bane,abinda suraj ya fahimtar dani kenan.
   Kiyi haquri mama ban san haka bane da ban furta wadanan kalamai a kanki ba.
   Hajiya zainab ta dago Imtihal daga jikinta tana share mata hawaye tace"Imtihal ba komai na yafe miki komq me kika ce akaina, ai a bisa rashin sani ne,don haka ki daina kuka yanzu lokacin farin ciki ne a gare mu,godiya ya kamata muyi wa ubangiji,ba kuka ba har dai da yasa kika taso a hannun qanin mahaifin ki wato Ahaji hamis,da kuma matar sa hajiya saudat, da ta riqe ki tamkar er ta,wanda ina roqon Allah da ya saka musu da gidan Aljanna akan riqon amana da suka miki, ta fadi hakan ne tana mai kallon  umma da Abba, wanda hakan yasa suka fadada murmushin su kafin suke cewa Amin,kuma muma munji dadi sosai da Allah yasa Imtihal ba'a haramtacciyar hanya ta fito.

Daga haka kowa yayi shiru,ba wanda ya sake cewa komai sai Afnan dake ta kallon Imtihal da ta sake komawa a jikin hajiya zainab ta lafe,yaji  farin ciki fal a ransa,yana ji baya da wani  sauran baqin ciki a rayuwa,dama rashin iyayen Imtihal ne ke damun shi sai gashi yau Allah ya nuna ma Imtihal iyayenta,ko iyayen ma mutanen kirki wadan da suka same ta ta hanyar halal.

Hajiya saratu da iya talatu da indo sai kallon su suke cike da jin dadi da Sha'awa.

Yayinda oganniya hajiya ke kallon Imtihal tun dazu kamar mai son zuwa tace da ita wani  abu amma hakan ya nemi ya gagare ta musamman ma idan ta tuna irin yanda ta nuna mata tsana duk da cewa ba rashin asalin ta kadai ne yasa take nuna mata tsana ba,ta tsani mutum marar asali ne a bisa abinda hajiya saratu tayi mata, na  raba ta da Alhj Basheer da tayi,wanda kan baqin cikin haka ne yasa ta kamu da ciwon hawan jini,shiyasa a duk lokacin da ta cika tuna hakan sai hawan jinin ta ya tashi duk da cewa Allah ya bata wasu 'ya'yan amma Abban Afnan kadai ya tsaya sauran duk sun rasu,amma hakan bai hana tafi  son Alhj Basheer fiye da Abban Afnan ba sbd shi Alhj Basheer sun jima suna neman haifuwa kafin su same shi,sai kuma ta rasa shi a dai dai lokacin da take ganin zata sami damar bashi kulawa.
   Wanda da ace mutuwa yayi ba dauke shi akayi ba da baza ta sa kanta a tunani irin haka ba.

To yanzu Alhmdlh Allah ya bayyana mata dan ta Muhammad Basheer.
      Sai dai farin cikin ta yaqi ya kammala kuma bata jin zai kammalu har sai Imtihal ta yafe mata akan tsanar da ta nuna mata bata ji ba, ba bata gani ba.
   Wanda bata jin zata iya barin har su fita daga asibitin nan,ba tare da ta roqi gafarar ta ba.

   Hakan yasa hajiya ta fara tako a hankali har ta isa gurin Imtihal,tare da kiran sunan ta,a hankali Imtihal ta dago tana kallon hajiya.




Anan zan dakata se naga yawan Vote din da zan samu se in cigaba.

Se mun had'u nan da sati Biyu.


Kada a manta da danna tauraron nan shi ze sa nayi making mind dina ko na cigaba da kawo muku littafin ko na dakata.


Nagode Sosai Ghost Reader's ana tare.

IMTIHAL (COMPLETED) .Where stories live. Discover now