8

139 3 0
                                    


   K'afarta ta fito da ita daga motar duka biyu amma jikinta na cikin motar, kallonsa take tace Idan nayi bacci fa kasan gobe da school kuma early morning zan tafi so kaga dole nayi bacci d wuri
Marairaicewa yafara dan Allah shidai zai kirata Wallahi Idan baiji miryarta ba bazai Iya bacci ba
Dariya ta saki tace kenan da baka bacci?
Inayi amma had'u wata dake tasaka duk nazama wani iri ban iya bacci ko maima fa Sweety Yaya Saleema ban iyawa
Hum to naji zan jira ka, bye fita tai hannun ya d'aga mata sannan yai kiss ya huro mata
Da gudu ta shige tana dariya kunya yabata lallai Deen
Lover gal Mama kinga yadda take murmushi shine ya sauketa fa wacce hira kukayi haka har kike dariya
Hararsa tafara kafin tazo ta zauna tace shi munafuki wutar sa daban, kasamin ido arayuwa komai nayi akan Idon ka
Wallahi kafita idona na rufe ka fita hancina kada na fatako. Waih lallai Yaya Saleema badan niba kyayi dariyar yau nafasan komai Wallahi shiru nake kawai nake
Kai yimana shiru, magananne kawai
Mama ce tace kai Sultan rabu da ita Saleema Allah yabada sa'a Allah yasa alkhairi matuqa nayi murna Allah ya tabbatar da alkhairi Deen Yaro mai hankali
Kanta sunkeye tace Ameen Mama
Lah kyabari nace Ameen d'in mana, amma ke kika fad'a zamani
Kallon sa kawai ta mik'e ta haye sama
Sultan yace Mama amma dai Idan komai ya daidaita lokaci kad'an za'asaka koh?
To kabari magana tayi girma zumud'i
A can sama wanka da alwala tai, Magreeb da Isha'i tayi kana tai shafa'i da wutr Al Qur'an ta janyo tafara karatun ta cikin nutsuwa gwanin sha'awa da dad'in saurara
Sautun wak'ar Nincy ajram ke tashi cikin sautin wak'ar Killina killina, killina nal'ab killina nafram, Addu'a taimaza ta shafa ta d'auka
"Hello Yaya Saleema nazata kinyi bacci?
Banyiba ko shirin baccin ban fara ba ma
Ok ya kike ya kika k'arasa gida kinci abinci kuwa?
A'a zanci amma anjima kad'an na idar da Sallah ne yanzu, saika kiranka
Tom naji bara nabarki kici abinci saina k'ara bugowa,amma bazan bar matata da yunwa ba
Itadai batada da tacewa Illa to. qasa ta sauka macaroni ce da kifi haka ta d'ebo har zata haye sama tajiyo maganar Abba tsayawa tai harya shigo
Sannu da zuwa Abba? Yauwa yace amma maganar sa kamar yana cikin b'acin rai zama yai Sultan ma yayi masa sannu
Kwafa yayi yace Wallahi Alhaji Sani dani yake zancen mutum kwatakwata bashida burin da ya wuce yaga ana rigima ga bak'in ciki da hassada komai ya had'a kai amma bai mori hali ba da girman sa Mts
Mama ce tace maikuma yayi kullum naga yanzu saikazo kana maganar sa?
Eh Wallahi Maman yara wai akan kwangilar da Alhaji Raheem ya samu wadda a qalla zata kai kimanin 50.5 shine sai wani zuwa yake yana cewa naje nima abani haka kawai
Nima wataran ina samun haka ko wadda ta fita, nazata shine yasamamun kwangilar Titin wuju wuju kuma da alkhairin da aka samu kaf nabiyawa yaran mu Hajji
Alhaji Raheem wana nad'aukeshi d'an uwa kuma Shege zai had'a mu ai kaca kaca namasa
Aikam gwara haka, tsinannne zai had'a ka fad'a da Abban Deen abinda ma zumunci zai k'ara d'in kuwa Imam da Saleema suna son juna
Kai dan Allah amma ba labari ko shiyasa naga yau suna tare basu zauna cikin mu ba?
Sultan ne yace eh Abba suna can suna love, sun barku dasu Aunty Ummi
Albarka ya sanya abun yace Lallai zumunci zaiqara habb'aka Allah ya kaimu lokacin
Haka Mama taitaimasa hira mai dad'i harya ware yamanta da wani Alhaji Sani
Itama Saleema hiranta take sha bayan sallamar da sukayi da iyayenta
Deen sai asirin zuciyar sa yake bajemata Ita kanta tarasa bakin magana Lallai dama ana irin wannan son?
Gashi kin gani wata zuciyar ta tace mata daga gefe
Yaya Saleema Plx ki gayan kina sona Allah ke nake jira cikina ya d'uri ruwa Idan baki gayan amsata ban Iya bacci kinji Ruhee gayan
Deen kenan to rife Idon ka Indai kanason jin amsar ka
Lah bafa kya ganina duk kunyar ce haka, naji na rufe har pillow na d'ora akai gayan inajin ki
I love u ! What Yaya Saleema kene kika fad'i k'ara naji
Nak'i wayon aikaji, hamdala yai wajan mai bayarwa da hanawa mai saka k'unci lokaci d'aya mai yayeshi cikin sakanni
Rasa bakin magana yai sai dariya, tana jinsa itama dariyar take tanajin kamar baya su a duniyar gani take matsalanta ya k'are tunda sun zamo abu guda suna son juna
Yaya Saleema"na'am
Nagode nagode Allah yabamu yara nagari Allah yabani ikon kula dake Allah yayimiki albarka
Ameen tace daga nan aka dasa hira kowa yana gayawa kowa kalaman k'aunar basu ankaraba saijin kiran assaltu sukai
Dariya yai yace nayi laifi Yaya Saleema nada lecture kuma na tsaidata amma Kada ki damu ni zanzo na kaiki maza yi bacci kafin akira na biyu kinji
Tom kaima kayi baccin kaji? Zanyi amma saina bari nafara jin saukar sanyayyen numfashin Yaya Saleema Idan tana bacci
Plx ka kwanta kaji a shagwab'e tayi maganar, wani irin abu yaji ajikinsa Yaya Saleema ta Iya magana haka Lallai ya more sosai
Ba yadda tai numfashi ta aje a hankali tamasa sallama wayar ta ajiye kusa da ita shiru sukai a haka shugaban b'arayi ya sace ta wato bacci
Waye Alhaji Sani
@ut@r h@jiy@ ce

SHI NAKE SOHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin