54

2.6K 163 0
                                    

🔺5⃣4⃣🔺
Imtihal ganin bai ce da ita komai ba ta jefar da pic din tabar dakin cikin sauri har tana hadawa da gudu,,tana shiga dakin ta ta fada ruf da ciki kan bed tare da fashewa da kuka,yayinda Afnan ya shigo dakin ya hau kan bed din kafin yayi wani  abu Imtihal tayi saurin safka daga kan bed din, Afnan yace "my imtee ki tsaya mana kiji, da ganin pic sai kuka,cike da shagwa6a tace "ba dole  ba tunda na tambaye ka pic din waye kamin shiru wanda hakan ya nuna min da akwai wani  abu tsakanin ka da ita,no my imtee ni ba wani  abu tsakani na da ita,
asali ma ban san meye a cikin envelope in ba,
saqo ne fa kika bude,
haka kawai baki san na waye ba, shiyasa nayi mamaki har na kasa cewa da ke komai,
ganin kina qoqarin jama kanki abinda bai ganoki ba..
...Allah ni ban yarda da zancen nan ba uhm uhm...cikin kuka ta nufi hanyar fita daga dakin, Afnan ya shiga kiranta yana bata haquri amma taqi ta tsaya sai da yayi mata magana cikin kakkausar murya yace "imtee kar ki fita daga cikiñ dakin nan!
ta tsaya cak tare da fasa bude qofar dakin,ta jingina a jinkin qofa tana mai ci gaba da kuka,cike da lallashi Afnan ke mata magana har ya qaraso kusa da ita,cikin hikima ya samu ya rungumota jikinsa duk da zillewar da take,yace my imtee baki yarda da abinda nace bane?ba ta iya ce masa komai ba face  cusa fuskar ta da tayi a qirjin sa ta sake fashewa da wani  sabon kuka, a cikin kuka ne take cewa yaya Afnan to idan har da gaske kake baka da alaqa da ita to ka fitar da pic din a gidan nan,sbd bana son sake ganin sa,dagota yayi yana share mata hawaye yace "abinda kike so kenan,ta gyada masa kai tana mai qara share hawayenta,ok zo muje ya fadi hakan ne tare da riqo hannunta suka tafi dakin shi,yasa hannu ya dauki pic ya mayar dashi a envelope,downstairs suka sauko ya kira Baba mai gadi ya miqa masa envelope din yace dashi don Allah baba ina son ka qona min photon nan ka kuma tattara kasa a shara,yana gama fada Baba mai gadi ya kar6a ya fice.

Afnan ya sauke ajiyar xuciya yaje kan kujera ya zauna tare da jinginawa,
yana kallon Imtihal da tayi tsaye tana kallon shi wacce da ganin ta kasan akwai sauran magana a tattare da ita,
Afnan yace zo mana my imtee, ba musu  taje ta kwanta kan jikinsa,ya shiga shafa bayanta a hankali yana tunanin yanda zasu kwashe da ita idan taji zance aurensa, ba irin abinda ma yafi tayar mai da hankali irin yanda ta aje mishi kuka akan photo kawai, to ina taga yarinyar ta shigo gidan...imtee tace yaya Afnan to meyasa ka qona saqon mutane?sbd mai shi baya buqatar photon, kwata kwata photon baya da wani  amfani a gareshi wanda da na qona da kar na qona duk d'aya mamaci ya karye, to meyasa baya buqatar photon aka bayar akai mishi? ni ma ban sani ba, to yaya Afnan .... ya lakato hancinta  yace"my imtee tambaya sai kace er jarida, cike da murmushi ta kalle shi tace yi haquri na daina, lumshe idonsa yayi yana ci gaba da shafa bayanta daga haka sukayi shiru yayinda yaji imtee ta lafe a jikin sa sosai,hakan ya bashi damar fahimtar tayi bacci.

Daukar ta yayi suka fice daki shima ya biye mata suka shiga baccin rana.

Basu suka tashi ba sai
guraren sallar zuhur sae da sukayi wanka sannan sukayi sallah, imtee taje ta dafa musu abu mai sauqi dafuwa sbd koda sukayi bacci bata girka musu na rana ba,sukayi zaune suna cin abincin su cikin jin dadi da kwanciyar hankali.

Da dare guraren qarfe tara ta fito daga wanka ta samu Afnan zaune akan bed din ta,ya bita da wani  mayataccen kallo yayinda imtee tayi saurin kauda idonta hade da dan guntun murmushi tare da duqar da kanta kamar mai jin kunya,sbd a duk lokacinda ya mata wannan kallon tasan buqatar sa, wacce yana kwanaki bai nemi hakan ba,amma a duk lokacinda ya nema abun ba sauqi.

zama tayi kan mirror tana shafe jikin ta da turarukka ta ko wace kusurwa,Afnan ne ya taso ya rungumota ta baya yakai  hannunsa tare da yaye towel din ta ya shafo qasan cikin ta yace"
my imtee babyn mu bai fara girma ba har yanzu?kai yaya Afnan wa yace ma ya isa fara girma, my imtee na qagu naga girman cikin nan dmn nasan ba qaramin kyau zai miki ba, kuma ni bana son ki koma gida idan kika haifu na fiso ki zauna anan mu raini babyn mu a tare, shiyasa ma kika ga na bude dayan dakin da nace ma Abba kar a gyara,yau na sa aka share shi min tsaf sbd gobe inshaAllah zan fara saka kayan babyn mu a ciki, wanda tunda naje England na fara siyo wasu kayan ban sanar da ke ba"Allah yaya Afnan!Allah kuwa,tayi murmushi cike da jin dadi, ta shafo cikinta tace "my child kaji daddy ya fara maka siyayya don haka se kayi ka girma ka fito dmn ka ganewa idon ka abinda dadynka ya saya maka wanda nasan zakayi farin ciki ba kadan ba,dmn dadynka ya iya siyayya sosoi,tana gama fada ta juyo cike da murmushi ta kalli Afnan da tun dazu shima murmushin yake,ya jawo hannunta yace "my imtee xo muje dakina...
kayan bacci fa? ba sai kin saka ba.

Suna isa dakin shi ya dauke ta cak sai kan bed,yayi kwance kan jikinta ya lafe a qirjinta kamar  jinjirin da zai sha mamma,a hankali ya shiga zare towel din jikinta yayinda ita ma ta kai hannu tana taya sa cire kayan jikinsa wanda me and Nafee muka bar dakin dmn gujewa ganin abinda yafi qarfin mu.
 
Da asuba suna gama  sallah suka koma bacci basu yi nisa da bacci ba aka shiga danna door bell,
a hankali Afnan ya tashi cike da jin bacci ya nufi downstairs tare da bude qofa,Baba mai gadi ne ya gani,
sai da suka gaisa ne yake cewa da Afnan Alhj yace yayi ta kiranka a waya baka daga ba shine ya kira a tawa wayar yace na sanar da kai ka same sa a asibiti hajiya ce ba lafiya.

IMTIHAL (COMPLETED) .Where stories live. Discover now