14

90 5 0
                                    


   Alhaji Abdulazeez kyad'a kai kawai yake yana tuna yadda yanzu d'an Alhaji Raheem yake damawa jiyama wata kwangilar yasamu
Indai haka ne ba shakka maganar Alhaji Sani gaskiya ce, impossible bazai yuyuba dole nad'auki action akan haka
Mik'ewa yayi. yafara had'a kayansa cikin briefcase nasa, Alhaji Sani duk abinda yake yana lura ganin yayi hanyar fita yasaka shi cewa Alhaj yayah?
Ai naga Idan banwa tufkar hanci ba, wankin hula zaikaini ga dare
Gara nafara tun yanzu, nasan yanacen yana zancen banza
Dariyar k'eta yasaki amma azuciyar sa, a fili saiyace ni yanzu banson aga kamar ninake zugaka, ko ace ni nace kabawa d'ana shiyasa banson kayi da garaje
Kai rabu dani sainayi, yana gama fad'a, ya tarkata kayansa ya fice, ko takan Abban Deen baibi ba, wanda yake k'ok'arin fitowa daga masallacin wajan
Allah ya kyauta, shine kad'ai abinda yafito daga bakin Abban Deen ya yi shigewar sa nasa office d'in
Tafiya suke, amma shi gani yake driver'n sam baya gudu, hakan yasa yace yabashi dakansa zai tuk'a, bashi yayi kafin wani lokaci saigasu a gida
Ko sallama baiyi ba, ya shige parlourn, kan kujera ya zauna, yana muzurai da raba Ido
A'a Abban Saleema kaine da wuri haka?, sannu da zuwa lemo da ruwa ta d'akko sai glass cup ta ajiye kan stool ta tsiya yamasa tabashi karb'a yayi, baidireba saidaya shanye
Alhaji lafiya wai naga kwana biyu wani iri nake ganin ka, kuma naga kamar lafiyarka k'alau?
Lafiya ta lou, ina Saleema take?
Suna waje itada Deen, kasan yazama d'an gida Sultan Kuma yazama d'an can tunda su Shehu suka dawo gidan da zama yanzu ganin Sultan yayi wuya
Mts, nifa banson wannan haukar, ke ninarabasu daga yau Kada ya k'ara zuwar mun gida macuta kawai, bani ba Alhaji Raheem ashe duk soyayyar dayake nuna mun k'aryace? Ha'intata zaiyi tabbas yau ko gobe za'amayar musu da kud'in su, kuma takardduna zai bani na gidaje na mugu kawai, ai Wallahi aminta batace haka ba
Alhaji kasan mai kake fad'a kuwa? da hankalin ka, Abban Deen nefa, bawani ba, ko laifi yayimaka bai cancanci wannan tozartawar ba, Kuma yara baku kuka had'a suba, sune suka had'a Kansu
Wani kafirin ne yace maka baya sonka, Wallahi musulmi dai Indai haryasan yadda kuke bazaiyi k'ok'arin da zai had'a ku ba
Ke ! yimun shiru, yarki ko tawa?, dukiyarki ko tawa, to babu wanda ya isa ya hanani abinda nace zanyi, ke inbanda hauka kina ganin d'ansa inda yanzu ya tusashi cikin Manyan mutane shima ana yi dashi, ninawa d'an ko oho
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" wacce irin masiface wannan, ya Allah kakamana d'auki, abinda ba'ayi ana yara ba, saida girma yazo anshiga uku
Kece kika shiga uku, fad'a yake sosai ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, kuka Maman Saleema tasaka da gudu ta haura sama sultan ta kirawo tace yazo gida da sauri
Ina ma gate Mama lafiya, baisaurari maizataceba da sauri ya k'arasa Ita ma ta sakko lokacin
Fad'a masa komai tayi na abinda yafada, shima salati yafara yace Abba Idan ma wani abu ya had'aku kuyi iyaku amma yara kada kusaka damu, Saleema da Deen ku barsu basuda laifi cikin abinda Ku keyi
Kuma Abba ai bakai yakamata kayi fushi da abinda Deen kesamu ba, Abban sane yakamata yayi fushi da shi, tunda komai yasamu kafin kowa yasani Saleema tasani, hatta kud'in sa Wallahi Mama yana account na Yaya Saleema, bashida mai shawara sai Ita, kenan Iyayensa sune zasuyi fushi akan ya d'auki budurwa ya barsu amma maimakon suyi fushi su abin sha'awa yake basu
Yimun shiru shashasha, tabbas Saleema ba Ita ba Deen, hasalima nayi mata miji nan da Sati uku zan mata aure dashi, nayadda dashi Kuma babu wanda zai kankare magana ta
'Ya ta wace, bata wani ba, saboda haka daga Yau kaima bakai basu, mugwaye kawai
Sultan Namiji ne, amma kuka yasaka Lallai raba Yaya Saleema da Deen kamar raba su da ransu ne
A baya kafin su furtawa junan su Kalmar SO, sun wahala bare yanzu da sukayi sabo, ace z,a'arabasu anso kashe Saleema ne
Wama Abba zaibawa Saleema, wani mara albarkar ne, zai raba wannan had'in, wani mara Imanine ya shiga tsakani iyayen su?
Bashida amsar tambayar sa, illa kansa daya dafe, ganin ba lokaci yasashi fita da sauri baizarce ko'ina ba, sai Lamido crescent gidan su Deen
Bayin Allah su basusan abinda ake ba, suna can suna soyayyar su, tana batason su rabu ganin ya mik'e zai gudu
Dariya yai mata yace Yaya Saleema Allah kinfiya shagwab'a idan ban tafi ba, so kike na kwana?
Eh mana aikaima gidan kune, Idan muna tare banson kace zaka tafi ko muna waya kace to bara nabar ki sainaji haushi
Murmushi yai Yaya Saleema kenan, nafiki jin haushin haka, amma yana iya sai hak'uri
Lallab'ata yayi da kalamai masu dad'i harta ware tadena cuno da baki
Rakoshi tayi, har wajan motarsa, suna tad'in su, da yayi kamar yashiga suyi sallama da Mama amma yace gobe yaje saboda Magreeb tayi
Sallama sukai, suna masu jin farinciki kafin akasin haka yazo
@ut@r h@jiy@ ce

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now