55

2.4K 147 0
                                    

🔺5⃣5⃣🔺
Afnan yace "subhanallah!ok Baba na gode..... ya tafi cikin sauri ya  shirya ya ja motar sa zuwa asibiti,bai wani  sha wahalar gane gurin da suke ba kasancewar ya kira Abba da ya shiga asibitin.

Da sallamar sa ya shiga dakin ya samu umma da Abba sunyi zugum suna kallon hajiya dake bacci,sai da ya gaida su ne sannan ya tambayi abinda ke damunta"Abba ya nisa cike da damuwa yace"hawan jininta ne ya tashi...hawan jini kuma Abba,dama hajiya na da ciwon hawan jini ne?eh sai dai yana jimawa sosai kafin ya tashi,to Abba me kuma ya tayar dashi yanzu,da tun inda aka fito bai tashi ba,kuma idan aure nane  naga cewa ba ra'ayin kaina ne za'a bi ba bare nace akanshi ne,Afnan wannan damuwar ta daban ce kuma bana tunanin qaramar damuwa ce wacce na rasa gane ainihin mene damuwar da tun muna yara take fama da ita wacce yawan tuna ta ke tayar mata da hawan jinin.

Sai dai na wannan karon yayi tsanani dmn tana tsaye  kawai lami taji faduwar ta,amma kuma Abba shine  baza ka bincike ta ka san wace irin damuwa bace wanda idan da akwai abinda za'a mata a yaye mata damuwar sai a mata, Afnan kenan ai sai dai addu'a sbd hajiya bata fadin damuwar bare har nasan wace iri ce,na sha tambayarta har nagaji bata gayan ba, kawai dai abinda na sani tun mahaifin mu yana raye idan ciwon ya tashi ya kan ce da ita ya kamata ace ta cire damuwa aranta  haka dmn kar taje ta jama kanta wata matsalar bayan abunda kike tunawa ma ya riga da ya tafi lokaci mai tsawo wanda ya kamata ace kin daina tuna abun,,,,,
sai dai tace dashi"ita kanta tana so ta cire damuwar a ranta amma abin ya faskara.

To Abba inace dai faduwar da tayi bai sa ta sami stroke ba dai ko?na yaushe kuma, gashi abinda na jima ina fargaba ne ,shiyasa a wannan ranar da ta fadi kan jin cewa kana shiga gidanta bata sani ba,nayi saurin tada ta sbd gudun faruwar haka wanda a sai Allah Allah nake kar ciwon nata ya tashi, bai tashi a wannan lokacin ba, se  yanzu ya kuma hada har da mutuwar rabin jiki.

Afnan yayi shiru yana jimamin abun,
can yace "Abba abinda nake ganin yafi shine a fitar da ita waje, ko za'a sami dawo da lafiyar rabin jikinta cikin gaggawa, dmn nasan a nan qasar zata jima tana wahalar jinya kafin a samu taji sauqi,, hakan nayi tunani Afnan wanda har na tsara tafiyar a gobe idan Allah ya kai mana rai.

Daga haka sukayi shiru Afnan ya d'aga daga gun gadon da hajiya take kwance wanda tun shigowar sa yake tsaye a gurin yana kallonta,yaje ya samu guri ya zauna.

A 6angaren Imtihal kuwa koda ta tashi daga bacci, bata sami Afnan ba wacce tayi tunanin office ya tafi har ma tana tunanin ko meeting din gaggawa ne ya same sa da har bai samu ya tada ta ta hada masa break fast ba.

Toilet ta fada tayi wanka ta shirya sannan taje ta sami abinda taci.

Tana gama cin abinci ta dan huta na 30mnt,
sannan ta tashi ta fara hada musu na rana sbd tasan idan Afnan ya fita bai yi karin kummallo ba yakan yi saurin dawowa gida yaci na rana.

Hakan yasa ta shiga aikin da sauri sauri ta samu kuwa ta kammala cikin lokaci.

Sai dai ga mamakinta har guraren qarfe 4:30pm Afnan bai shigo gidan ba, hakan yasa ta dauko wayar ta dmn ta kira shi se taji door bell, taje ta bude qofar tare da rungumosa a hankali tace"yaya Afnan sannu da zuwa,daga mata kai kawai yayi tare da dan guntun murmushi hade da shafo fuskarta, sannan suka fice daki,da shigar su ta dauko masa ruwa masu sanyi yasha, kafin yake fara rage kayan jikin sa,
a gajiye yakai  dubansa ga imtee wacce ta mayar da ruwa a frigde, yace "my imtee please muje ki taya ni wanka sbd yau a gajiye nake har bana jin zan iya murza jikina da kyau,tace"tam" tare da dauke kayan sa  da ya cire   takai su a gurin da ya dace, yayinda take tambayar sa abinda ya gajiyar dashi da yawa haka,"yace asibiti na tafi shiyasa ban samu naje office kan lokaci ba kuma koda naje na sami ayukka su min yawa sosai,hakan yasa har na kai wannan lokacin ban samu na dawo ba ban kuma samu na sakawa cikina komai ba,
cikiñ er damuwà imtee tace"to yaya Afnan me ya hana kaci wani  abu a can?sorry my imtee kinsan ban cika son cin abincin waje ba idan ba dole ba, ya fadi hakan ne tare da riqo hannunta yace "oya muje ki min wankan sae nazo naci abinci kinji,kai ta gyada mishi kafin suke ficewa toilet.

Sun dan jima kafin suke fitowa.

Cikin qana nan kaya ya shirya, Imtihal taje ta dauko masa abinci yayi zaune ya fara ci, ya kalli Imtihal da ke zaune a side dinsa yace "my imtee abincin fa baza kici ba?nuna cikin ta tayi tace "wannan babyn ne zai yadda a jira Daddyn shi, da dai ace  da ne da bana dauke da komai da zan iya  jira  har ka dawo sai muci a tare, Afnan yayi murmushi yace "ai gwara da ya hana ki jira ni din,dmn ni bana son kina zama da yunwa.

Daga haka sukayi shiru har ya kammala cin abinci, Imtihal ta kwashe kwanika takai kitchen ta dawo ta same shi yayi kwance yana hutawa,taje kusa dashi ta kwanta tana taya shi hutun, tace"yaya Afnan me kaje yi a asibiti? Hajiya ce ba lafiya ina so ma na sanar da ke anjima da dare zamu je dubata kasancewar gobe Abba zai fice da ita India, Allah sarki abun har ya kai haka Allah ya bata lafiya,Amin cewar Afnan.

Imtihál tayi shiru hade da marairai cewa tana kallon sa,
Afnan yace "lafiya my imtee?grapes nake so naci gashi kuma na cinye na jiya, kuma ina buqatar cinsa a yanxu, ka taimaka min da key din motar ka naje na siyo, uhm my imtee kenan ko ban siyo ba kina tunanin zan barki kije siyen wani  abu ne, meyasa baza ka barni ba?sbd bana da ra'ayin hakan, yi haquri ban sani ba ai da ban furta hakan ba, a'a ni ban dauke sa da zafi ba ai,
ban sani ba ko ke baki ji dadin hana kin da nayi ba,,Allah banji komai ba,,OK tashi kije kan mirror ki dauki key kije ki bude mota akwai grapes a ciki mantawa nayi ban shigo miki dashi ba,cike da murna ta sauka kan bed tare da fadin"thank u!
Afnan yayi murmushi ya bita da ido har ta fita yana mai jin dadin sauqin kai irin nata.

Bayan taje ta dauko ne taje kitchen ta dauraye ta samu guri ta saka sannan ta tafi dashi daki.

Da dare suka je suka dubo hajiya a asibiti suka dawo.

Da safe ma kafin a fice da ita zuwa India sai da suka je dubata, wanda daga can Afnan yakai  Imtihal gidansu Islam bai je dauko ta ba sae dare.

A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau kusan watan hajiya daya ana abu daya wanda sai sauqi ya samu abun ya koma tashi, shiyasa kwata kwata Abba ya ajiye zancen auren Afnan har sai ya ga lafiyar hajiya tukun.

IMTIHAL (COMPLETED) .Where stories live. Discover now