Zama yayi kusa da Ita ya yaye alkyabbar da aka nad'eta da Ita, kabbara yayi ya godewa Allah daya bashi Yaya Saleema amatsayin mata
Wani kyalli takeyi ga wani sanyin k'amshi dayake tashi a jikin ta, rigar da aka saka daga ciki, tayimata kyau super ce riga da skirt purple anyi d'in kin ya tattare daga k'irji sai wajan yayi wani iri gwanin sha'awa ga albarka tun k'irjin ta a bud'e, hakan yasaka Deen cikin wani yanayi
Daurewa yayi yace my choice ya kikejin wannan ranar ta yau?, murmushi tai a hankali tace inaji kamar babu wanda Allah yayiwa sakamako mai kyau a wannan ranar kamar ni, inaji ko a yanzu na mutu nacika buri na, tunda gani gaka matsayin ma'aurata babu abinda yakai hakan dad'i a waje na.
Kyad'a kai yayi, sannan yace Allah yayi miki albarka Matar arzik'i, hannun ta ya kamo a hankali wanda yayi kyau da jan lalle, murzawa ya fara yace Yaya Saleema taso muje a d'akko plate muci kazar amarci koh?
Huum tace sannan ta mik'e a hankali, da hannu ya nuna mata tai gaba, nok'e kafad'a tayi tace kayi gaba kaine babba, dariya yayi yace nine babba sainace kifara gaba kije ki d'akko.
Kallon sa tayi, kana tafara tafiya, mazaunan ta yabi da kallo tanajin farin ciki Saleema kayan Allah dashen Allah kainuwa yarinya mai hankali da tarbiyya, juyowa tai tace kaganka mekatsaya kallo ina tare dakai kana tunanin wani waje?, haba dai Tawan ked'in dai nake tunawa dakuma yadda Allah ya juya al'amransa yabashi Saleema lokacin daya fara cire tsammani akan ta.
Hannun sa ta janyo tace tawo muje nidai, eyen ba jiki yayi sauk'i harwani janyo ni ake, nazata ni zanyi d'awainiya ashe ke zakiyi?, ba nice zanyi ba, tana magana ta tafi luuu zata fad'i da sauri ya tarota hankalin sa tashe
Akan k'irjin sa yasata, yafara buga bayan ta kunnanta ya je yace Yaya Saleema I'm sorry nazata jikin yayi sauqi?, sannu koh?
Kai ta d'aga a hankali yafara tafiya da Ita, har kan gado ya ajiye ta k'afa fun ta ya aza akan bed peck yamata yace zauna naje na d'akko kasa d'agowa tayi, a hankali ya fice yana wai wayan ta
Hannu tasaka a fuskarta tana k'ara godewa Allah dayabata Deen matsayin miji, bataji shigowar sa ba, saijin hannun sa tai yana cire hannun ta akan fuska.
Yaya Saleema tunanin me takeyi?, bata tuna komai illa Deen d'in ta, d'alle mata baki yayi yace astagfurullah sunan miji gatsal ki gyara kinji
Baki ta turo tace saika dake ni bayan bani da lafiya?, sorry baby bazan kuma ba, tawo muci abinci, hannun yakama suka sauka kan rug dake cikin bedroom d'in
Leda ce fara ya bud'e, abune cikin irin ledar nan mai kyalli kulli biyu, janyo d'aya yayi ya bud'e cikin plate d'in ya juye. Hmm k'amshi d'an shila ne guda uku manya sunji k'uli da cabbage ga cucumber a had'e sai tashin k'amshi mai dad'i
Bismillah sukai suka fara ci, sunayi suna korawa da sanyayyiyar madarar shanu, a haka suka ci harsuka k'oshi, Kallon ta yayi yace waih lallai zanyi aiki a buhariyya amma Yaya Saleema take cin abinci haka?, au addu'a zanyi ma yau Yaya Saleema taci abinci, rabon ta da abinci wajan sati guda kinga sainayi murna yau kinci abinci.
Huum kaji da shi, murmushi yayi ya lakucemata hanci yakwanto da kanta kafadar sa, a haka yajata da hira, Ita gaba d'aya kunyar sa take ji, Deen yau shine a jikin ta, lallai aure da girma yake.
Hab'arta ya d'aga yace Yaya Saleema tashi a hankali kinji kawo hannun ki muzaga abinci yayai diet saimu kwanta. Mik'ar da Ita yayi a haka suka d'an zagaye bedroom d'in yana rik'e da Ita, sannan ya zaunarta akan d'an stool, yashiga toilet ruwan wanka ya had'a mata sannan yazo yace Yaya Saleema ruwan yayi ready aje ayi wanka
A hankali tana dafe cinya ta mike, rik'ota yayi da kansa ya taimaka mata tarage skirt d'in jikin ta, rigar zai zuge hannun sa ta kama, ta marairaice tace kabari zanyi da kaina kaji?, uhm uhm jikin ki baiyi kwari ba, amma next time komai nizanwa Yaya Saleema
Har bakin toilet ya rakata saida yaji alamar zubar ruwa sannan shima yashiga nasa d'akin yayi wanka, a shirye ya shigo mata yana k'amshi, wow Deen badai kyau ba, kan gado ya ganta cikin wata doguwar riga maroon har k'asa take amma tai kyau, itama k'amshi takeyi kanta a k'asa saboda Ita fa yaran mamaki yake bata, yadda yake sarrafa ta take masa abu, (Nace kinyi irinta Deedoh, taiwa Ahmad KALLON KITSE, Ashe rogo ne.lol)
@ut@r h@jiy@