27

64 1 0
                                    


    Ranar d'aurin aure ****
Tunda safe Abban Saleema yaketa zirga zirga gida ya cika da jama'a, Idan ka duba kowa murna yake yi, Maman Saleema itama bakin ta har kunne.
   Su sultan ba zama anata zirga zirgar inda zasuyi walima suga waje ya had'u, Abba har tambayar sa yayi cewa ina zaifita da safe haka bayan wanka yakamata yayi shidasu Yaya Na'eem?
    Magana yai masa akan yanason zuwa karb'a takalmin sane, ah to ainaga baka shirya ba, haka ya fice yana dariya qasa qasa.
   Saleema ana d'aki wanka ta fito mai make up ce zaune kan gadon ta, tana jiran ta, duk ta rame abin tausayi, ga jiri dake d'ibarta, a haka dai take k'arfin halin yin wasu abubuwan.
   Qawayenta irinsu STYLICH dasu Anker Zahra Bukar ana zaune anata shafta, ga Faty Afreen da Basmah ga Ayusha Mohd, kai da yawa dai, tun Asubah suka zo, murna suke taya ta. Saboda kowa yasan soyayyar Deen da Saleema ace kuma ba zasuyi aure ba, shiyasa alokacin da sukaji zancen fasawa kowa ya jiman tamata.
    Deen shima yanacan su Sultan da Shehu Halifan Malam M wabeel, Malam kilu Man Nass Isjerp and the rest dukkan su, suma shiri suke anayi ana hira mai dad'i
   Yaran gidan su Deen duk sunzo, jikokin gidan suma da yawa, dangi anata raha, Mom tasa murna takeyi d'anta zaisamu abinda yake so.
   Alhaji Sani anacan anata murna za'ayi auran d'ansa dukiya suke facaka da ita, kamar me, anyi dinner wajan uku duk amarya na gadon Asibiti.
    9:30 dai dai kowa kagani yaci kwalliya, Deen milk shadda yasaka sai hula baqa da takalmi, gashinsa yayi kwance luff a bayan sa, sai k'amshi takeyi, Ango sak ,fuskarsa sai annuri take fiddawa, suma abokansa a daran akayimusu d'inki iri daya yadine sukai Ash colour suma hula bak'a, abin saiyayi tsari.
   A gida suka zauna Sultan da Shehu sune kad'ai suka fito saboda kada Abba yagansu ya fuskanci wani abu.
   Mutane sun fara taruwa gida ya cika, k'ofar gida ma haka, saijiran lokaci. Abba ma yayi kyau kaya iri daya sukai da Alhaji Sani, su kuma Farar shadda ce sai aiki ruwan kwai, Abban Deen shima Ita yayi saboda Sultan yakai d'in kin, shiyasa yabada komai ayi uku harta takalmi iri daya zasu saka, amma fa Abban Saleema baisani ba.
    10:00 dangin Ango suka zo, Alhaji Sani shida tawagar abokan sa, da walliyin daya nad'a, sai gaisawa akeyi, yaran gidan su Deen duk suna wajan ana karbar bak'i dasu.
    Zuwan Abban Deen shi yasaka hankalin Alhaji Sani tashi, ganin yadda ya fito mutum mai kwarjini da kamala, jama'ar sai aka koma wajan sa, hannu kawai yake mik'awa ga marok'a sukai masa caa, baibi takan Abban Saleema ba, illa abokansa dayake ta tasu.
    Limamin ne yace kowa ya motso, waliyin Ango yazo na amarya ma yazo, haka duk sukai gaba, already su Deen sunzo suna wajan amma cikin motocin su, hankalin sa a tashe Idan yaga lokaci yana tafiya.
  Saleema itama d'aki tasamu ta zauna, sai zarya takeyi, tanajiran taga yadda Allah zaiyi da ita.
    Addu'a aka fara, sannan akayi tambayoyi bisa al'ada tsakanin waliyan biyu, kowa ya aminta da abinda kowa yace, sannan maid'aurawa ya d'aura akan sadaki 50k bisa sunna da koyarwar ma'aiki saw.
   Marok'i ne ya busa sarewa, kana aka furta da BABBAR murya cewa *An d'aura auren Saleema Abdulazeez da Imam Deen Raheem sadaki lakadan ba ajalan ba bisa yardar waliyin Ango da na amarya.
    Ihu Deen yasaka acikin motar baibari ma angama fad'a ba, ya fincike ya bud'e motar ya fito, Sultan kam kuka yasaka dama zaiga wannan ranar lallai Allah mai iko.
   Alhaji Sani zagi ya k'unduma da sauri ya cakumi wuyan abokin nasa, munafuki da d'ana za'a d'aura amma kuka ha'inceni to dole ku warware abawa Sagir matarsa.
  Aikin gama ya gama, mutane sai kokon to suke ko ya haukace?, Abban Saleema kam daskarewa yayi a wajan, illa wani mugun kallo dayake jefawa yayan sa

    Saleema tana cikin gida itama da gudu da fito jin ana gud'a ana had'a sunan ta dana Deen matsayin Ango da amarya, hoo tamanta da jikin ta sai tsalle da murna itada Mamanta rungume juna sukai sunata murna hawayen dad'i ne idon Yaya Na'eem da matarsa lokacin dasukaga irin farin cikin da kanwarsa da Mahaifiyar sa suke ciki.
    Sultan acan kasa had'a ido yayi da Abban sa, saboda yasan tabbas dashi aka had'a yin komai.
   Abban Deen bakinsa har kunne lokacin dayaga yadda Alhaji Sani yake hauka yana kururuwa, shi dariya abin yabashi ma. Tafiya yai wajan Abban Saleema hannu ya mik'amasa, bashi yayi amma fuskar sa a cunkushe ba alamar annuri cikinta. Tabbas saiya rama abinda akayi masa, 'yarsa akama a d'aura mata aure da wani bayan ga wanda yace abawa, Huum Idan kunsan wata bakusan wata ba.
    Baice komai ba a wajan, saima k'ok'ari da yayi ya b'oye bacin ransa, kada agani, Alhaji Sani shida Sagir wanda abokai kewa dariya kasa zaman wajan sukai da b'acin rai suka tafi, da kuma burin d'aukan fansa.
    Walima aka tafi harda Abban Saleema wanda Yaya Abbas ya d'auka, saigani yayi anshiga Meena, jama'a kamar me, gashi nan komai birjik kama daga nakan ci harna sha, saiyanzu yayi tunanin yadda yaga kowa ya hak'ura ashe da tsiyar da sika shirya.
  Wajan yayi kyau Deen sai washe baki ake, sultan kam shida Shehu sai tsiya suke masa wai gawa tak'i rami shida Matar tasa.
    Anyi pictures da video coverage, komai yatafi cikin tsari har lokacin tashi yayi kowa yakama gaban sa.
   Suma iyayen mata sunacan ana shagali harda masu kid'an kwarya, gidan su Saleema kam Sa'adu Bori aka kira, harda Ita wajan rawa, ganomin Auta filin rawa sai cashewa suke abin su.
    Maman Deen kasa zama tai saida tazo wajan Maman Saleema nan ma hawayen dad'i suka zubar, ganin yadda kwanaki suke cikin bak'in ciki amma yau sai godiya.
    Haka akayi yini, wajan 6 akazo d'aukan amarya, ansha kuka Maman ta kamar bazasu rabu ba, D'akin Abban ta aka kaita, tana kuka take neman yafiyar sa da afuwar sa, yanajin tausayin yarsa, amma yakasa tausayamata a fili.
    Da kyar ya furta Allah yabada sa'a yanagama fad'a ya shiga d'akin sa.
   Haka aka d'auketa sai gidanta dake Tarauni inda gidan mijinta masoyinta Deen yake.

  Tare da rakiyar 'yan uwanta da k'awayenta da aminan ta, duk d'okin da take saitaji tadena lokacin da taga kowa nashirin tafiya, basu bari Ango yazo ba, jama'ar suka tafi Anker itada da STYLICH aka bari wajanta, suma dai nasiha da fad'a suke mata, akan zamantakewar aure. Kada taga ada yanamata abubuwa tazata haka ne zai d'ore akwai rayuwa Kuma hak'uri shine gaba, tunda d'an Adam ajizi ne, akwai mantuwa.
    Haka suka zauna saiwajan 8 sannan Ango ya shigo shida abokan sa, a parlour suka zauna, basuyi wani shashancin nan ba, abinda ya kasu shi sukai, sai addu'a da akayi ta d'orewar zaman lafiya.
    Sultan harda shi, lokacin da zasu tafi wajan ta yaje hannunta yakama nasiha yayi mata da kuma fad'an ta kula da kanta dakuma shan magani akan lokaci yana kuka tana kuka suka tafi.
  Su STYLICH saida suma suka tab'a kukan, saboda kowa yasan shaquwar su, gashi aure zai raba, haka ya musu rakiya ya dawo.
  @ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now