Saleema murmushi ta bishi da shi axuciyarta tana godewa Allah da yayimata kyauta da miji alfahari ga kowa babu wanda zai kushe Deen koya fad'i aibunsa lallai tayi dace
Bata tab'a taking lecture mai dad'i ba irin yau sosai ta fuskanci komai tana kuma tattare da nishad'i da tunanin abin k'aunar ta
Deen 11 nayi ya fito ta class nasu yafara biyowa da lecturer aciki so ganinta kawai yayi yaji komai ya tafi duk wata damuwa na rashin ta da yayi na some hours ta kau, juyawa yake shirin yi, a jikinsa yaji kamar ana kallon sa d'aga manyan Idon sa yayi, yap Yaya Saleema ce da zuciya da ido sukai magana kana kowa yai murmushi suka maida hankali kan abinda suke
2 daidai aka tashi, Jakarta da handout nata ta rik'o a hankali ta fito bayan turmutsutsun fitowa da tabari akayi
Batazo da mota ba ga shi maybe Sultan yana class what can I do?, tsaye tai tana tuna ya zatayi horn tafara sharewa tai ganin kamar bata ganshi ba yasaka shi fitowa ya k'araso
"Hy My choice"
Kai dama Kaine, Wallahi nagaji let's go, tare suka jera abin sha'awa bayan d'unbin Idon da aka bisu da shi
Shiga sukai yaja sai gida, a motar yake cewa shifa ya gayawa Mom Ita zata gayawa Dad ayi komai da wuri ya matsu ya gansu tare
Koh to ai yanzuma tare muke Imamu
Lah Allah bansan wannan sunan nudai ki canjan Plx kinji Yaya Saleema?
Nima banson wannan yayan da kake cemun ka dena
To ai my choice nake cewa kad'an nake cewa Yaya Saleema yanzu. Tom zan canja Deeni
Tab zan rama Saleematuwa kece ma kikafi cancanta da sunan bani ba
Haka sukai hiran su harya direta ya juya shima gida
Alhamdulillah kowanne b'angare sunyi na'am da zabin nasu iyayen murna kamar me, abinda suke so tuntuni Allah baiso ba sai Yanzu
Yau gidan su Saleema cike yake matan yayunta suka zo, tarasa inda zatayi saboda murna tanason yaran su sosai
Yau wayarta na sama ko Deen ba'ayi waya dashi ba kuma ya bugo, ganin har wajan azahar bata d'agaba yasa ya tawo
Har ciki ya shigo, tana ganinsa da gudu tai kitchen tana dariya, tasan laifinta Yanzu data d'akko wayarta 22 missed call kuma duk nasa
Gaishesu yayi aka d'an tab'a hira yaron Yaya Sameer ya kirawo yace jekace da Aunty ta shirya asiyo ice cream koh?
Yes uncle inason ice cream da Chocolate koh? yes har Ita
Shiga yai Aunty Uncle yace ki shirya muje asiyo mana sweet
Kai kace bata nan, tana nan uncle tace bata nan haka yaje yace masa
Kai ta dafe tace kaji Yaro, k'amshin turaren sa taji tasan shine suman tsaye tai idonta ta rufe
My choice nakira ba kiyi picking ba nazo kin gudu nace ki shirya ance baki nan why?
Nifa ba komai wayan na sama shiyasa bangani ba, sorry kaji. nak'i saikin shirya munje Aunty Aisha tace kiyi maza
Ba yadda tai haka ta haura sama ta shirya suka tafi. Shop rite sukaje nan yace yaran su d'auka ko menene Ita kuma perfumes da Undies ya jibgomata harda su toms yaga tana sawa. Itadai kallon sa take baran daya d'akko bra Wallahi exactly shine size nata ya akayi ya sani?
Batada amsar tambayar ta amma wataran zata tambaye shi akwai lokaci, a hanya ta Rahma suya ya biya nan ma kayan kwalam da makulashe ya siyo musu basu jima ba koda suka isa gida Aunty Aisha taga saurin dawowar su
A compound suka tsaya d'an hira suka tab'a kana yamata sallama suna d'aga wa juna hannu harya fice.
India kai wannan soyayya haka?, shikuma mutum kullum idonsa akan mutane ba to munfi India k'are war sa Idon Ka
Alhamdulillah Deen karatun sa yake cikin sa'a da nutsuwa, kuma yana bin Abban sa wajan aikin su nan da nan Abban sa yafara d'ora shi akan k'ananan kwangilar da ake bashi irin Asibiti shakatafi da ake ginawa to yana bashi yaga yazaiyi kuma a sannu a hankali yafara artring yana zuwa class yana d'aukan darasi akan haka
Dama ya iya sosai amma ganin Yanzu kamar hakan zai taka rawar gani a aikinsa yasaka ya maida hankali sosai
Kuma fine tunda gashi Asibiti na k'aramar hukumar Dala shi yazana kuma yabada umarnin yadda yake so yakasance matuk'a wajan yayi kyau
Shiyasa yanzu bayada lokaci har paint wannan karan Abban Saleema yabashi yace aje ayi a k'aramar hukumar Ungwaggo
Deen ya faso kud'in da zaisamu kaf gida hud'u zai raba yabawa Mom d'aya Abban sa d'aya, Saleema d'aya sai kuma aje asasu cikin account
Iyayen su suna alfahari dasu, Deen ya dage sosai a kullum Idan ya tuna Saleema itace tasakashi barin abinda yake muradu sama da shekara 20 kuma gashi yasamu abinda yafisa saiya k'ara godewa Allah
Yau kaf suna majalisa ana hira kaf family'ne aka had'u harda Yayun Deen maza anata raha ana cewa shima Deen yabi sahun su Abba d'an kwangila zaizama tunda gashi yafara cikin sa'a abokansa iyayen su Har bashi suke
Murmushi kawai yake yace Wallahi ina tunanin ya akayi nafara wanan aikin bayan bashine zab'ina naba?
Zab'in budurwar Kane fa munafuki kazata bansan komai ba?
Sultan zama yayi yagawa musu yadda aka fara soyayyar da yadda a fakaice suka canja course da komai da komai wayyo dukkan su saida suka rik'e ciki saboda dariya
Lallai kunsha da kyar kaikuma Sultan kayi aikin zumunci ka ceto rayuka biyu
Tsokanarsa suke ana yakusa mutuwa suma Kansu iyayen dariya suke, abin kamar shirin film ko cikin Hausa novel
Shi bata dariyar yake ba, dama akan sa Yaya Saleema tabar zab'inta? kuma itama duk felling dayaji taji tansonsa haka dama? Lallai yazama dole yasaka wa da Saleema da abin alkhairi kula da ita shine wajibi ashe ana sonsa haka?
Batazoba saboda yau lecture ta yamma gareta, amma komai akai ya d'auko mata
Shine driver nata yanzu duk inda zata shizai kaita, tun tana jin kunya harta ware tasa ba tanason Deem yana kyau tata mata kuma yanda yake burgeta bai tab'a kama hannunta ba koda da wasa sab'anin yanzu da hakan yazaman ruwan dare
@ut@r h@jiy@