66

2.2K 226 4
                                    

Kindly Press the Star Button Please.



🔺6⃣6⃣🔺
Cike da mamaki Alhj basheer ke kallon wacce ke bakin qofar,wato wacce zàncen ya fito dàga bakinta.
yace"Iya Talatu! (cewa da mai aikin gidansa)yaci gaba da cewa "me kike cewa ne haka?ni ina naga wasu 'ya'ya bayan wadanda nake da su yanxu sai kuma wacce ta rasu?qwarai kuwa haka ne amma wacce kake tunanin ta rasu ba mutuwa tayi ba sbd ita ce Imtihal din nan da kake gani.

Mamaki qarara a fuskar kowannen su musamman ma Maman Nusaiba, da kuma abokiyar zamanta wacce taji abin ya daure mata kai sosai, yayinda Imtihal ta tashi zaune tana kallon iya talatu.

Iya talatu ta kira indo mai aikin gidan su Afnan tace"indo shigo daga ciki, ba musu indo ta shigo, iya talatu tace da Alhj Basheer inace kasan wannan? Qwarai kuwa ni nasan indo ba er ki bace,qwarai kuwa 'yata ce na tura ta aikine  a gidan hajiya saudat (cewa da umman Afnan)dmn Imtihal kadai  sbd burin da ke  cikin raina na sanar da kai er ka ba mutuwa tayi ba tana raye...... Iya talatu garin yaya haka bayan cewa akayi 'yata bata ko zo da rai ba,,, wannan shiri ne kawai na matar ka hajiya hasina (cewa da abokiyar zaman Maman Nusaiba) ta fadi hakan ne tare da nuna ta da yatsa,ai kuwa kowa yakai  duban sa ga hajiya hasina wacce duk da irin rudun da ta shiga bai hana ta iya furta cewa "qarya kike yi iya Talatu!

Da mamaki Alhj Basheer ya kalli iya talatu sbd yasan halin hajiya hasina matar kirki ce, yace"iya talatu anya kuwa zancen nan naki gaskiya ne ko kuwa kuskure kikayi ba a nan kika so kawo zancen ba,,,,ba kuskure a ciki, kuma tabbas zancen da nake sanar da kài gaskiya ne ba qarya a ciki dmn bazan ta6a
manta wata rana da daddare ina a nawa daki ina bacci sai naji yo sautin kukan suraj sosai, na tashi da hanzari na na nufi dakin hajiya Zainab (cewa da maman Nusaiba)yayinda na same ta tana ta faman naquda,
hakan yasa na lalla6a suraj nace ya tafi daki na yayi bacci.

Ni kuma na tafi gurinta dmn na taimaka mata sbd ko a qauyen mu na kan kar6i haifuwa.

Hajiya hasina ce ta shigo ta same ni, cike da murmushin ta tace na tafi kawai zata kar6i haifuwar,sanin cewa ma'aikaciyar asibiti ce yasa na fita ban kuma yi tunanin zata cutar da ita ba sbd yanda naga suna zaman lafiya da ita.

  Amma ashe ba anan gizo yake saqa ba,zaman lafiyar daine amma abin bai kai har zuci ba.
Wanda hakan yasa ta bawa hajiya Zainab wani  magani da yasa ta qara shiga wahalar naquda sosai,
ta kuma tafiyar ta zuwa nata daki.

Jin kukan jinjira ne yasa tayi saurin dawowa ta sami nice na kar6i haifuwar,sbd nishin hajiya zainab da naji kamar zata mutu shiyasa na dawo dakin ba shiri,yayinda na shiga taimaka mata har ta haifo erta wacce fitowar ta keda wuya hajiya zainab ta suma.

Hajiya hasina na ganin haka  tace nayi sauri na dauko reza a yanke cibi a samu a ceto ran hajiya zainab.

Na tafi cikin sauri har ina hadawa da tuntu6e sae dai koda na dawo ba jinjira ba uwar tafiya,ga hajiya zainab kwance cikin jini, nan na shiga neman hajiya hasina  ban ganta ba sai kukan jaririya dana nake jiyowa yana fita ta hanyar gidan.

Hakan yasa na shiga bibiyar inda sautin kukan ke fitowa.

Abin mamaki abin daure kai na hango hajiya hasina dauke da jaririya a cikin kwali ta miqawa marigayi idi  mai gadi tare da miqa mishi kudi masu yawa wanda suka rikita shi har ya shiga washe baki  ya kar6i jaririyar sai gyada kai yake tayi kamar kan dan qadangarwa,da yake idi yana dan da ta6in hankali.
da haka har ya fita da ga gidan.

Cikin sauri na 6uya dmn kar hajiya hasina ta ganni,
tana shigewa gidan nayi sauri na bi bayan idi har ina hadawa da gudu kar ya tsere min kasancewar bai san dani ba, tafiya mukayi mai nisa har gurin wata qatuwar bola da ke kan titi,yaje ya ajiye jaririya  ya juyo,
nayi saurin 6uya amma hakan bai hana ya hango wulgawa ta ba,nan ya shiga rarraba ido ko zai ga wa nene,ni kuma sai faman qara 6uya nake,,,ban ankara ba naji saukar qaton dutse  akaina,ya kuma tafi da gudu,ni kuma tuni jini ya wanke min fuska na durqushe a nan gurin  yayinda na fara ganin bishi bishi  wanda nayi minti 15 a nan gurin ina faman danne kai, gashi ina jin yanda jaririyar keta faman kuka ba halin na cece ta,sbd yanda na bugu aka.

Ina cikin hakane na hango hasken mota ta tsaya a dai dai nan gurin bolar,wanda ke cikiñ motar
ya fito, na dago kai na da qyar  ina kallon shi,sae kawai naga Alhj hamis (Abban Afnan) wanda na jima da sanin sa sbd yana da en uwa a nan qauyen mu shiyasa akai akai yake zuwa garin, wanda duk yaje se ya samu talakawan da ya tallafa ma,
ciki har da ni nasha samun tallafinsa shiyasa bazan ta6a manta shi ba.

Gaban motar sa ya bude yana duba wani  abu, wanda yana cikin haka ne ya jiyo sautin kukan jinjira ya daina aikin da yake cike da mamaki ya shiga dube dube a inda yake jiyo sautin kukan,fitilar wayar sa ya kunna sbd gurin ba haske, ya shiga yadiya har ya kai gun kwali ya jima yana kallon abinda ke ciki cikin tsananin mamaki,wanda da hanzarin sa ya koma mota ya kira hajiya saudat(umman Afnan)

Wanda ita ma tana ganin abinda ke cikin kwalin ta shiga mamaki  sosai,sun jima suna mamaki, sannan suka shiga tattauna wa tsakanin su sbd na hango sai magana suke amma bana jin me suke fada.  
Suna gama zancen da suke suka dauke ta suka saka a mota,
na yunqura da qyar na tashi ina yi musu hannu  amma ba wanda ya ganni a cikin su,har suka tada motar su yayinda jiri ya debe ni na zube a nan gurin.

Ban sami kaina ba sai da safe na ganni a asibiti, a nan asibiti hajiya hasina ta min kashe di, wanda ya rikita ni sosai kan kar na kuskure na sanar da kowa  gaskiyar abinda ya faru.
hakan yasa nayi shiru da baki na,amma bani da niyar barin abun a raina har sai na sanar da kai dmn abu ne da bana jin zan iya barin sa a cikin raina, sai dai ina tunanin ta yanda zaka yadda da zance na dmn hajiya hasina mace ce mai yi maka kirki sosai ta yanda bana tunanin kai tsaye zaka yadda da zance na.

Hajiya
Zainab kuwa  kwanan ta biyu bata san inda kanta yake ba.

Da taji sauqi ne hajiya hasina  ta sanar da ita cewa er da ta haifa bata zo da rai ba kuma har an kaita makwancinta,haka kaima  ta sanar da kai ta waya sbd kayi tafiya koda akayi haifuwar.

Ni kuma ban iya bari na sami sauqi ba na tafi gidan Alhj hamis sbd na san halin da jaririyar take ciki.

Koda na shiga gidan na sami hajiya saudat na bata madara cike da kulawa tamkar er cikin ta.
   Afnan kuwa sai murna yake ya sami qanwa.

Na zauna muka gaisa  bayan mun gama gaisawa sai saqe saqe nake a cikiñ raina ta yanda zan samarwa indo aiki a gidan dmn na riqa sanin halin da jaririyar take ciki kafin na sami damar sanar da kai gaskiyar lamari.

kamar hajiya taji me nake qisawa a cikin raina tace min tana ko buqatar er aiki sbd ta rage mata wasu ayyukan gida, cike da jin dadi na nuna mata eh za'a samu wanda hakan yasa na kawo musu indo.

Haka indo taci gaba da aiki a gidan su yayinda ko yaushe ina cike da tunnanin ta yanda zan sanar da kai cewa er ka tana raye bata mutu ba wanda sai a yau Allah ya bani ikon damar sanar da kai.

Gabadaya dakin sai da kowa ya sauke nannauyen ajiyar zuciya musamman ma hajiya da taji jikinta ya mutu liqis sai kallon Imtihal take tana tuna irin tsanar da ta nuna mata,ashe jikar ta ce bàta sani ba.

Alhj Basheer ko idon sa na kan matar sa hasina wacce taji gabadaya komai ya dagule mata sae zufa dake ta faman karyo mata da kuma tsanin jin kunyar Alhj Basheer har ta kasa hada ido da shi,hakan yasa ya tabbata lallai zancen iya talatu gaskiya ne.

Cikin tsananin 6acin rai ya tafi gurin ta tare da kife ta da mari yace kije na sake ki saki uku, kuma sai na hada ki da hukuma ta hukun taki, kuka ta shiga yi sosai dmn bata zaci zai yi mata hukunci saki irin wannan ba, gashi tana matuqar son shi fiye da tsohon mijinta.

Hakan yasa ta durqushe tare da riqe qafafun sa tana bashi haquri da nuna tsananin nadamar da tayi, tare kuma da rantsuwar cewa bazata qara yadda kishi yasa ta aikata mummanan aiki irin wannan ba, Alhj Basheer ya bangazar da ita gefe ya shiga shurinta ta koina,da sauri Maman nusaiba ta dakatar da shi,yayinda ita ma ya iza ta gefe ya ci gaba da shurin hajiya hasina kan cewa ta fitar mai da ido baya son sake ganin ta!kuma Allah ya isa tsakani na dake da kika munafur ce ni da halaye na gari!

Kuka sosai hajiya hasina keyi ta tashi tsaye tana ci gaba da bashi haquri,
zuciyar sa ce ta rufe,ya fitar da ita ta qarfin tsiya daga dakin, ya rufe qofar tare da saurin danne zuciyar sa,wanda ba shiri ya zube a nan gurin,su Abba suka yo kanshi da sauri.

Hajiya hasina kuwa tana fita taga en sanda sun shigo asibitin biye da wani marar lafiya ya dafe zuciyar shi da ke masa tsananin zafi yayin da nurses ke gudu dashi kan ambulance bed,numfashin ta ne ya tsaya cak tare da saurin riqo hannun shi tace"kamal my son!da qyar kamal ya iya bude idonsa yace mamah!

To masu karatu tambaya gare ku.

Shin kamal yayan Imtihal ne ?
ko kuwa hajiya hasina da tsofon mijinta ta haifi kamal?







More Vote Please.

IMTIHAL (COMPLETED) .Where stories live. Discover now