*RABI'ATUL ADDAWIYYA*
*34*
Kwance take cikin bedroom d'in Ummi ta rufe jikinta har zuwa samar kanta da k'aton bargo amma duk da haka sai rawan sanyi takeyi.
A kalla ta d'auki mintoci 30 ahakan sannan tasoma zufa alamar zazzabin dake damunta zai sauka.K'ara gyara blanket d'in tayi tare da jan siririyar tsaki ta furta "Duk da ban kyauta mishi ba ai tunda na kira phone d'insa sai ya d'auka yaji uzirina ba wai yayi watsi da niba." Ta kuma jan wani tsakin cike da jin takaici.
Wani sarawa taji gefen kanta yayi mata ta dafe wurin tana matsan kwalla.
"Wai dama haka fushin masoyi yake ga masiyiya?" Ta tambayi kanta."Lallai kam in haka abin yake masoya suna shan azaba, wash ni Addawiyya, Allah kakawomin mafita, ka karkatomin da hankali Yaya Ali ya bar fushi nan ko nasami sa'ida a ruhina."
Kimanin kwanaki uku kenan da dawowarsu amma ko sau d'aya Haydar baizo gidansu ba kuma bai kirata a waya ba ita ce ta kirashi ranar da suka kwana biyu da dawowa yak'i d'agawa abinda yayi mugun b'ata mata rai har ya haifar mata da zazzabi mai zafi kuma tundaga lokacin bata sake kiranshi ba duk da muradin son jin muryanshi da takeyi kamar me.
Sai bayan azahar ta farka daga barci da ya kwasheta bata sani, da hanzari ta shige bathroom, tana fitowa ta shimfid'a sallaya ta hau, bayan ta idar ta mik'e ta shafa lotion ta zura doguwar riga roba mai d'auke da k'ananar stones ta yane kanta da karamin gyale shima tafito parlor.
Gyefen ummi ta zauna a kasalance ta ce "Ummi barka da war haka, nabarki da aiki ko? "
Cike da kulawa ta amsa "Alhamdulillahi Auta, yajikin naki, kin warware? ko sai nakira miki Salma ko Hameed wani yazo ya dubaki?"
"A'a na warke, kasala ce kawai taragenmin yanzu kuma itama zata bari."
"Tam Allah yakara lafiya."
"Amin."
"Ga abinci can a dining kije kici zakiji karfin jikin"
"Ok nagode Ummina."
Tura abincin takeyi kawai kamar tana cin magani sabida gaba d'aya zuciyarta taki yi mata dad'i ga bakinta ba d'and'ano sam.
Tana gamawa ta gyara wurin ta dawo ta zauna ta bud'e data. Dan wata kila zatasami abin zai d'ebe mata kewa.
Ganin Maryam a online yasa ta tura mata sak'o.
'''Ki turomin document d'in Babban goro na (khadeeja candy) da cigaban Gidan k'unci na (bebeelo) da kuma document d'in Wata uwar na (Haemeebrah) ke da dai novels masu dad'i masu d'auke da darasoshin rayuwar da muke ciki."Ta shiga ta duba Haydar taga yana online, kamar zatayi mishi magana kuma sai ta fasa ta had'e fuska tana hararan wayarta kamar shi ne agabanta.
Tana shirin sauka taga ya turo mata da massage da sauri ta duba "Malamansu ki cire photo nan dake kan profile naki yanzu."
K'uri tayiwa gajeren sakon da ido kamar wacce ta warke makanta cikin tura baki ta shiga setting tayi remove ta sauka da sauri batare da ta duba massage d'in Maryam da taga sun shigo ba.
Haydar ganin ta sauka yaja tsuka. "Wato tafi k'arfin ta amsamin kenan?"
'To ko sabon saurayi tayi balarabe, shi yasa tasomamin wulakanci irin tasu na mata?.' Wani shashi na zuciyar shi ya amsa mishi 'Kaima baka kyauta mata ba Ali. kome tayi maka ai ka nemeta ka saurari uzurinta ba wai kayi ta fushi da babu gaira babu dalili.'
"Yes ban kyauta ba kam!." Ya ambata da k'arfi. Ya mik'e ya zari key d'in motarshi yafice har yana had'awa da gudu.
A parking lot ya had'u da Hameed ya/ce "Yaya Haydar sai ina zuwa haka kuma?"
"Inda ka aike ni." Ya masa mishi bai kuma jira amsarsa ba ya shige mota ya fizga da k'arfi, mai gadi ga wangale gate ya fice.
"Allah yayi maka sauki kai kam." Hameed ya furta cikin tab'e baki.
Tana kwance saman Cushing suna hira da Ummi ta tsinkayi sallamarsa, Ummi ce ta amsa mishi ya shigo a natse ya russuna ya gaida Ummie ta amsa cikin fara'a tare da mikewa ta bar parlorn.
Kallon kallo sukayiwa juna sai taga yarame amma ya k'ara kyau sosai.
Shima kallo d'aya yagano ta rame sai dai yana cike da mamakin girma da cikan da tayi wanda sam bai lura da suba sanda suka had'u airport.
Itace ta soma janye idanunta,cike da yanga ta motsa lips d'in ta ce "Ina yini, ya office?"Bai amsa ba illah idanu da ya kuma bud'ewa yana k'are mata kallo, kamar yau yasoma ganinta.
Wani matsanancin kunya ne ya kawo mata ziyara domin ta tuna rigan jikinta ta kamata tsan-tsan gyalenta bai rufe komi ba.Cikin shagwababbiyar murya ta ce "Please Yaya Ali d'an jirani a sitting room."
Ko motsi baiyi ba balle ta saran zai fice.
Tashi tayi ta haye upstairs cikin sarsarfa don ta sanyo hijab.Murmushi ya saki mai sauti yana mai furta "Komi naki mai kyau da burgewa ne Rabi'atu,ya Allah ka mallakamin ita da sauri."
YOU ARE READING
RABI'ARUL ADDAWIYYA.
PoetryZumunci ne mai ban al'ajabi tsakanin jinsin mutum da Aljan wanda ya rabe tsakanin musulmai da kafiransu.