12

113 2 0
                                    

One week later
Alhaji Sani lokacin da yaso tafiya Allah baiyi ba, sai a yau ranar laraba ranar sa'a ya d'auki motar sa, sai birnin gwari wajan amintaccen bokan sa
Tafiyar awa hud'u ta kaishi , kafin yafara shiga surk'uk'in dajin da bokan yake. Motar sa ma ajiye ta yayi ya k'arasa da k'afa
Ya tsinanne mai salwanta rayuwar mutane, ya Shege d'an shegiya, Mai bak'in hali mai muni kamar biri, watsewa ta tabbata gareka uban shegu
Wannan shine kirarin danaji Alhaji Sani yayiwa la'antaccen bokansa, da baya da baya ya shiga bukkar tasa
Wata bukkace daga waje k'arama amma cikinta babba ne, zama yai kan wani buzu amma na bak'ar akuya shikuma bokan wanda yana zaune akan kunkuru ne daga shi sai banttai sai wasu layu da guraye nannad'e a jikin sa.
Gashin kansa tsrabar daud'a ya koma fari da ja, idonsa kamar wuta jajawur, juyowa yai ya fuskanci Alhaji Sani kafin ya shek'e da wata irin dariya, kai kace aradu ce ta sauka
Sannun ka da zuwa abokin shaid'an, mai tarwatsa kan jama'a lokaci d'aya kazo a sa'a aljani Durfus yana nan zuwansa kenan, tashi kayi gaisuwa gareshi
Nan Alhaji Sani ba tsoro yatashi yana rawa yana wani sunbatu tsaya haka! akace masa kazo a sa'a zaka sami yadda kake so a wajan Alhaji Abdulazeez amma wajan Alhaji Raheem babu sa'a zakasami tarin dukiya da gidaje wajan sa
Komai kace zaiyi batare da shakka ba, ungu wani ruwa suka bashi da wani k'ulli. wannan maganin kasamu nama kabashi yaci Idan yaci saika d'auki guda d'aya ka tabbata yabawa kare, ruwan kuma kabashi yasha Idan kai haka ka gama dashi da dukiyarsa
Maganarka itace abar bid'a a wajan sa bata kowa ba, zai rabu da kowa da komi sai kai
Jini zaka sadaukar, sannan kabada dubu d'ari wadda za'asallami Durfus da ita
Aljihunsa ya tab'a kud'i yad'ebo baisan adadin suba ya mik'a, kafin yai magana bokan kansa ya b'ace shima tashi yayi yafita da rarrafe har wajan motar sa
(Allahu Akhbar kaji wad'anda Allah ya b'atar kan duniya daba komai cikinta face tarin takaici da k'alubal'e amma har kake tunanin zama, lallai wanda yab'ata, ya b'ata b'ata manisanci. Kowa zuciyarsa k'awa da kyalekyalen duniya lahira ko oho bakai aikin dazakaga kayan alatun ba, Allah kasa mudace)
Cikin farin ciki da murna yatawo hanya yana mai cike da nishad'i burinsa ya kusa cika, zaisami dukiya, kai ya godewa Boka uban shegu
Yau tun safe Deen daya fita wajan aikin sa, bai saurari Saleema da waya ba. Saboda aiki yasha kansa ga masu wajan yau sukazo shiyasa gaba d'aya baya hayyacin sa
Bashi yasami kansa ba, sai wajan 4pm, wayar sa yafara d'akko wa cikin mota, OMG! ba adadi missed call na Saleema
Bugawa yai, no response, dayake yagama da kowa, ba wani abu motarsa kawai ya shiga yakama hanya, a hanya yayita kiranta ko alamar d'agawa ba aiba
Hankalinsa tashe, Allah yasa lafiya, ko fushi tayi? baisani ba
Gidan su ya zarce, da Sultan yagani a zaune a balcony yana karatu, kwala masa kira yayi
K'asa ya kalla, dariya sukai wa juna, daga sama Sultan yace na Saleema bada kanka a sare, yau mutuniyar fushi take da kowa
Ido ya bud'e yace sakko Plx laifinane sakko da sauri, yana dariya ya sakko. Hannu yabashi suka gaisa yace kai Wallahi namata laifi nan yaga yamasa komai
Haba aboki dan wannan shine zata yiwa mutane bore, abinci ma ta k'i ci, ashe hakane mts Allah ya kyauta
Hannunsa yakama suka shiga ciki, daidai nan ta sakko k'asa da k'aton hijab nata
Kallon juna sukai, na yan sakkani, juyar da kanta tai, da saurin sa ya je gunta yace haba Yaya Saleema kiji uzirina mana tsaya kiji. Nak'i saidaka shanyani zaka wani kwaso rub'abben abokin ka kuzo mun
Lah nine roting, amma Yaya Saleema kin yanken, mijin ki shine ai
"Yaro kasan yafika komai, dama nasan had'a mu kayi, tona hak'ura"
"Yauwa Yaya Saleema ko abinci banciba Wallahi aiki yamun yawa, nan yafara gayamata bai k'arasa ba tace sorry My choice
Kitchen tashiga abinci ta zuba cikin tray tareda mug wanda kunun Aya ne dayaji kayan k'amshi da sanyin sa ta zubo
sai kayan fruits data yanka, jerawa tai ta fito, hangar garden tai, bayanta yabi shima yana k'issima abubuwa da dama a ransa
Deen kaci abinci, akan budurwa zaka wulak'an tani?nashiryaku ai, hhhhh to dakada ka shiryamu rub'abbe kawai
Dariya sukai duka, daidai nan ta bud'e k'ofar suka shiga
Saving nasa tai, Wainar shinkafa ce da miyar taushe, taji naman kasuwa sai k'amshi ke tashi
Ruwa ta zuba masa hannu ya wanke, yafara ci itama hannu tasaka atare sukaci suna jefawa juna murmushi
Koda suka gama, again ruwa ta zuba masa ya wanke, sannan ta matsar da kwanukan gefe ta fuskance shi
Yaya Saleema bantab'ajin murna irinta Yau ba, ina alfahari dake, naciri tura kaf family namu, zanyi wa wadda nake so abu da kud'ina da Jikina da k'arfina kuma
Iyayen mu sun kasance Indai zasu yiwa Yaro aure, sune suke komai, harta gida su zasu baka kayan lefe sadaki komai da kika sani wanda akeyi nisa ala'ada sune keyi
Amma abin dad'i, ni da kaina da kud'i na zansiyawa My choice komai
Yau aka ban Rabin kud'in aiki na, zan yiwa Abba da Mom bayani, amma kud'in na Yaya Saleema ne
Inajin dad'i da kud'ina zan miki komai, tunda dama nakine komai na Deen na Saleema ne
Ajiyar zuciya ta sauke tayi hamdala ga ubangiji, tanuna masa murnarta sosai, tayimasa addu'a akan Allah ya taimakeshi akan kowanne abin hallita
Yana jin dadin Addu'ar Saleema Idan tamasa, sai wajan magreeb yayi harama, rakashi tai suna kewar juna ya tafi bayan sun cika cikin su da dad'ad'an kalamai

Kan titi ya cilla motar tasa, yana tafiya cikin hankali tareda wani cool music da yasaka mai dadin sauraro
Yanajin wata qaunar Saleema tana bin jikin sa, da komai nasa haka yai horn maigadi yazo ya bud'e masa
Parking area yayi ya aje motar sa, kana ya shiga gida
Parlour ya shiga anan yaga iyayensa a zaune, qarasawa yai gaishesu yai yace ya dawo lafiya
Abban sane yace Deen andawo lafiya?
Lafiya lou Abba nasameku lafiya?
Lag
lafiya lou na Saleema, dariya yai yace Abba ai Saleema tanada kirki, daga wajan ta nake nan yaga yamasa yadda sukai
Mom tasa itama dariya tai, tace Saleema itama ta iya shirme banda abinta taqicin abinci saboda wani dalili nata
A nan ya zauna akasha hira, kud'i ya je yaciro a cikin boot na motar sa, kana ya shigo ya dire gaban Abban nasa
Yace Abba ga kud'in nan, rabine aka ban na aikina 7.k ne
Kasamun albarka, amma zanyi wani abu acikin su, mekenan?
Kansa ya sunkuyar yace Abba dama haka nace acikin kud'in zanyiwa Saleema lefe da kayan sa rana, sai Kuma Sadaki duka zan nizan bada
Nasan kanayi kuma kaine maiyi, amma alfarma nake nema kabarni nayiwa Saleema komai da kaina hakan zaisa naji dad'i inada kud'in
Abba Idan nayi laifi kayi haquri kayi hak'uri, amma Idan akaban damar yin haka zanyi murna
Tafi yaji daga bayan sa, cousin nasa ne Shehu da Halifa ina da gudu ya mik'e suka rungume juna, dan uwa ya kake?
Lafiya lou na Saleema, Abba yazo yana marairaicewa akan Saleema. Wallahi kaf online sunsan Saleema amma abaki koni banga pics nata ba bare naganta
Dariya sukai shehu yace biki ya matsone?
Eh mana wata uku nan gaba kaga gara afara shiri, tun yanzu dama gobe za'akai kud'i koh Abba?
Eh Idan Allah ya kaimu, anan suka shan take ana hira saiga Sultan shima aka d'ora dashi
Har sallahr Isha'i suna tare, anan hira, yawan zancen labarin Saleema ma ne, Sultan ne yace kai Wallahi kanabada Maza kabi ka rud'e komai Saleema haba
Eh naji itama Yaya Saleema na sona, kamar yadda nake sonta
Nagani ai, Deeni, duka ya kaimasa yace kai wallahi daga yau Yaya Deen baka isa kana cemun Deen ba
Yayar ka zan aura, koh to Yaya nan suka tafa, kafin suka tashi akayi alwala aka tafi masallaci
Suna dawowa dining sukai anan akaci abinci aka baje sunce anan zasu kwana
Sultan jin haka, yace to bara yayiwa Abba waya yaga yamasa
9:00 aka tashi a parlour akayi d'akin Deen, kowanne matashi ya d'auka Deen kan Sofa ya hau, ya janyo wayar sa
Dialling number tata yayi, a'a kaga na Saleema za'afara koh?, muma bara muyi da namu bebs d'in
To wayahanaku?, yana magana ta d'auka My sugar?
Kaje gida lafiya, ya kake ya gajiyar aiki?
Feel fyn my choice, naje gida gasu shehu sun matsa yau saisunji muryar ki?
Dariya tai, tace to basu mugaisa, amma ki canja murya kada amusu irin muryan da kike mun
Amrak my sugar, basu tai nan suka gaisa suna mata shaqiyanci, sosai taji sun kwanta mata sunada kirki
Sultan ne ya karb'a yace amarya ya kike?
Uwaka nake, angayamaka muryanka zata canja mun, Dariya tai tace ka gujemu koh?
Zaka dawo ne.
Ni bani baby muyi hira, enye baby manya to gashi, bashi yayi nan ya amsa suka ci gaba da hirar su
Washe gari akaje akaika kud'i a gwangwazo gidan kakkanin ta, already dama ansaka rana
Iyayen suma Kansu ganin ankai kud'in sai murna suka ringa yi
Shida Ita aranar kamar zasu zuba ruwa a qasa su sha, shi kasa bacci ma yayi Illa Sallah da nuna godiyar su ga Ubangiji
Tunda aka kawo kud'i kuma Deen yazama d'an gida abincima anan yake ci Abban Saleema dariya abin yake bashi yanda yake ganin su
Itama Exam tasata agaba, kullum cikin karatu, danma yabata space yanxu
Yau Alhaji Sani yayi nufin aiwatar da k'udirin sa

@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now