K'arshen makirci page. 1

802 40 2
                                    

*ƘARSHEN MAKIRCI*
_(Nadama)_

11/03/2019

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 1

*Ƙagaggen labari ne, in kinga yayi iri ɗaya da labarinki ko wata 'yar uwarki to arashi ne, amma banyi ko dan kowa ba sai dan in isar da saƙo da faɗakarwa cikin nishaɗi.*

*Gargaɗi*
_Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a mayar mini da shi Audio a ɗaura min shi a kafar youtube channel ko website ko facebook ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, da fatan za a kiyaye_

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

SULEJA

A Ranar hutun ƙarshen mako Asabar da yammacin La'asar a kan hanyar babban titin Abuja, Hadari ne kewaye a sararin samaniya baƙinƙirin, garin yayi duhu sosai sai walk'iya da rugugin haɗuwar hadari ke tashi. Wasu Motoci ne guda biyu jere bisa kan titi suna tsula gudu tamkar zasu tashi sama, sai suka yi ratse zuwa cikin wani jeji mai madai-daiciyar hanya a Suleja kafin a k'arasa garin Abuja, Motocin baƙaƙe wuluk tare da gilas ɗinsu, baka iya tantance Mutanan da suke ciki, haka suka nausa cikin wannan jeji mai duhuwa da yawan bishiyoyin itatuwa, sai da suka shiga ciki sosai kafin suka tsaya. Mutanan dake cikin motar farko duk suka fito waje, wasu Maza jibga-jibga baƙaƙe har su uku suka bayyana, fuskokinsu a murtuke babu alamar Annuri a tare dasu, ɗayan Motar kuma Mutum biyu ne suka bayyana, suka haɗu su biyar, Alhaji Nura, Gamzaki, Ukasha, Barde, Usama. ɗaya daga ciki mai suna Gamzaki yace

"Alhaji wannan jeji ne mai ɗauke da gonakin Mutane daga ciki, daga Farkon shiga kuma zuwa nan gaba kaɗan Mallakin Gomnati ne, kaga wancen ramin shine jiya muka zo muka haƙa shi, Alhaji zamu sanya shi a ciki ne mu mai da ƙasa mu rufe ko kuma zamu barshi ne dan a ji labarin ganin gawarsa?"

Murmushi Alhaji Nura yayi cike da ƙasaita yace

"Gamazaki ko ka manta Abinda muka aikata ɗazun a garin Kano? Ai tunda mun kashe shi bana son a samu labarin ganin gawarsa saboda kar 'yan sanda su samu damar yin bincike, koda nasan akwai tazara tsakanin nan zuwa Kano, amma saboda tsaro kawai ku sashi a ramin ku mai da ƙasa ku rufe, daga yau mun rufe shafinsa"

Sai duk suka bushe da wani wawan dariya mai cike da amo da shaƙiyanci.

Baba Habu yana tafe bisa kan hanyarsa na komawa gida daga Gonarsa, cikin sauri yake tafiyar kafin ruwar sama ya sauka, a dai-dai lokacin da yaji shigowar wa'innan Motocin cikin jejin, cikin kiɗima da tsoro ya nima mafaka ya ɓoye, ya aje kayan Nomansa ya haye saman bishiyar Mangwaro ya laɓe tare da zuba musu ido. Duk abinda suke yi akan idonsa a lokacin da suka fito suka fara magana sam baya jin abinda suke faɗa, sai dariyarsu daya hautsina masa ciki saboda tsananin tsoro, duk tunaninsa basu wuce 'yan Fashi ba ko Matsafa, sai ya ƙanƙame jikinsa ya jawo wani reshe na bishiyar ya kare kansa dan kar su ganshi. Wani ɗumi ne yaji yana bin jikinsa da sauri ya taɓa wandonsa ashe fitsari ya saki saboda firgici.

'Oh ni Habu yau naga ta kaina tsautsayi yasa na fito Gonar nan, sai da Hansatu tace karna fito na huta amma naƙi ji, Allah ka fiddani daga jejin nan lafiya, da alama wa'innan Mutane ba abin Arziki suka zo shukawa ba'

Zancen zuci yayi gumi ya gama wanke masa fuska.

Su Barde suka buɗe bayan boot suka fito da Imran baya motsi kamar matacce duk jini ya gama wanke masa fuska saboda tsananin dukan da suka yi masa a kai, suka kama shi suka jefa cikin ramin da suka haƙa sannan suka sanya ƙasa suka rufe shi.

Nura wanda suka kira da Alhaji yayi Murmushin mugunta wanda babu d'igon Imani a zuciyarsa

"Shikenan labarin ka ya k'are Alhaji Imran Sa'eed ka Mutu su Inna dole a koma Mahaifa ƙasar Chadi, Imran ka zame min ƙarfen ƙafa sai yau na samu nasara akan ka, burina ya cika"

K'ARSHEN MAKIRCI (Nadama)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang