*RABI'ATUL ADDAWIYYA*
*25*
Zuwa can ta saki dariya mai sauti sai kuma ta soke kanta atsakanin cinyoyinta tana girgiza kai tare da cigaba dayin dariyan.
"Ke! Auta kina da lafiya kuwa?." Cewar Ummi tare da kai hannuzata d'ago kanta da ta soke. Tura baki tayi tamik'e da sauri tashige room d'insu, ummi zata bi bayanta Hindu ta rik'ota ta zaunar tayi k'asa da murya "Ummi ki kyaleta watakila tunanin wani abu takeyi kika katseta.
"Hindu hakikanin gaskiya inajin tsoron ayyikan Auta kada fa muyi sakaci wata rana awayi gari ta hauka ce."
"A'a Ummi ba'abinda zai faru insha Allah, adage dai dayi mata addu'a shi yafi."
"To Allah ya warware mana lamuranmu."
"Amin."
Bayan sungama cin supper, suna zaune a parlor, Ummi na damawa Abbie fura, Hindu kuma ta duk'ufa akan laptop tana wani aiki don tasoma koyarwa a F.C.E yanzu wata na biyu kenan da soma wanta. Addawiyya tare da Abbie kuwa kallon drama na larabawa sukeyi a channel d'insu. Dik abinda bata ganeba cikin larabcin sai ta tambayi Abbie ya fassara mata.
Ubaiyyu yayi sallama saida aka amsa mishi sannan ya shigo ya zauna tare da zamewa ya gaida Abbie, Ummi da Hindu, shi kuma Addawiyya ta gaishe shi.
Abbie ya tashi ya shiga room d'insa bai jimaba yafito da sak'o ya mik'a masa. Yayi musu sallama ya fice, Hindu ta dubi Addawiyya ta ce "Malama tashi kiraka shi." Baki ture tafice bako mayafi jikinta. Ummi ta rakata da idanu fuskanta d'auke da murmushi, cikin ranta tana addu'ar Allah ya had'a kansu zumuncinsu dasu Alh. Gambo yakuma k'arfi, haka abin yake agefen Abbie, sosai yake murad'in su k'ulla zumunta tsakaninsa da zuri'ar Alh. Gambo.Kamar yasan zata biyo shi a baya, da yafita sai ya tsaya a daf da parlorn yana ganin tafito yayi gaba cikin tak'ama daya aro da raan tsaka. Ja tayi ta tsaya tana kallon solon iskaro dayakeyi mata, sai da ya shiga motarshi sannan ya gano bata biyo shi ba yafito da sauri yana waige waige can ya hangota tsaye bakin parlornsu ta kafeshi da mayan idanunta mai jefashi cikin rud'ani dazarar yayi arba dasu.
Sauke tak'amar ya yi yadawo inda take tsaye kamar zai rungumeta ta ja baya yasa dariya ya ce "Baki san kin girma bane halan, da kika fito babu mayafi?" Harara ta watsa mishi, ya kuma matsowa kusa da ita tayi saurin juya mishi baya ta ce "Zan saita maka maths d'inka da yasami matsala in har kace haka zaka rik'a yimin"
"Me nayi miki yanzu?"
Banza tayi da shi zuwancan kuma ta ce "Sai da safe, kagaishemin da Aisha inkaje wurinta, kuma wayar da ka sayo zaka bani, ina rok'onka dan Allah kabawa Aisha ne domin ita tafini bukatar ta. Tana sonka da gaskiya dan Allah ka k'eta kyau domin hakan zaifima alkhairi."
Ko kafin yayi magana ta shige parlor ta barshi nan tsaye cike da mamakin inda ta sami labarin wayar da ya saya mata. Yana driving hankalinsa ya kasu biyu, lamarin Addawiyya yasoma shanye tunaninsa.
Kamar kullum duk in sun fito break a school k'asan bishiyar mango suke zama suyi ta hiransu ita da maryam har zuwa sanda lokaci komawa class zaiyi.
Yauma zaune suke suna hira akan test d'in dasu kayi d'azun kafin fitowarsu. Maryam tace "Ke kam my Addawiy kinji dad'inki ba'abin da yake baki wuya jiba yarda kika riga kowa gama test alhalin da gwaraza masu tsananin kwazo a ajin amma tun sanda kikazo duk suka koma lakas kamar sun mace, ba salo da fi'ili dan sungamu da wacce da damasu akomi.Dariya tasaka sosai, " Maryam kenan Allah kina da abin dariya kam, kinsan ni kam sam banga wani kwazo danake dashi ba tunda banyi ko quartern kiba a komi da komai."
"Kefa 'yar rainin hankali ce wata rana my Addawiy, wato abin naki har da tsokana ko?"
"Ba tsokana sai gaskiya 'yan mata Doguwa."
YOU ARE READING
RABI'ARUL ADDAWIYYA.
PoetryZumunci ne mai ban al'ajabi tsakanin jinsin mutum da Aljan wanda ya rabe tsakanin musulmai da kafiransu.