74

1.9K 155 0
                                    

🔺7⃣4⃣🔺
Cike da damuwa taje ta zauna kan bed tana nadamar abubuwan da ta mishi,yayinda idanunta suka ciko tap da qwallah har suna qoqarin zubowa taji sallamar Nusaiba tayi saurin dakatar da zubowar su hade da qirqiro dan guntun murmushi kafin take amsa sallamar.

Nusaiba ta ajiye kayan da ke hannun ta tare da zaunawa kusa da Imtihal  tace "Anti gashi inji pharmacist kabeer  yace a bawa jarirai, sosai Imtihal ta nuna farin cikin ta tare da bude kayan,  turarukka ne masu kyau na jarirai da kuma tsadaddin tufafi set bibbiyu,imtee tace amma sun gode sosai,wai yaushe ne za'ayi tambaya? um to tukuna Abba bai gama binciken da yake akan sa ba amma ya bashi damar ya riqa zowa muna dan gaisawa shine yau ya samu yazo har ma yake cewa ayi haquri ya makara bai zo ganin jarirai ba,to gashi kuwa yaya Afnan ya fità dasu? eh ya gansu a gurin yaya Afnan, to kimana godiya sosai idan kika koma,ai har ya fice,da wuri haka? Eh dama ya dan jima kafin fitar yaya Afnan kuma anty ni ban cika son jimawar nan ana ta fira ba, dmn tun ana fadar abinda ya dace har azo ana fadin abinda bashi bane, duk da cewa pharmacist kabeer kamar baya daya daga cikin iren iren en iska samarin nan, musamman ma dana ga Abba ya bashi damar  ci gaba da zuwa muna gaisawa,,,haka ne kuma kinyi tunani.

Daga haka Nusaiba ta tashi zata fice Imtihal tace ki dauki kayan ki kai ma umma ta gani,tace to tare da daukar kayan ta fice.

Yayinda imtee ta shiga tunanin yanda zata shawo kan Afnan har ya saurare ta.

         ********** 

A 6angaren su kamal kuwa sae abinda ya qaru,
shiyasa mahaifin sa ya yanke  shawarar  ya dauke dansa ya tafi dashi qasar India ba tare da Hajiya hasina tasan abinda ake ciki ba sai da ta shigo dakin ne taga ba kowa hakan yasa ta tambaya aka sanar da ita.
   Bata ji dadi ba ko kadan na rashin sanar da ita da bai yi ba,sai kuma ta koma tunanin yanda zata tunkari dangin ta sbd tuna irin wulaqancin da ta musu kasancewar  dangin ta talakawa ne sosai,kuma koda ta taso iyayen ta sun rasu a hanun danginta ta taso, kuma duk cikin dangin su ita  kadai ce ta auri mai kudi shiyasa take wulaqan ta su har abin ba kyan gani,wanda a lokacin tsofon mijinta ne take aure wato mahaifin kamal kuma shima a cikin danginsu shine mai kudi hakan yasa ta hada har da danginsa tana yi ma wulaqanci har ma iyayensa bata ragawa, amma shi da'a take masa sosai har baya yarda da abinda ake cewa tana yima iyayensa, sai da Allah ya nuna masa wanda haka ne sanadiyar rabuwar sa da ita.

Kuma koda ya sake ta duk tana da  arziqinta shiyasa da ta koma gurin dangin ta ba ta rage wulaqancin da take musu ba har tayi aure na biyu wanda tun da tayi auren bata ta6a leqa su ba ko sau daya.

Da tunanin haka ne ta fita  daga cikin asibiti.

A 6angaren imtee kuwa har ran suna bata samu shawo kan Afnan ba dmn duk ya shigo gidan fuskar nan tashi a daure  take da har bata san ta yanda zata iya tunkarar shi ta mishi magana ba.

Gashi yau suna tana buqatar tayi magana dashi amma hakan ya gagare ta,shi kuwa  komai yake buqata sai dai ya tambayi Islam ko Nusaiba,ya maida Imtihal tamkar ma bai san waye ita ba.

Yara sunci sunan Abban Afnan da Abban Imtihal wato(Hamis da Basheer) yayinda ake kiran yaran da Aasim da Aasif.

Jama'a sun taru sosai gwanin ban sha'awa abin ba'a cewa komai, en uwa da abokan arziki ba wanda bai zo ba.


Sai dai Imtihal jin dadin ta ragagge ne sbd fishin da Afnan keyi da ita amma da aka zo photo kya rantse ba komai tsakanin su yanda Afnan ya sake yana jan Imtihal ana musu hotuna suda 'ya'yansu Aasim da Aasif,hakan yasa Imtihal ta sake sosai har tana jin dadi dmn ta dauka cewa ya daina fishin da yake da ita.

Bayan biki ya watse da kwana biyu.

Da dare Imtihal na zaune tana riqe da Asif yayinda Asim ke kwance kan bed yana bacci ta jawo wayarta dmn ta kira Afnan sai dai koda ta kira layukan sa a kashe suke.

Zeenat ce ta shigo dakin riqe da envelope tace"Aunty gashi tun jiya da dare yaya Afnan ya bani yace na baki se na manta  ban baki ba,sai yau da safe na tuna,imtee tace jiya da dare  yaya Afnan ya shigo gidan nan?eh mana Aunty kinsan tafiya zai yi kuma yace zai jima kafin yake dawowa shiyasa yazo ma su Abba da umma ban kwana to a lokacin ne yace mu dauko masa Asif da Asim nida zara har muka zo muka same ki kina shan tea,,,amma shine baku sanar dani inda zaku kai su ba, Aunty na dauka cewa kinsan da zuwan sa ai, ok naji yaushe ne ya baki saqon da shigowar sa ne ko kuwa sai da zai tafi?sai da zai tafi ne dmn har ma ya tada motar sa ya kira ni ya bani yace na baki.

Imtihal tayi shiru yayinda zeenat ta tashi ta fita daga dakin.

Shirun da tayi ne take cewa a ranta yanzu shine yaya Afnan zai yi tafiya ko ya sanar dani gashi kuma zai jima sosai, wato kenan ashe bai daina fishin da yake dani ba,,,hawaye ne suka zubo mata zar har suna sauka kan envelope yayinda ta bude envelope din a hankali tare da zaro abinda ke ciki.

IMTIHAL (COMPLETED) .Where stories live. Discover now