*RABI'ATU ADDAWIYYA*
*31*
Yana shiga parlorn daidai ta fito daga kitchen d'auke da tire madaidaici shak'e da kayan motsaba baki.
Gabanta taji ya fad'i, yasoma rawa ta tsaya tsak tare da sauke kai k'asa. Tasan Aliyu ne yazo wurin tunda taji jikinta ya sanja, baki ta tura saci kallon k'afar shigowa. Tsaye yake ya hard'e hannayesa ak'iirji ya zubo mata idanu bako k'iiftawa, sai ta kara daburcewa gabanta nacigaba da harbawa, ta koma da kanta k'asa ta kasa cira k'afarta.
Takowa yayi asannu har ya iso inda take tsaye ya mik'a hannu ya amshi tiren ya matsa daf da kunninta ya ce "Hala ni dodone da kike jin tsorona har jikinki yana rawa haka?"
Wani yar taji ajikinta, tayi saurin ja baya batare da ta amsa ba. K'ara matsowa yayi zata gudu ya take mata kafa ta rintse idanunta dan azaba, ya saki murmushi mai sauti ta bud'e idanun tana hararanshi.
"Waww beauty kinfi kyau ahaka cigaba da min abin."
Tura baki tayi sai kuma ta marairaice face ta ce "Ka d'agamin yatsu kada kajimin ciwo."
Da sauri ya d'aga yana kiran "Am sorry da zafi ko?"
Wani kallo ta sauke mishi tayi gaba yabiyo bayanta yana dariya k'asa-k'asa.Zama tayi gefen Maryam tana yamutsa fuska, sai tayi mishi mugun kyau ahaka, ya ajiye tiren akan table dake gabansu yana kok'arin bud'e robar coke tayi saurin rik'e hannunsa sai kuma ta saki da hanzari tana yarfe yatsu.
Murmushi yayi mai burgewa, yaja baya ya zauna akujeran dake kallonta, ya kai dubanshi inda khairi take zaune, wacce tumd'azu ta sake baki da hanci tana kallon abin al'ajabi, 'Wai Yaya Haydar ne yake nuna soyayyarshi a zahiri haka bako kunya.'
"Ke tashi kibawa mutane wuri, kina wani kallon mutane idanu bud'e ba d'igon kunya." Maganarshi ya katse mata tunani.
Da sauri Kahiri mike tabar wurin tana dariya, cije labbansa yayi yana bin bayanta da harara.
"K'awarmu kin iso lafiya?" Ya ce da maryam wacce kallo d'aya taga dacewarsu da Addawiyya. "Lafiya lau, ya office da ayyuka?."
"Alhamdulillah amma ba dad'i kam."
"Ayya to Allah tai maka."
"Amin, thanks."
Addawiyya wacce take saurarensu ta motsa a sannu cike da class ta soma zubawa Maryam drink ta mik'a mata sannan ta bud'e container mai d'auke da danbum nama tazuba ta tura gabanta tana satan kallon Haydar wanda yayi balance ya zuba kafeta da manyan idanunshi.
"Godiya nake aminiyata."
Murmushi tayi batare datace k'alaba. Haka nan takejin mulki da isa na shigarta.
Sosai ta takura da zamanshi a wurin, duk motsin daza tayi eyes d'inshi na kanta, tana son gudu amma ta kasa tashi domin leg nata bazasu d'auketa yarda take so ba.
Hira suke tayi da Maryam kamar sun dad'e da sanin juna, ita dai komi takasa cewa koda kuwa sun sakota cikin hiran iyakarta gyada kai ko girgizawa, tazama kurman k'arfi da yaji.
Shigowar Hameed yasa taji kuzari yazo mata ta tashi da sauri tashige bedroom.
Dariya Hameed yasa yana nuna Haydar "Da kyau nawa yasoma bada assignment kenan, tam Allah yasa ayi nasara."
Had'e fuska Haydar yayi tare da wulla mishi harara ya ce "Kaifa banza ne wallahi, gashi nan da zuwanka ka kora mana abokiyar hira ko k'awarmu?"
Murmusawa maryam tayi tare da gyad'a mishi kai.
Tabe baki Hameed yayi yamufi dinning area yana cewa "Kadai tsaya kallon ruwa kwad'o yayima k'afa."
"Bakinka ya bi rariya."
CZYTASZ
RABI'ARUL ADDAWIYYA.
PoezjaZumunci ne mai ban al'ajabi tsakanin jinsin mutum da Aljan wanda ya rabe tsakanin musulmai da kafiransu.