26

50 1 0
                                    


  Gudu me keke napep yakeyi amma ina Deen gani ya keyi kamar bama ya tafiya, hankalin sa a matular tashe yarasa yadda zaiyi kukan ma ya k'are sai dacin zuciya da zafin idanu.
  Yana wannan tunanin ma harsuka k'araso asibitin, kud'i yadebo baisan adadin su ba, ya zuba masa a jiki gani yakeyi kafin yasaka hannu ya amsa kud'in b'ata wani lokaci ne.
    Da hanzari yashiga asibitin, hankali a tashe. Su Yaya Ali da Yaya Abbas yagani sunata zagaye, kafadar su ya dafa, haki yake yana tambayar ina Saleema ya yagansu a haka?, ina Mama d Mom?
    Da hannu suka nunamasa wani d'aki, yana zuwa Abban sa yagani da yaran gidan suna zaune ga Mom nasa a gefe. Shima bin bayan su yai ya zauna  Abbane yafara magana.
   "Wato abinda yasaka nace a zauna ba wani abu bane sabo kowa yasan matakin da muke kai, nayanke shawara nida wan Abban Ku Na'eem, akan a gobe dole shine waliyyin Saleema, wani abokin mu kuma naji shi suka saka waliyin Ango, dashi mukayi magana akan bazai bawa d'an Alhaji Sani ya ya aura ba, saboda sanin halin sa, a gobe kai Deen za'a d'aura aure. Idan yaso suyi masifar su daga baya. Addu'a nasaka ayitayimana akan Allah ya karkato da hankalin Abban ku kanmu.
    Deen kaikuma bance ka gayawa  kowa ba, koda yake kafada ma babu laifi. Saleema tana nan d ranta suma tai. Nasan abinda ya kawoka kenan, muma mun zata ta mutu.
   Maman ta itama suma tai amma anyimata allura rashin bacci, kwanciyar hankali, cin abinci shiyakawo mata haka, addu'ar Ka Saleema take buk'ata, tashi kaje wanccen d'akin kaitake nema, Allah yaimuku albarka.
    Yanxu sai kowa yafara shiri, sultan aje ayi barbing hair, Shehu aje a samowa Deen kayan da zaisa, a yau aje Meena Event a tambayo gobe zamuyi walima a nan.
    Amarya babu abinda zatayi, a gobe kuma zataje gidan ta, taqarasa warkewa acan, wannan maganar tazama sirri tsakani na da kune, amma tun yanzu afara shiri, Na'eem saikaje wajan Abban ku, kanuna yayi haquri komai dakai za'ayi kaga masan wani abin. Tom Abba Alhamdulillah kowa ya tashi yaje, afara nemar sutturar da za'a saka, Hajiya kema kyayiwa telanku magana ko ayiwa Ummi waya a yau taimaza tashiga store tasiyo muku abubuwa keda Bintu.
   Kowa a wajan ka kalleshi yana cike da murna da farin ciki, bakunan su kamar gonar auduga, godiya suke tayi wa Abba harsaida yace ya isa dama shi kallon Alhaji Sani yakeyi yagama shirmen sa, amma Saleema sai Deen.
   Acan d'aki sukansu Doctors din sune suka nemi da a kira musu Deen badan komai ba, sunyi Iya yinsu sunga shine maganin, a yanzu haka daya shiga, dukkan su fitowa sukai a bakin gadon ya zauna yanajin a yau bashida bakin godiya ga mahaifin sa, amma kuma addu'a itace babbar godiyar sa ga Abban sa.
    Sai kuma wajan ubangiji daya nufa zasu zama abu guda shida Saleema, Saleema takusa zama Iyalin sa, zaizama babu shamaki tsakanin sa da kyakyawan lips nata, Salatin Annabi shikuma shine nuna godiyar sa ga ubangiji, sai rik'e auran sa da daraja.
   ******** Some hours later
      Saleema ta farka, hartaji labarin komai da aka shirya, Maman ta itama ta farka hankalin ta ya kwanta da taga 'yarta hartana magana, Iyalan biyu yau kaikace sallah ce a wajan su.
    Tunda Abba suka fita basu dawo ba, sunacan ana cacumar kud'in sa. Deen yakasa ya tsare yana kusa da Saleema minti d'aya biyu yace sannu one love da akwai wani abu, murmushi kawai take masa, jikin ta ba kwari alwala Deen ne yamata ma tana turjewa abarta zata Iya amma ina saida yagama mata tas sannan ya janyo hijab
yasamata dadduma yasamata akan bed d'in yace tayi a haka, jiri ne yake d'iban ta.
   Sultan kam shidai baida walwala harsaiyaga and'aura, shiyasa har yanzu baida kuzari.
    Saleema jiki yayi d'an fyn, koda Abban ta ya dawo murna yayi yace aisaita tafi gida, tunda jiki yayi sauqi, zama yayi yanamata nasiha datayi haquri batace komai ba saboda tasan abin bai tabbata illama hak'uri data bashi akan bijiremasa datayi a baya.
     Deen yana karkashin gado, a nan ya buya dayaji shigowar Abban, haka yace bara ya kira Maman ta azo a tarkata kaya su koma gida.

   Shirin biki sosai akeyi, Yayun Deen mata duk sunzo, kowacce ba zama tafita nemo abubuwan da zasuyi, dangin mom tasa anmusu waya nan suma sukace suna hanya, tunda abin unexpected yazo, dangin Maman Saleema su harsun cika gida ma, Abba sai washe baki yaga kowa ya hakura
    Saleema koda suka koma gida, wayar tace mak'ale suna tad'i da Deen ahaka suka shafe awowi suna hira.
   *Washe gari ranar d'aurin aure*
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOOù les histoires vivent. Découvrez maintenant