page 22

764 62 0
                                    

*RABI'ATUL ADDAWIYYA.*

*22*

Tafiya sukayi mai cike da nushad'i Abbi da Alh. Gambo cikin motar babban yaro Alhjin Suka shiga mai suna Ayub Ummi kuma motar Ubayyu suka shiga yaronshi na biyu kenan kuma auta domin daga kanshi mamansu tasami matsa a mahaifarta bata sake haihuwa ba.

Sun sami ilimi sosai both side boko d  Islama dukkansu suna aikin gobnati kuma suna da rufin asiri dai dai misali,  Ayub yayi aure har da yaranshi biyu.

Maman su Hajiya Raliya mace ce mai kirki da dad'in zama yanzu haka tajawo Ummi ajiki ta maidata tamkar 'yar uwarta ta jini inkagansu kace sun dad'e tare da juna ne.

Sun sami tarba ta karamci sosai a gidan Alh. Muktar Chanji.  Mahaifiyarsa Hajiya Sharifat wanda ake kira da Hajja ita ce tayi ta hidima da su.

Hira suke ta sha abinsu cikin falon hajja bayan kammala cin lunch.

Azuciye ta shigo ba d'a'a ta zauna gefen Hajja tana ta cika da batsewa cikin k'unar rai Hajja ta danqashi kanta tana cewa "wWai me yasa har yanzu baki da nutsuwa ne Khairiyya?"

  Tura baki yarinya da aka kira da Khairiyya tayi tace "Me nayi kuma Hajiyan complain?"

"Kinci gidanku nace, ke makauniya ce halan sanda kika shigo bakiga bak'i a tare dani ba ne ko ya?"

"Oh sorry  mutane sam banlura dabku ba." Tafad'i cikin salon iskanci.

Hajja sauke kanta tayi kasa cike dajin kunyar abinda khairiyya tayi ma su Ummi, su kam ko ajikinsu don ba'abinda ya damesu tunaninsuma wata kila tana da motsin rashin saiti ne dubi da yarda take ta gyad'a kai kamar mai sauraron music,  nan kuwa da hankalinta ras tsaban rashin tarbiya ne ke damunta.

Ad'age take kallon Addawiyya wacce bama tasan tanayi ba don hankalinta nakan indian film da ake nunawa a Bollywood. Aunty Hindu ce take lura da abinda take yi kuma take taji tsanar yarinyar ya d'arsu a ranta, ta had'e rai ahankali ta matsa kunnin Ummi tace "Ummi kira su Abbi mutafi hakanan wallahi natsani gidan yanzu."

  Kallon mamaki Ummi tabita da shi batare da tace komi ba tasoma dealing number Abbie.

Sai bayan sa'asar sukayi haramar tafiya domin su Abbie sunfita da Alhjin wani wuri.

Abin arziki sosai Hajja tabasu, don ledar Hindu daban tabata abinda yayi mugun bawa Hindu mamaki ainun.

Haka Alhjin yayi musu kyauta ta bajinta yayi ta musu godiyan ziyaran dasu kawo mishi. Aha sukayi musu sallama sukabar Hajja cike da kewa. Ita kam 'yar fitsara khairiyya tana tsaye a balcony tana ta jifansu da harara kamar sunyi mata laifi, yayin da uwarta matar gidan hajiya Karima, basu kai isar dazata tafito su gaisa da ita ba,  tana can kwance tana barcin asara,  da alama wurinta Khairi ta d'auko d'abi'un banza.

"Wallahi Ummi tunda nake bantabajin tsanar gida irin na Alh. Muktar chanji ba duk da tarin karramawan da akayi mana."

"To Hindu duk akanme kika damu kanki da zancen? Mu zumunci ya kaimu kuma munyi an wuce wurin don haka bana son sakejin maganar kinji ko?"

"Eh ummi insha Allahu ya wuce."

"Uhmm Ummi wata kila zata zama 'yar gidanne domin nayi mafarkin wai Alhjin yazo neman aurenta tana ta kuka bata sonshi. Wallahi saida na ganshi na tuna mafarkin."

Da sauri Hindu takawoma Addawiyya duka ta kauce tare ta mik'ewa ta gudu d'aki tana dariya.

 Ajiyar zuciya Ummi taja tace "Hindu lamarin auta yana jefani cikin rud'ani fa."

Kamar zatayi kuka ta amsa "Nima haka ummi kuma wallahi yawanci mafarkinta gaskiya yake zama,  amma ina addu'a Allah yasa wasa takemin batayi mufarkin komi ba.'

"Amin dai."

Da hanzari ta sauko down stairs tana gyara zaman karamin hijab d'in na school.
Ta russuna gefen Ummi tace "Ina kwana Ummi?" 

"Muntashi lafiya Auta?"

" Lafiya lau."

"Madallah."

Tana kok'arin fita ta tsinkayi muryan Hindu "Autan Ummi dawo maza ki karya" A mairaice ta juyo "Aunty zan makara in na tsaya yin breakfast gashi yau monday"

"koma meye sai kinsha koda tea ne kafin ki tafi don haka oya zo ki amsa.'

Kallon ummi take tana son tasa baki amma taki cewa komi sai ma yi tayi kamar bata wurin ta maida hankalinta kan karatun dala'ilul khairat d'inta.

Baki ature tayi ta shan ruwan tea din bako bread har ta hanye tas ta fice da gudu tana kallon agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta.

Tana fitowa gate motar Ubaiyyu na tsayawa don haka batare da bata lokaci ta fad'a back seat tare da cewa "Don Allah saukeni a school sai kadawo kasami Abbien."

Baice komi ba ya ja motar amma zuciyarshi cike da mamakinta yake na yarda ta bashi umurni batare da ya shirya ba sannan sakon gaggawa dadyn shi ya turoshi amsa wurin Abbie.

Suna isa ta fice tare da d'aga mishi hannu tace "Kayi sauri kada Abbie  yafita." Tayi gaba da sauri,  girgiza kanshi yayi yana sakin smile sannan yaja motar da gudu ya bar wurin.

Tana dawowa school taci karo da Hindu zaune k'asar bishiyar umbrella ta zuba tagumi hawaye yana zirara.

Zama tayi gefenta jiki a sanyaye ta kai hannu tana share mata hawayen tare da cewa "Waya yataba minke aunty? Ummi ko Abbie?"

Girgiza kai tayi cikin rawar murya tace "Mafarkinki ne ya tabbata Addawiy."

Wani dariya Addawiyya ta saki ta mike tayi ciki da gudu,  Hindu tabi bayanta da kallo sai kuma ta mik'e ta rufa mata baya cike da tuhuma.

Mrs j moon

RABI'ARUL ADDAWIYYA.Where stories live. Discover now