71

2K 156 0
                                    

🔺7⃣1⃣🔺

    Afnan ya sauke ajiyar zuciya yace ba haka bane my imtee lubna ce a kamfanin mu take aiki abu kawai taxo kar6a   amma abinda kike tunani bai ta6a shiga tsakani na da ita ba,asali ma bata ta6a zuwa gidan nan ba sae yau....bata ta6a zuwa nan gidan ba shine baza ta tsaya a harabar gida ba har sai ta shigo ciki hakan bai mata ba ma har sai da taje dakin ka ta kuma yi ale ale a kan gadon ka,ko kuwa ganin kake I'm only 19yrs shine kake min kallon qaràmar yarinya mara  wayo,hakan yasa kake yin abinda kaga dama,kana nuna min ai ba haka bane,,,sosai Afnan ya shiga mamaki da jin cewà har saman gadon sa imtee taga lubna ,
yace kan gado na fa kika ce! zan maka qarya ne ko kuwa duk a tunanin ka da kuka gama abinda kukeyi ta fita gidan,,,,duk da yaji zafin abinda ta fada amma yayi shiru, yana tuna cewa jiya ta riga shi shigowa gidan kuma tabbas da ya shigo yaga  lokacin da lubna ke saukowa downstairs wanda duk a tunanin sa imtee ta kamawa wasu kayan suka shiga dasu daki..... Imtee ta katse shi da cewa shine  kayi saurin  sallamar ta  don kar na fahimci abinda ke faruwa,, my imtee wallahi ba haka bane,kawai dai kuskuren da nayi shine da nace da Baba mai gadi ya bata damar shiga falo ta zauna ta jirani kafin nazo, wanda bansan kaudin da yasa har taje  dakina ta kwanta ba,amma a iya falo na bada damar ta tsaya, kuma my imtee ko ina aikata wani  abu da ita ta yaya rashin hankali na zai kai ga ranar da zaki dawo har ma naje dauko ki amma nace tazo...Hm yaya Afnan Kenan ai idan lokacin tonon asirin mutum yayi dabara 6ace masa take 6at,,, my imtee baki yarda dani bane wallahi ba abinda ya ta6a shiga tsakani na da wata mace a duniyar nan idan bake ba... Ta yaya kake tunanin zan yarda da kai!ta yaya zan yarda da mutum irin ka!ada dai na yarda da kai dari bisa dari amma a yanzu 0%,
ba kuwa zan sake yarda da kai ba har abada!bare har na sake yarda da cewa ni wata abu ce a rayuwar ka,,, please my imtee try to understand........
Don't ever try to call me ur imtee again!bcs tuni na fhmci cewa a iya le6en ka kadai sunan ya tsaya bai kai har zuci ba, na fahimci hakan tun a ranar da naji zancen aurenka,wanda da farko ban yarda da hakan ba sai gashi koda nazo dakin ka naji zancen a kunne na,shine da auren ya 6are takaici ya maka yawa har ka kasa haqura ka koma wa harakar neman mata,me na rage ka dashi!me na rage ka dashi da zaka min haka!......no my imtee ....I told u!ka kirani da Imtihal dina ko kuma ka kirani da asalin sunana wato Rabi'a,,,lumshe idon shi yayi cike da damuwa yana mamakin irin yanda take masa tsiwa haka da maganganu mara dàdin ji, yace to naji amma don Allah ki fahimce ni wallahi auren da na tashi yi ba'a son raina bane....ka dai ce min ba'a son ranka auren ya 6are ba zanfi yarda da hakan dmn na tabbatar da ace Nusaiba ba qanwa ta bace uwa daya uba daya,
da ba abinda zai hana ka aureta,sbd kwana biyu kadai suka rage ayi auren,amma da yake ni shara ce a gurin ka bani da wani  amfani, baka sanar dani  zancen auren ba,sai da naji a bakin Islam,,,imtee na 6oye miki zancen aure na ne sbd......sbd kafi so kawai naji gudar kawo amarya in yaso  baqinci yasa zuciyata ta buga na mutu ko,se kuyi amarcin ku cikin jin dadi da kwanciyar hankali ba mai takura ku...a'ah! What's wrong with u!
ta yaya kike tunanin haka daga gare ni,,,ya bazan yi tunanin haka ba, wata qil ma wannan  lubña kaine kace taje kan bed dinka ta kwanta,dmn na ganta na  nemi a raba aure na da kai in yaso ka nemo wata matar ka aura sbd ni ka gama amfanuwa da jiki na!tana gama fadar haka tace"sannan kuma ina neman alfarma daya a gurin da kar ka sake kawo min wata mace a nan gidan sbd ko ta jiya na raga matà ne a bisa wani  dalili da kuma tsohon cikin da nake dauke da shi, wanda da zarar na haife maka abinda ke ciki zan ajiye maka shi na bar maka gidan ba sai ka nemi ka koreni ba,
nida da kaina zan fita..... Tana gama fada ta fita daga dakin Afnan ya biyota  sai haquri yake bata akan ta tsaya ta saurare shi amma taqi.
Tana shiga dakin ta tayi saurin rufe qofa tare da saka key,bata ma iya dagawa daga gun qofar ba ta zube a nan gurin tana kuka mai cin rai.

Afnan kuwa bai fasa bata haquri ba har yana hadawa da dukan qofa.

Haka yayi ta faman dukan qofar har ya gaji bata bude ba sae yaji damuwa ta qara masa yawa wanda cike da damuwa ya tafi dakin sa.

Imtee kuwa ta jima sosai tana kuka, daga haka ne bacci ya kwashe ta a nan gurin.

Tun daga ranar kowanen su ya shiga qunci  musamman ma Afnan da imtee taqi bashi damar ya fahimtar da ita, kuma kullum dakinta yana a rufe bata fitowa sai taji ya fita, ta fito ta nemi abinda zata ci ta koma.,,,Afnan kuwa dole ya koma cin abinci a gurin su umma,umma kuwa duk a tunanin ta  tsufan ciki ne yasa Imtihal ta daina girka abinci shiyasa a duk lokacin da Afnan yaje cin abinci sai ta sakawa imtee nata a kula tace ya kai mata, shiko sai dai ya kaiwa Baba mai gadi sbd yasan ko ya kai mata baza ta saurare shi ba bare ta kar6i abincin.
              *****
Lokaci ya tafi yayinda cikin Imtee ya qara girma sosai har bata iya doguwar tafiya wanda ko abinci da qyar take iya dafawa.

Afnan kuwa kullum  damuwar sa sai qaruwa take sbd har yanzu imtee bata kulashi shiyasa duk ya bi ya rame,ya zamo abin tausayi.

        **********

A 6angaren Hajiya hasina kuwa tunda kamal ya farfado ba abinda yake furtawa face Imtihal!shiyasa ciwon yaqi ci yaqi cinyewa sbd yaqi ya fitar da abinda ke sa zuciyar sa damuwa, sae qara saka son Imtihal yake a ransa Wanda hakan yasa  nadarmar hajiya hasina ta qaru har ma wani lokaci ta tasa kamal gaba tana ta kuka har dai idan ta tuna cewa yarinyar da tasa a jefar ce  danta ke mutuwar so har ya kamu da ciwon zuciya mai tsanani,wanda abin sai qaruwa yake,kuma tasan Imtihal ta riga ta masa nisa, shiyasa taji gabadaya duniya tayi mata zafi.

Ga shi kuma tsofon mijinta idan yana nan ko dakin baya bari ta xauna bare taje kusa da kamal sbd a cewar baqin halin ta ne da kamal ya kwaso ya kaishi ga hakan,sbd yaji labarin duk muguntar da kamal yayi har takai ga aka rufe shi a cell.

Su imtee kuwa cikinta har ya shiga wata na goma, amma bata haifu ba sai wani  irin nauyi da take jin cikin na qarawa.
      
    5:00pm

Zaune take a kici tana yanka ku6ewa Afnan ya shigo da sallamar sa ta amsa sallamar ba tare da ta dago ta kalle shi ba.

Cikin muryar lallashi Afnan ya shiga yi mata magana,sai dai kamar bada ita yakeyi ba sai yankar ku6ewarta da ta sama gaba,haka ya qaraci zancen sa har ya gaji yayi shiru yana kallonta,can ya fita yayinda ta gama yanka ku6ewar ta ta shi dmn taje ta duba miyar da ta dora,nan slice daya na ku6ewa ya fadi kan tiles ba tare da ta sani ba har ma ta dora qafar ta akai, ta tafi haka sae kawai sul6i ya jata ,tayi baya ta fadi da qarfin tsiyà wanda hakan yasa ta saki qara sosai,  Afnan kuwa har yaje falo ya zauna yaji ihun ta,,yazo da gudu ya same ta kwance ta riqe ciki sai faman ihu take tana juyi,kan kace me jini ya shiga fitowa ta qasan ta, ai kuwa Afnan ya rikice sosai ya dauke ta a rikice yaje ya saka ta a mota ya fice da ita asibiti.

IMTIHAL (COMPLETED) .Where stories live. Discover now