22

56 1 0
                                    


  "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiuun, Alhaj haka kazama nashiga uku na lalace yarka ta cikin ka, amma baka damu da damuwar ta ba"
   Kuka sultan yasaka baran Mama da Mom tasu sultan kuka suka saka dukkan su, Yaya Na'eem kansa saidaya zubar da kwalla yanason tilon k'anwar sa, bayason abinda zai b'ata ranta amma gashi yanaji yana gani wani zaisaka suyi asarar k'anwar su.
   Baya ya juya ya fashe da kuka, Abban Deen kansa baisan lokacin daya fara hawaye ba, saidaya ji danshi kan fuskar sa. Hannu biyu yasaka ya dafe kansa yace wannan masifa tame ce ni Raheem?
  Sultan ne yace Abba Idan kanayiwa Allah da manzon sa ka taimaki yar uwata kabata wanda take so, kada ka biyewa abokin ka kaji Abba?, kansa ya dafa yace sultan kayi hak'uri nikaina hankalina ya tashi matuqa, kalli mahaifiyar ka inda take kuka narasa meke damun Abdul Aziz, amma acigaba da gayawa Allah shizaimana magani.
   Zaman kurame ake a wajan, babu mai cewa kanzil kowa da tunanin daya keyi, har akayi Sallah ta Isha'i babu labarin farfad'owar wani acikin su, hakan yasaka iyayen k'ara shiga tashin hankali, wani abin takaici NTA da ake gani a reception d'in saiga shi an hasko IV na d'aurin auren harda kirarin masoya da ake masa, mai gayyata Alhaji Raheem
   Murmushi Abban Deen yai yace kuji sabuwa wainine mai gayyata?, Allah yafika Sani, haka sukaita zama har wani lokaci kafin Deen akace ya farka, da saurin su, suka shiga d'akin a kwance yake akan gado ga drip a hannun sa duk bandage akan sa abin tausayi hawaye yana tsiyaya a fuskar sa
  Mom tasa ce ta k'arasa, hannun sa takama tace Deen kadena kuka mene haka namiji ne kai, kazama jarumi kaji?
   A hankali ya furta Mom niba namiji bane, kuma niba jarumi bane indai akan soyayyar Saleema ne, Mom wai Abba yace bazai ban Saleema ba?, menayi masa Mom? kuka ya fashe dashi sosai yana dafe da kansa
     Gefen gadon ta zauna, kansa ta dafa tace Deen, ka d'auki kaddara maikyau da mara kyau, shine kazama cikakken musulmi, kuma KA d'auka jarrabawa ce kuke yi, Allah yasa ku cinye a sa'a.
  Deen duk kanmu da munada iko na baka Saleema Wallahi a yau zamu d'aura muku aure mu baka Ita, amma bamuda wannan ikon.
   Yan uwan Abban ta Kansu da sukayi magana akan yazaiyi haka?, wallahi nuna musu yayi shi yakeda iko da yaran sa, saboda haka kadage da addu'a itace mafita.
  Maman Saleema itake wannan bayanin bayan Mom tai nata. Ido ya kuramata yace Mama meyasa kaddarar ba tazo ba tun kafin nafara son Yaya Saleema?, me yasa kaddarar bata zoba saida muka kusan cimma burin mu?, anya kuwa?, Deen kaifa musulmi ne saboda haka kada kayi sab'o katuna Allah shikeda iko akan komai, kuma da sanin sa da yadda sa hakan take kasan cewa.
   Baijira komai ba ya koma ya kwanta, minti biyu uku ya mike da sauri Mama ina Yaya Saleema?
  Kallon juna iyayen sukai, Abba ne yayi k'arfin halin yace kagane itama fad'uwa tai saboda haka tana nan asibitin itama ta kusa ta farka tunda kaima gashi jikin naka yana samun improvements sauran nata koh?
    Kai ya d'aga sannan ya koma ya kwanta. 12:00 wayar Mama tai ringing tana dubawa taga Abba ne a kasalance ta d'aga
  Ba sallama tambayar ta yayi akan a nan zata kwana ko zata dawo gida?, shi zaisaka a rufemasa gida, kasa cemasa komai tai saima hanging nata da tayi tajuya baya tana share hawaye.
    Saleema jikin nata ba sauqi, tunda gashi har wajan Asubah babu wani cigaba bare asaran zata farka, yan uwa kowa addu'a yake mata tunda duk kansu anan suka kwana.
    Deen alluran bacci aka samasa, shiyasa yayi baccin sa sosai bare ya tashi yace akaita gun sa.
   8:23 Saleema ta farka da sunan Allah a bakin ta, bud'e idonta tai, ganin ta datayi akan gadon Asibiti shiyasa tafara hasasho meya kawo ta?, kasa tuna komai tayi har Doctor Feedoh ta shigo Ita da wasu staff da sauri suka k'arasa magana sukai mata sannu, da ido ta amsa.
   Auna nata suka fara yi, Alhamdulillah jikin da sauqi, bugun zuciyar ya daidaita, sai abinda ba'a rasa ba. Magana ta jiyo daga waje cewar Abban ta yazo yace ta fito jibi d'aurin aure so zai kaita wajan gyaran amare, nan fa kwakwalwar ta tafara tuno mata komai, kara tasaka ta mike tana Abba da sauri sukayo kanta kafin ma su k'arasa ta zube a k'asa
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now