page 30

687 58 2
                                    

*RABI'ATU ADDAWIYYA*

*30*

Turus Hindu tayi sadda ta fito daga toilet ta cimma Addawiyya zaune hawaye jagejage a fuskanta.

 Cikin rawar jiki ta isa inda take zaune ta dafa kad'anta ta ce "Autan Ummi me ya faru?"
 
Mai makon ta amsa sai ta fashe da kuka mai sauti.

Gaban Hindu ya yanke ya fad'i rass!!! Ta zauna gefenta jiki ba k'wari ta kamo hannunta ta rintse gam ta ce "Fad'amin damuwarki Addawiyya, ko bakiso na sami k'aruwan twins ba ne?"

Da sauri ta girgiza kai tana jan hanci ta ce "Tunani nake da ace hussain ya rasu ko ya zakiji aranki."

Cikin daburcewa Hindu tace "Autan Ummi wani abu ya farune?'

"Eh." Ta amsa tare da bata labarin tundaga sanka taji Uncle Habibullah yayi mata magana a parlour zuwa sanda ta ceci jaririn ahannun hajiya karima ta d'ora da cewa "Amma ina mai rok'oonki dan Allah tare da manzonsa kada kisanar da kowa zancen, ita da kanta zata fad'a da bakinta intaji azaba."

"Autan Ummi kinaganin rashin d'aukan matakin ba zai kuma bata dama wata rana tadowo ta cutar dasu ba?"

Jim tayi tana nazari "Bana tunanin zata kuma samun kuzarin sake cutar dasu, sabida yanzu haka tana cikin rud'anin kamata danayi tare da fargaba kada Alhaji yaji kuma tana mugun tsoron 'yan sanda, tana can ana fetsa yawo."
Tagarasa maganar cike da dariyan mugunta, hawayen daya makale yazubo a fuskanta ta sa hannu ta share tana cigaba da dariyar.

Kama kunninta Hindu tayi tace "Allah shiryamin ke Addawiy .

"Amin.'

"Allah yacigaba dabamu kariya gabaki d'aya."

"Amin Aunty, shi ne addu'ar da yadace muyi tayi kawai domin ita kaddaran Allah wanzarciya ce inta tashi zuwa babu tsimi babu daraba sai ta Allah."

Haka ne kam, Allah ya datar damu.'

"Ami."

A tare Salma da Ummi suka iso, sai murna sukeyi suna hamdalah ga Allah.

Addawiyya tun shigowarsu da sun had'a idanu da Salma sai ta sa dariya.
Ummi ta dubeta tayi mata dak'uwa "Kinci gidanku Auta, yazakisa mutane agaba kiyi tayi musu dariya kamar  mai tanbotsai."

Dariya takuma kwashewa dashi har da rik'e ciki, Ummi ta zabura tayo kanta ta kwasa da gudu tabar room d'in.
 
"Ummi kibarni da ita, nasa abinda take ma dariya kuma zanci mutuncinta inbata kiyayeni ba."

"Oh to kunfi kusa ai, nawa idanu."

Hindu ta sauke kallonta bisa tumbin Salma ta kauda kanta gefe tana dariya k'asa-k'asa ta ce "Eh dole autan Ummi tayi ta dariyan murna ashe mun kusa samun wani k'aruwan ne."

Cike dajin kunya Salma ta mik'e ta fad'a toilet, suka saka dariya har Ummi.

"Allah yaraba lafiya."

"Allahumma Amin Ummin mu."

 
Mugun karo sukayi da juna ta kwalla k'ara ta zube saman kneel, domin tayi mugun tsorata da ganinsa. Cikin hanzari ya d'agata yana kiran "Sorry sorry Rabi'a, bakiji ciwo ba?"

Ta zame jikinta hannunta dafe da k'irjinta,  da baya da baya take tagiya eyes d'inta yana kanshi har ta shige cikin kitchen ta kulle.

Dafe kai ya yi tare da cije lips ya saki murmushi mai sauti "I really luv u pretty." Ya furta ahankali sai kuma ya yamutsa fuska "Uhmm Allah kin wuce pretty  akomai my heart, beauty zaifi dacewa dake my kwaila." Sai yasaki dariya ya dungule hannu ya naushi iska yana kuma furta "Amma fa Hameed d'an air ne, yanzu wannan zankad'ed'iyar budurwan yake kiranta da kwaila?"

RABI'ARUL ADDAWIYYA.Where stories live. Discover now