59&60

3K 169 4
                                    

🔺59 &60🔺
Tare da saurin kar6e zoben da yake miqa mata,yayinda Abba ya fito ta koma bayan sa ta 6uya tace"Abba ce ya fitar mana da gida shi mugu ne allura yake ma mutum ta qarfin tsiya,yace"maminah ba allura zai miki ba koma daga ciki kinji, ba musu ta koma sae yi take tana kallon doctor mansur a tsorace.

Abba yace "kaga yanda abun nata yake ko,inace za'a sami maganin da zata riqa sha ko abin zai rage, eh to zan bincika inshaAllah idan an samu sai nazo mata dashi gobe, sannan ga wadanan magungunan sae a fara bata, Abba ya kar6a tare da miqa masa kudi masu yawa har ma sunfi kudin  maganin, Dr mansur ya kar6a yayi godiya ya fice.

Da safe koda kowa ya farka ya sami Imtihal zaune a tsakiyar gado sai wasa take da zobe,.
     Umma da suhaila sai kallonta suke cikin tausayi.
Indo mai aiki ce ta shigo bayan kowa ya gama sallah ta kawo ma Imtihal abinci kasancewar tun jiya taqi taci komai ,ba yanda ba'a yi da ita ba amma taqi ci, ko yanzu kuwa haka abin ya kasance ba yanda aka iya dole aka ajiye sbd da an matsa mata kwa6ar da abinci take.

Guraren qarfe goma Islam ta shigo gidan ita da suraj kasancewar sai yau sukaji rasuwar Afnan,wanda mutuwar ba Islam kadai ta girgiza ba har da suraj.
Koda suka shiga sun samu Abba ya tasa Imtihal gaba dmn taci abinci amma ko kallon abinci bata yi ba bare a sa ran zata ci.

Cike da ladabi suka zauna a qasa tare da gaida su Abba sannan suka musu gaisuwa.

Basu wani  jima ba Abba da suraj suka tashi suka tafi  gurin zaman kar6ar gaisuwa.

Yayinda islam ta tashi a hankali taje kusa da Imtihal ta zauna tana kallon yanda take wasa da zobe wanda aikin kenan.

Islam ta share hawayen da suka zubo mata ta dauko plate din abincin da aka ajiye ma Imtihal, ta debo abincin a spoon ta kai a bakin Imtihal,Imtihal  ta dago tana kallon Islam da tun shigowar su sai yanzu ne ta kalle ta, Imtihal tayi murmushi tare da girgiza kanta tace"nifa yaya Afnan nake jira ya dawo muci abinci"islam tace kiyi haquri kici kinji.... nifa bazan ci ba sai idan yaya  Afnan dawo.

islam
tayi shiru tana kallon imtihal kamar mai wani  nazari "tace ai kuwa idan baki ci abinci ba bazai zoba, kuma ko yazo zaiyi fishi dake tunda kika bar babyn sa da yunwa,da mamaki Imtihal ta kalli Islam tace"baby?sae kuma tayi dariya ta girgiza kanta,ta bugo cikin ta tare da fadin, au baki san cewa fishi mukeyi  nida baby ba sbd ya tafi ya barmu shiyasa baza muci abinci ba har sai ya dawo,Islam tace to ai shima yana can yana fishi dake kan kinqi kici abinci, shiyasa ma bazai dawo ba..... Imtihal tayi saurin kallon Islam cikin muryar kuka tace ni bana son yayi fishi dani kuma ina son ya dawo, ok to kici abinci kinji,Imtihal ta kalli Islam tare da gyada mata kai,yayinda Islam ta kai mata abinci a baki,Imtihal kuwa ta shiga kar6ar abincin tana ci,  har ta qoshi sannan ta bata ruwa tasha,Imtihal tayi dariya cike da jin dadi tace"Islam ni yau bazan ma yi bacci ba, zanyi ta jiran shi har sai ya dawo tunda kince min idan naci abinci zai dawo,no kiyi baccin ki kawai...um um ni bazan yi bacci ba  sae na ganshi,kuma idan yaji ma bai zo zanje na same sa har inda yake, islam ta girgiza kanta tare saurin share hawayen da suka zubo mata, Imtihal tace"lah wai  kuka  kike yi  kin dauka da wasa nake Allah da gaske nake gaya miki.

Yinin ranar haka Islam take ta ma Imtihal wayo sannan take cin abinci,
     Da dare kuwa maganin bacci aka bata sannan aka samu tayi bacci.
    

Bayan kwana biyar da faruwar hakan,

Gurare qarfe 7:00pm Imtihal ce ta tasa umma gaba tana mata kuka yayinda take cewa"ni umma har yanzu yaya Afnan bai dawo ba bayan duk abincin da nake ta ci kullum"ki qara haquri dai kinji, ta langwa6ar da kai tana kallon umma tace"ko dai sai na tafi na dubo shi idan ba wani  abu ke damunsa ba"a'a ba sai kinje ba... To ni kullum sai ace min idan naci abinci zai zo amma har yanzu bai dawo ba ni gaskiya na gaji da jiran shi haka,kici gaba da haquri kinji"
Imtihal kallon umma kawai tayi tana fadin wasu maganganu ciki ciki da ba'a jin me take fada.

IMTIHAL (COMPLETED) .Where stories live. Discover now